EZRA 5

An Sāke Kama Aikin Gina Haikali

1 Haggai kuwa, da Zakariya ɗan Iddo, annabawa, suka yi wa Yahudawan da suke a Yahuza da Urushalima wa’azi da sunan Allah na Isra’ila wanda yake iko da su.

2 Sai Zarubabel ɗan Sheyaltiyel, da Yeshuwa ɗan Yehozodak, suka tashi suka sāke kama aikin gina Haikalin Allah wanda yake a Urushalima. Annabawan Allah suna tare da su, suna taimakonsu.

3 A wannan lokaci kuma, sai Tatenai, mai mulkin lardin Yammacin Kogi, da Shetar-bozenai, da abokansu suka je wurinsu suka yi magana da su, suka ce, “Wa ya ba ku izini ku gina Haikalin nan, har ku gama wannan garu?”

4 Suka kuma tambaye su, “Ina sunayen waɗanda suke yin wannan gini?”

5 Amma ikon Allah yana kan dattawan Yahudawa, saboda haka ba su hana su yin ginin ba, sai sun kai wa Dariyus labari, sun sami amsa a rubuce tukuna.

6 Wannan ita ce wasiƙar da Tattenai mai mulkin lardin Yammacin Kogi, da Shetar-bozenai, da abokansu ma’aikatan hukuma waɗanda suke Yammacin Kogi, suka aika wa sarki Dariyus.

7 “Zuwa ga sarki Dariyus, salama gare ka.

8 Muna sanar da sarki, cewa mun tafi lardin Yahuza a wurin Haikalin Allah Mai Girma. Ana ginin Haikalin da manyan duwatsu, ana kuma sa katakai a bango. Aikin yana ci gaba sosai a hannunsu.

9 “Mun yi magana da dattawan, muka tambaye su wane ne ya ba su izini su gina wannan Haikali har su gama bangonsa.

10 Mun kuma tambaye su sunayensu don mu rubuta maka sunayen mutanen da suke shugabanninsu.

11 To, sai suka ce mana, ‘Mu bayin Allah ne wanda yake da sama da ƙasa, muna sāke gina Haikalin da wani babban sarki na Isra’ila ya gina tun shekaru da yawa da suka wuce.

12 Amma saboda kakanninmu suka tsokani Allah na Sama, sai ya bashe su a hannun Nebukadnezzar, Sarkin Babila, mutumin Kaldiya. Shi ne ya lalatar da Haikalin nan, ya kuma kwashe jama’a zuwa Babila.

13 Amma a shekara ta fari ta sarautar Sairus, Sarkin Babila, sai ya ba da izini a sāke gina wannan Haikali na Allah.

14 Kwanonin zinariya da na azurfa na Haikalin Allah, waɗanda Nebukadnezzar ya kwashe daga cikin Haikalin da yake Urushalima, zuwa haikalin gumaka na Babila, sarki Sairus ya ɗauke su daga haikalin Babila ya ba wani mai suna Sheshbazzar wanda ya naɗa shi mai mulki.

15 Ya ce masa, ya ɗauki waɗannan kwanoni, ya tafi, ya sa su cikin Haikalin da yake a Urushalima, a sāke gina Haikalin Allah a wurin da yake a dā.’

16 Sheshbazzar kuwa ya zo ya aza harsashin ginin Haikalin Allah wanda yake a Urushalima. Tun daga wannan lokaci, har yanzu ana ta gininsa, har yanzu kuma ba a gama ba.

17 Domin haka in ya gamshi sarki, sai a bincike ɗakin littattafan da yake Babila don a gani ko sarki Sairus ya ba da izini a sāke gina wannan Haikalin Allah a Urushalima. Bari sarki ya aiko mana da abin da ya gani a kan wannan al’amari.”