FAR 7

Ruwan Tsufana

1 Sai Ubangiji ya ce wa Nuhu, “Ka shiga jirgin, kai da iyalinka duka, gama na ga a wannan zamani, kai adali ne a gare ni.

2 Daga cikin dabbobi masu tsarki ka ɗauki bakwai bakwai, namiji da ta mace, marasa tsarki kuwa namiji da ta mace,

3 da kuma tsuntsayen sararin sama bakwai bakwai, namiji da ta mace, domin a wanzar da irinsu a duniya duka.

4 Gama da sauran kwana bakwai kāna in sa a yi ruwa a duniya yini arba’in da dare arba’in. Dukan abu mai rai wanda na yi zan shafe shi daga duniya.”

5 Nuhu kuwa ya yi dukan abin da Ubangiji ya umarce shi.

6 Nuhu yana da shekara ɗari shida lokacin da Ruwan Tsufana ya kwararo bisa duniya.

7 Nuhu da ‘ya’yansa da matarsa, da matan ‘ya’yansa tare da shi suka shiga jirgi, domin su tsira daga Ruwan Tsufana.

8 Daga dabbobi masu tsabta da marasa tsabta, da na tsuntsaye, da na kowane mai rarrafe a ƙasa,

9 biyu biyu, namiji da mata, suka shiga jirgi tare da Nuhu, kamar yadda Allah ya umarci Nuhu.

10 Sai bayan kwana bakwai ruwayen suka kwararo bisa duniya.

11 A ranar sha bakwai ga wata na biyu, na shekara ta ɗari shida na rayuwar Nuhu, a ran nan sai dukan maɓuɓɓugai na manyan zurfafa suka fashe, tagogin sammai suka buɗe.

12 Ruwa yana ta kwararowa bisa duniya yini arba’in da dare arba’in.

13 A wannan rana Nuhu da ‘ya’yansa, Shem, da Ham, da Yafet, da matar Nuhu da matan ‘ya’yansa tare suka shiga jirgin,

14 su da kowace dabbar jeji bisa ga irinta, da dukan dabbobin gida bisa ga irinsu, da kowane mai rarrafe wanda yake rarrafe bisa ƙasa, bisa ga irinsa, da kowane tsuntsun gida da na jeji wanda yake numfashi.

15-16 Su waɗanda suka shiga, namiji ne da ta mace na kowane taliki, suka shiga jirgin kamar yadda Allah ya umarce shi. Sai Ubangiji ya kulle jirgi daga baya.

17 Aka yi ta kwararo ruwa bisa duniya har kwana arba’in, ruwayen kuwa suka ƙaru, har suka ɗaga jirgin sama, ya kuwa tashi can ƙoli birbishin duniya.

18 Ruwa ya bunƙasa ya ƙaru ƙwarai bisa duniya, jirgin kuwa ya yi ta yawo bisa fuskar ruwaye.

19 Ruwa kuwa ya bunƙasa ainun a bisa duniya, har ya rufe kawunan dukan duwatsu masu tsayi da yake ƙarƙashin sammai duka.

20 Ruwa ya bunƙasa bisa duwatsu ya yi musu zara da ƙafa ashirin da biyar.

21 Duk taliki wanda yake motsi bisa duniya ya mutu, da tsuntsaye, da dabbobin gida, da na jeji, da dukan masu rarrafe waɗanda suke rarrafe bisa duniya, da kowane mutum,

22 da kowane abin da yake bisa sandararriyar ƙasa wanda yake da numfashin rai cikin kafafen hancinsa ya mutu.

23 Ubangiji ya shafe kowane mai rai wanda yake bisa ƙasa, da mutum, da dabba, da masu rarrafe, da tsuntsayen sararin sama, an shafe su daga duniya. Nuhu kaɗai aka bari, da waɗanda suke tare da shi cikin jirgi.

24 Ruwa kuma ya mamaye duniya har kwana ɗari da hamsin.