FAR 9

Allah ya Yi Alkawari da Nuhu

1 Allah kuwa ya sa wa Nuhu da ‘ya’yansa albarka, ya ce musu, “Ku yi ‘ya’ya ku hayayyafa, ku cika duniya.

2 Kowace dabba ta duniya, da kowane tsuntsu na sararin sama, da kowane mai rarrafe a ƙasa, da dukan kifaye na teku, za su riƙa jin tsoronku suna fargaba. An ba da su a hannunku.

3 Kowane abu mai motsi wanda yake da rai, zai zama abincinku. Daidai kamar yadda na ba ku ɗanyun ganyaye, na ba ku kome da kome.

4 Akwai abu ɗaya da ba za ku ci ba, shi ne naman da jininsa yake cikinsa, wato mushe.

5 Idan wani ya kashe ka zan hukunta shi da mutuwa. Zan kashe dabbar da za ta kashe ka, zan hukunta duk wanda ya kashe mutum ɗan’uwansa.

6 “Duk wanda ya kashe mutum, ta hannun mutum za a kashe shi, gama Allah ya yi mutum cikin siffarsa.

7 Amma ku, ku yi ‘ya’ya ku hayayyafa, ku riɓaɓɓanya a duniya ku yawaita a cikinta.”

8 Allah kuwa ya ce wa Nuhu da ‘ya’yansa.

9 “Ga shi, na kafa alkawari tsakanina da ku da zuriyarku a bayanku,

10 da kowane mai rai da yake tare da ku, da tsuntsaye, da dabbobin gida da na jeji, duk dai iyakar abin da ya fita daga jirgin, kowane mai rai na duniya.

11 Na kafa alkawarina da ku. Daɗai ba za a ƙara hallaka talikai duka da ruwa ba, ba kuma za a ƙara yin Ruwan Tsufana da zai hallaka duniya ba.”

12 Allah ya ce, “Wannan ita ce alamar alkawarin da yake tsakanina da ku, da kowane mai rai da yake tare da ku, har dukan zamanai masu zuwa,

13 na sa bakana cikin girgije, ya zama alamar alkawari tsakanina da duniya.

14 Sa’ad da na kawo gizagizai bisa duniya, aka ga bakan a cikin gizagizai,

15 zan tuna da alkawarin da yake tsakanina da ku, da kowane mai rai da dukan talikai. Ruwa kuma ba zai ƙara yin rigyawar da za ta hallaka talikai duka ba.

16 Sa’ad da bakan yake cikin girgije zan dube shi, in tuna da madawwamin alkawari tsakanin Allah da kowane mai rai da dukan talikan da suke bisa duniya.”

17 Allah ya ce wa Nuhu, “Wannan ita ce alamar alkawari wanda na kafa tsakanina da dukan talikan da suke bisa duniya.”

Nuhu da ‘Ya’yansa Maza

18 ‘Ya’yan Nuhu waɗanda suka fito daga jirgi su ne Shem, da Ham, da Yafet. Ham shi ne mahaifin Kan’ana.

19 Su uku ɗin nan su ne ‘ya’yan Nuhu, daga gare su duniya za ta cika da mutane.

20 Nuhu shi ya fara noma, ya yi gonar inabi.

21 Ya sha daga cikin ruwan inabin ya kuwa bugu, ya kwanta tsirara a cikin alfarwarsa.

22 Sai Ham, mahaifin Kan’ana, ya ga tsiraicin mahaifinsa, ya faɗa wa ‘yan’uwansa biyu waɗanda suke waje.

23 Sai Shem da Yafet suka ɗauki riga, suka ɗibiya bisa kafaɗunsu, suka yi tafiya da baya da baya suka rufa tsiraicin mahaifinsu, suka juya fuskokinsu, ba su kuwa ga tsiraicin mahaifinsu ba.

24 Sa’ad da ruwan inabin ya sau Nuhu, ya san abin da ƙaramin ɗansa ya yi masa.

25 Sai ya ce, “La’ananne ne Kan’ana, bawan bayi zai zama ga ‘yan’uwansa.”

26 Ya kuma ce, “Bari Ubangiji Allahna, ya sa wa Shem albarka, Kan’ana kuwa ya bauta masa.

27 Allah ya sa Yafet ya yawaita, ya sa ya zauna a alfarwan Shem, Kan’ana kuwa ya bauta masa.”

28 Bayan Ruwan Tsufana, Nuhu ya yi shekara ɗari uku da hamsin.

29 Shekarun Nuhu duka ɗari tara da hamsin ne, ya rasu.