FAR 6

Muguntar ‘Yan Adam

1 Da mutane suka fara yawaita a duniya suka kuwa haifi ‘ya’ya mata,

2 sai ‘ya’yan Allah suka ga ‘yan matan mutane kyawawa ne, suka zaɓi waɗanda suke so, suka aura.

3 Sai Ubangiji ya ce, “Numfashina ba zai zauna cikin mutum har abada ba, gama shi mai mutuwa ne. Nan gaba kwanakinsa ba zai ɗara shekara ɗari da ashirin ba.”

4 A waɗannan kwanaki kuwa, ‘ya’yan Allah suka shiga wurin ‘yan matan mutane, suka kuwa haifa musu ‘ya’ya. Su ne manya manyan mutanen dā, shahararru.

5 Ubangiji kuwa ya ga muguntar mutum ta ƙasaita a duniya, dukan zace-zacen tunanin zuciyarsa kuma mugunta ne kullayaumin.

6 Ubangiji ya damu da ya yi mutum a duniya, abin ya ɓata masa zuciya ƙwarai.

7 Sai Ubangiji ya ce, “Zan shafe mutum daga duniya, mutum da dabba, da masu rarrafe, da tsuntsayen sararin sama, gama na damu da na halicce su.”

8 Amma Nuhu ya sami tagomashi a gaban Ubangiji.

9 Waɗannan su ne zuriyar Nuhu. Nuhu adali ne, salihi ne kuma a cikin zamaninsa. Nuhu ya yi tafiya tare da Allah.

10 Nuhu kuwa ya haifi ‘ya’ya uku, Shem, da Ham, da Yafet.

11 Amma dukan sauran mutane mugaye ne a gaban Allah, muguntarsu kuwa ta bazu ko’ina.

12 Allah ya dubi duniya, ga shi kuwa ta ɓaci, gama dukan mutane sun lalatar da tafarkunsu a cikin duniya.

Nuhu ya Sassaƙa Jirgi

13 Allah ya ce wa Nuhu, “Na riga na yi niyyar hallaka dukan talikai, gama duniya tana cike da ayyukansu na zunubi.

14 Ka sassaƙa wa kanka jirgi na itacen gofer, ka yi ɗakuna a cikin jirgin, ka dalaye cikinsa da bayansa da ƙaro.

15 Ga yadda za ka sassaƙa shi, tsawon jirgin ƙafa ɗari huɗu da hamsin, faɗinsa ƙafa saba’in da biyar, tsayinsa ƙafa arba’in da biyar.

16 Ka yi wa jirgin rufe, ka bar inci goma sha takwas tsakanin rufin da gyaffansa. Ka yi shi hawa uku, ka yi ƙofa a gefe.

17 Gama ga shi, zan kawo rigyawa bisa duniya, ta hallaka dukan mai numfashin rai da yake ƙarƙashin sama, dukan abin da yake a duniya zai mutu.

18 Amma ni zan kafa alkawari tsakanina da kai, za ka shiga cikin jirgin, kai da ‘ya’yanka, da matarka, da matan ‘ya’yanka tare da kai.

19 Daga kowane irin mai rai kuma za ka shigar da biyu biyu a cikin jirgin, domin su rayu tare da kai, amma su kasance namiji da ta mace.

20 Tsuntsaye bisa ga irinsu, dabbobi bisa ga irinsu, da kowane irin mai rarrafe a ƙasa bisa ga irinsa, biyu biyu na kowane iri za su shiga tare da kai, su rayu.

21 Ka ɗauki kuma kowane irin abinci da ake ci, ka tanada, zai kuwa zama abincinka da nasu.”

22 Nuhu ya yi dukan abin da Allah ya umarce shi.