FIT 21

Yadda Za a Yi da Bayi

1 “Waɗannan su ne ka’idodin da za a ba Isra’ilawa.

2 Idan ka sayi bawa Ba’ibrane, zai yi bauta shekara shida, a shekara ta bakwai kuwa, a ‘yantar da shi kyauta.

3 Idan yana shi kaɗai aka saye shi, sai ya fita shi kaɗai, idan kuwa yana da aure sa’ad da aka saye shi, sai matarsa ta fita tare da shi.

4 Idan kuwa ubangijinsa ne ya auro masa matar, ta kuwa haifa masa ‘ya’ya mata ko maza, to, matar da ‘ya’yanta za su zama na ubangijinsa, amma shi kaɗai zai fita.

5 Amma idan hakika bawa ya hurta ya ce, yana ƙaunar ubangijinsa, da matarsa, da ‘ya’yansa, ba ya son ‘yancin,

6 to, sai ubangijinsa ya kawo shi a gaban Allah a ƙofa ko a madogarar ƙofa, sa’an nan ubangijinsa ya huda kunnensa da abin hudawa. Zai bauta wa ubangijinsa muddin ransa.

7 “Idan mutum ya sayar da ‘yarsa kamar baiwa, ba za a ‘yanta ta kamar bawa ba.

8 Idan ba ta gamshi maigidanta wanda ya maishe ta kamar ɗaya daga cikin matansa ba, sai ya yarda a fanshe ta. Amma ba shi da iko ya sayar da ita ga baƙi, tun da yake bai kyauta mata ba.

9 Idan ya ba da ita ga ɗansa ne sai ya maishe ta kamar ‘yarsa.

10 In mutumin ya auri wata kuma, ba zai hana wa baiwar abinci da sutura ba, ba kuma zai ƙi kwana da ita ba.

11 Idan kuwa bai cika mata wajiban nan uku ba, sai ta fita abinta, ba zai karɓi kome ba.”

Dokoki game da Nuna Ƙarfi da Yaji

12 “Duk wanda ya bugi mutum har ya kashe shi, lalle, shi ma sai a kashe shi.

13 In ba da nufi ya kashe shi ba, amma tsautsayi ne, to, sai mutumin ya tsere zuwa inda zan nuna muku.

14 Amma idan mutum ya fāɗa wa ɗan’uwansa da niyyar kisankai, lalle, sai a kashe shi ko da ya gudu zuwa bagadena.

15 “Wanda ya bugi mahaifinsa ko mahaifiyarsa, lalle, kashe shi za a yi.

16 “Wanda ya saci mutum, ya sayar, ko kuwa a iske shi a hannunsa, lalle kashe shi za a yi.

17 “Wanda ya raina mahaifinsa ko mahaifiyarsa, lalle kashe shi za a yi.

18 “Idan mutane suka yi faɗa, ɗayan ya jefa ɗayan da dutse, ko ya naushe shi amma bai mutu ba, sai dai ya yi ta jiyya,

19 idan mutumin ya sāke tashi ya yi tafiya ko da yana dogarawa da sanda, wanda ya buge shi zai kuɓuta, sai dai zai biya diyyar lokacin da ya ɓāta masa, ya kuma lura da shi har ya warke sarai.

20 “In mutum ya dūki bawansa ko baiwarsa da sanda har ya mutu a hannunsa, lalle ne a hukunta shi.

21 Amma idan bawan ya rayu kwana ɗaya ko biyu, to, kada a hukunta shi, gama bawan dukiyarsa ne.

22 “Idan mutum biyu na faɗa, har suka yi wa mace mai ciki rauni, har ya sa ta yi ɓari, amma wani lahani bai same ta ba, za a ci wa wanda ya yi mata raunin tara bisa ga yadda mijinta ya yanka zai biya, in dai abin da ya yanka ya yi daidai da abin da alƙalai suka tsara.

23 Amma in wani lahani ya auku, to, sai a hukunta rai a maimakon rai,

24 ido a maimakon ido, haƙori a maimakon haƙori, hannu a maimakon hannu, ƙafa a maimakon ƙafa,

25 ƙuna a maimakon ƙuna, rauni a maimakon rauni, ƙujewa a maimakon ƙujewa.

26 “Idan mutum ya bugi bawansa ko baiwarsa a ido har idon ya lalace, sai ya ‘yanta bawan ko baiwar a maimakon idon.

27 Idan ya fangare haƙorin bawansa ko na baiwarsa, sai ya ‘yanta bawan ko baiwar a maimakon haƙorin.”

Hakkin Masu Abu

28 “Idan sa ya kashe ko mace ko namiji, to, lalle ne a jajjefi san da duwatsu, kada kuma a ci namansa, mai san kuwa zai kuɓuta.

29 Amma idan san ya saba fafarar mutane, aka kuma yi wa mai shi kashedi, amma bai kula ba, har san ya kashe ko mace ko namiji, sai a jajjefi san duk da mai shi.

30 Idan an yanka masa diyya, sai ya biya iyakar abin da aka yanka masa don ya fanshi ransa.

31 Haka kuma za a yi idan san ya kashe ɗan wani ko ‘yar wani.

32 Idan san ya kashe bawa ko baiwa, sai mai san ya biya wa ubangijin bawan, ko baiwar, shekel talatin a kuma jajjefi san.

33 “Idan mutum ya bar rami a buɗe, ko ya haƙa rami bai rufe ba, in sa ko jaki ya fāɗa ciki,

34 mai ramin zai biya mai san ko mai jakin, mushen ya zama nasa.

35 Idan san wani ya yi wa na wani rauni har ya mutu, sai ya sayar da san da yake da rai a raba kuɗin. Haka kuma za su raba mushen.

36 Amma idan dā ma an sani san mafaɗaci ne, mai san kuwa bai kula da shi ba, sai ya biya, wato ya ba da sa a maimakon mushen. Mushen kuwa zai zama nasa.”