FAR 11

Hasumiyar Babila

1 A lokacin, harshen mutanen duniya ɗaya ne, maganarsu kuma ɗaya ce.

2 Sa’ad da mutane suke ta yin ƙaura daga gabas, sai suka sami fili a ƙasar Shinar, suka zauna a can.

3 Sai suka ce wa juna, “Ku zo, mu yi tubula, mu gasa su sosai.” Suka yi aiki da tubali maimakon dutse, katsi kuma maimakon lāka.

4 Sai suka ce, “Ku zo, mu gina wa kanmu birni, da hasumiya wadda ƙwanƙolinta zai kai can cikin sammai domin mu yi wa kanmu suna, domin kada mu warwatsu ko’ina bisa duniya.”

5 Ubangiji kuwa ya sauko ya ga birnin da hasumiyar da ‘yan adam suka gina.

6 Ubangiji kuwa ya ce, “Ga su, su jama’a ɗaya ce, su duka kuwa harshensu guda ne, to fa, ga irin abin da suka fara yi, ba abin da za su shawarta su yi da zai gagare su.

7 Zo mu sauka, mu dagula harshensu, domin kada su fahimci maganar juna.”

8 Haka kuwa daga wurin Ubangiji ya warwatsa su ko’ina bisa duniya, sai suka daina gina birnin.

9 Domin haka aka kira sunan wurin Babila, domin a nan ne Ubangiji ya dagula harshen dukan duniya, daga nan ne kuma Ubangiji ya warwatsa su ko’ina bisa duniya.

Zuriyar Shem

10 Waɗannan su ne zuriyar Shem. Lokacin da Shem yake da shekara ɗari, ya haifi Arfakshad bayan Ruwan Tsufana da shekara biyu.

11 Shem kuwa ya yi shekara ɗari biyar bayan haihuwar Arfakshad, ya kuma haifi ‘ya’ya mata da maza.

12 Sa’ad da Arfakshad yake da shekara talatin da biyar ya haifi Shela.

13 Arfakshad kuwa ya yi shekara arbaminya da uku bayan haihuwar Shela, ya kuma haifi ‘ya’ya mata da maza.

14 Sa’ad da Shela yake da shekara talatin, ya haifi Eber,

15 Shela kuwa ya yi shekara arbaminya da uku bayan haihuwar Eber, ya kuma haifi ‘ya’ya mata da maza.

16 Sa’ad da Eber ya yi shekara talatin da huɗu ya haifi Feleg,

17 Eber kuwa ya yi shekara arbaminya da talatin, bayan haihuwar Feleg, ya kuma haifi ‘ya’ya mata da maza.

18 Sa’ad da Feleg ya yi shekara talatin ya haifi Reyu.

19 Feleg ya yi shekara metan da tara bayan haihuwar Reyu, ya kuma haifi ‘ya’ya mata da maza.

20 Sa’ad da Reyu ya yi shekara talatin da biyu ya haifi Serug.

21 Reyu kuwa ya yi shekara metan da bakwai bayan haihuwar Serug, ya kuma haifi ‘ya’ya mata da maza.

22 Sa’ad da Serug ya yi shekara talatin ya haifi Nahor,

23 Serug kuwa ya yi shekara metan bayan haihuwar Nahor, ya kuma haifi ‘ya’ya mata da maza.

24 Sa’ad da Nahor ya yi shekara ashirin da tara, ya haifi Tera,

25 Nahor kuwa ya yi shekara ɗari da goma sha tara bayan haihuwar Tera, ya kuma haifi ‘ya’ya mata da maza.

26 Sa’ad da Tera ya yi shekara saba’in, ya haifi Abram, da Nahor, da Haran.

27 Yanzu dai waɗannan su ne zuriyar Tera, Tera ya haifi Abram, da Nahor, da Haran, Haran kuwa shi ne ya haifi Lutu.

28 Haran kuwa ya rasu a idon mahaifinsa Tera a ƙasar haihuwarsa, a Ur ta Kaldiyawa.

29 Da Abram da Nahor suka yi aure, sunan matar Abram Saraya, sunan matar Nahor kuwa Milka, ita ‘yar Haran ce, mahaifin Milka da Iskaya.

30 Saraya kuwa ba ta haihuwa, wato ba ta da ɗa.

31 Sai Tera ya ɗauki ɗansa Abram da Lutu ɗan Haran, jikansa, da Saraya surukarsa, wato matar ɗansa Abram, suka tafi tare, daga Ur ta Kalidiyawa zuwa ƙasar Kan’ana, amma da suka isa Haran, suka zauna a can.

32 Kwanakin Tera shekara ce metan da biyar, Tera kuwa ya rasu a Haran.