FAR 12

Allah a Kira Abram

1 Ana nan sai Ubangiji ya ce wa Abram, “Ka fita daga ƙasarka, da danginka, da gidan mahaifinka zuwa ƙasar da zan nuna maka.

2 Zan kuwa maishe ka al’umma mai girma, zan sa maka albarka, in sa ka ka yi suna, domin ka zama sanadin albarka.

3 Waɗanda suka sa maka albarka zan sa musu albarka, amma zan la’anta waɗanda suka la’anta ka. Dukan al’umman duniya za su roƙe ni in sa musu albarka kamar yadda na sa maka.”

4 Abram kuwa ya kama hanya bisa ga faɗar Ubangiji, Lutu kuma ya tafi tare da shi, Abram yana da shekara saba’in da biyar sa’ad da ya yi ƙaura daga Haran.

5 Abram kuwa ya ɗauki matarsa Saraya da Lutu, ɗan ɗan’uwansa, da dukan dukiyarsu, da dukan mallakarsu waɗanda suka tattara a Haran.

Sa’ad da suka kai ƙasar Kan’ana,

6 Abram ya ratsa ƙasar zuwa Shekem, wurin itacen oak na More. A lokacin nan Kan’aniyawa suke a ƙasar.

7 Sai Ubangiji ya bayyana ga Abram, ya ce, “Ga zuriyarka zan ba da wannan ƙasa.” Sai ya gina bagade ga Ubangiji, wanda ya bayyana gare shi.

8 Ya zakuɗa daga nan zuwa dutsen da yake gabashin Betel, ya kafa alfarwarsa, Betel tana yamma, Ai tana gabas, a nan ya gina wa Ubangiji bagade, ya kira bisa sunan Ubangiji.

9 Abram kuwa ya ci gaba da tafiya, ya nufi zuwa wajen Negeb.

Abram a Masar

10 A lokacin nan ana yunwa a ƙasar. Sai Abram ya tafi Masar baƙunci, gama yunwa ta tsananta a ƙasar.

11 Sa’ad da yake gab da shiga Masar, ya ce wa matarsa, Saraya, “Na sani ke kyakkyawar mace ce,

12 lokacin da Masarawa suka gan ki za su ce, ‘Wannan matarsa ce,’ za su kashe ni, amma za su bar ki da rai.

13 Ki ce ke ‘yar’uwata ce, domin dalilinki kome sai ya tafi mini daidai a kuma bar ni da raina.”

14 Sa’ad da Abram ya shiga Masar sai Masarawa suka ga matar kyakkyawa ce ƙwarai.

15 Da fādawan Fir’auna suka gan ta, sai suka yabe ta a gaban Fir’auna. Aka ɗauke ta aka kai ta gidan Fir’auna.

16 Saboda ita Fir’auna ya yi wa Abram alheri. Abram yana da tumaki, da takarkarai, da jakai maza, da barori mata da maza, da jakai mata, da raƙuma.

17 Sai Ubangiji ya wahalar da Fir’auna da gidansa da manya manyan annobai saboda matar Abram, Saraya.

18 Sai Fir’auna ya kirawo Abram, ya ce, “Mene ne wannan da ka yi mini? Don me ba ka faɗa mini ita matarka ce ba?

19 Don me ka ce ita ‘yar’uwarka ce, har na ɗauke ta ta zama matata? To, ga matarka, ka ɗauke ta ka tafi.”

20 Fir’auna kuma ya umarci mutanensa a kan Abram, su raka shi da matarsa, da dukan abin da yake da shi.