EZRA 4

Magabta Suna Hana Aiki

1 Sa’ad da abokan gāban Yahuza da Biliyaminu suka ji waɗanda suka komo daga bauta suna gina Haikalin Ubangiji Allah na Isra’ila,

2 sai suka tafi wurin Zarubabel, da shugabannin gidajen kakanni, suka ce musu, “Ku yarda mana mu yi ginin tare, gama muna yi wa Allahnku sujada kamar yadda kuke yi, muna kuma ta miƙa masa sadaka tun kwanakin Esar-haddon, Sarkin Assuriya, wanda ya kawo mu nan.”

3 Amma Zarubabel, da Yeshuwa, da shugabannin gidajen kakannin Isra’ila suka ce musu, “Ba abin da za ku yi tare da mu na ginin Haikalin Allahnmu, amma mu kaɗai za mu yi wa Ubangiji Allah na Isra’ila, gini kamar yadda sarki Sairus, wato Sarkin Farisa, ya umarce mu.”

4 Sai mutanen ƙasar suka shiga karya zuciyar jama’ar Yahuza, su kuwa suka ji tsoron yin gini.

5 Mutanen kuwa suka yi ijara da mashawarta, da za su sa niyyarsu ta shiririce tun daga zamanin Sairus, Sarkin Farisa, har zuwa zamanin Dariyus, Sarkin Farisa.

6 A farkon sarautar Ahasurus, sai suka rubuta takarda ƙara a kan mazaunan Yahuza, da Urushalima.

Takarda Zuwa ga Sarki

7 A zamanin Artashate kuma sai Bishlam, da Mitredat, da Tabeyel, da magoya bayansu suka rubuta wa Artashate Sarkin Farisa takarda da harufan Suriya, aka fassara ta.

8 Rehum shugaban sojoji, da Shimshai magatakarda, suka rubuta takardar ƙara a kan Urushalima zuwa Sarki Artashate.

9 Sa’an nan Rehum shugaban sojoji ya rubuta tare da Shimshai magatakarda,da abokansu, da alƙalai, da masu mulkin larduna, da ma’aikatan hukumomi, wato mutanen Farisa, da na Erek, da na Babila, da na Shusha a ƙasar Elam,

10 da sauran al’ummai, waɗanda mai girma, Asnaffar, ya kwaso, ya zaunar da su a biranen Samariya, da sauran wurare na Yammacin Kogi.

11 Ga abin da suka rubuta.

“Gaisuwa daga talakawanka, mutane na hayin Kogin zuwa ga sarki Artashate.

12 “Muna sanar da sarki, cewa Yahudawan nan waɗanda suka fito daga gare ka suka zo wurinmu, sun tafi Urushalima, suna sāke gina mugun birnin nan na tawaye, sun fara gina garun, ba da jimawa ba za su gama ginin.

13 Sarki ya sani fa, idan an sāke gina birnin, aka kuma gama garun, ba za su biya haraji ko kuɗin shiga da fita na kaya ko kuɗin fito ba, baitulmalin sarki za ta rasa kuɗi ke nan.

14 Da yake muke cin moriyar fāda, ba daidai ba ne mu bari a raina sarki. Saboda haka muke sanar da sarki,

15 domin a bincika a littattafan tarihin kakanninka. Za ka gani a littattafan tarihi, cewa wannan birni na tayarwa ne, mai yin ta’adi ga sarakuna da larduna. A nan ne aka ta da hargitsi a dā. Shi ya sa aka lalatar da shi.

16 Muna sanar da sarki fa, idan aka sāke gina wannan birni da garunsa, ba za ka sami abin mallaka a lardin Yammacin Kogi ba.”

Amsar Sarki

17 Sarki kuma ya aika musu da amsa ya ce, “Gaisuwa zuwa ga Rehum shugaban sojoji, da Shimshai magatakarda, da abokansu waɗanda suke zaune a Samariya da lardin Yammacin Kogi.

18 “An karanta mini wasiƙar da kuka aiko mana, filla filla.

19 Na ba da umarni, aka bincika, aka kuwa tarar, cewa wannan birni ya tayar wa sarakuna a dā, an yi tawaye da hargitsi cikinsa.

20 Manya manyan sarakuna sun yi sarauta a Urushalima, waɗanda suka yi mulki a kan dukan lardin Yammacin Kogi, waɗanda aka biya su haraji, da kuɗin shiga da fita na kaya, da kuɗin fito.

21 Saboda haka sai ka umarci waɗannan mutane su daina gina birnin nan, sai lokacin da na ba da umarni.

22 Ka kula fa, kada ka yi kasala a wannan al’amari, don me ɓarna za ta bunƙasa har ta cuci sarki?”

23 Sa’ad da aka karanta wa Rehum, da Shamshai magatakarda, da abokansu, wasiƙar sarki Artashate, suka hanzarta suka tafi wurin Yahudawa a Urushalima, suka gwada musu iko, suka tilasta musu su daina ginin.

24 An tsai da aikin Haikalin Allah a Urushalima, sai a shekara ta biyu ta sarautar Dariyus Sarkin Farisa.