FIT 25

Sadakoki domin Yin Wuri Mai Tsarki

1 Ubangiji ya ce wa Musa,

2 “Faɗa wa Isra’ilawa su karɓo mini kaya daga dukan wanda ya yi niyyar bayarwa.

3 Ga irin sadakokin da za ku karɓa, zinariya, da azurfa, da tagulla,

4 da ulu mai launin shuɗi, da mai launin shunayya, da mai launin ja, da lilin mai laushi, da gashin akuya,

5 da jemammun fatun raguna, da fatun awaki, da itacen ƙirya,

6 da mai domin fitila, da kayan yaji domin man keɓewa, da turaren ƙonawa,

7 da onis, da duwatsun da za a mammanne a falmaran da ƙyallen maƙalawa a ƙirji.

8 Za su yi tsattsarkan wuri domina, don in zauna tare da su.

9 Za ku yi mazaunina da kayayyakinsa duka, bisa ga irin fasalin da zan nuna maka.”

Akwatin Alkawari

10 “Sai ku yi akwatin alkawari da itacen maje, tsawonsa ya zama kamu biyu da rabi, fāɗinsa kuwa kamu ɗaya da rabi, tsayinsa ya zama kamu ɗaya da rabi.

11 Ku dalaye shi da zinariya tsantsa ciki da waje. Ku yi wa gyaffansa ado da gurun zinariya.

12 Za ku yi wa akwatin ƙawanya huɗu na zinariya ku liƙa a kowace kusurwar akwatin, wato ƙawanya biyu a kowane gefe na tsawon.

13 Za ku kuma yi sanduna da itacen ƙirya, ku dalaye su da zinariya.

14 Ku sa sandunan a kafar kowace ƙawanya da take gyaffan akwatin saboda ɗaukarsa.

15 Za a bar sandunan cikin ƙawanen akwatin, kada a zare su.

16 A kuma sa allunan da suke da dokokin da zan ba ka a cikin akwatin.

17 “Za ku yi wa akwatin murfi da zinariya tsantsa, tsawonsa kamu biyu da rabi, fāɗinsa kuma kamu ɗaya da rabi.

18 Za ku yi siffofin kerubobi biyu da ƙerarriyar zinariya, ku sa a gefen nan biyu na murfin.

19 Siffar kerub ɗaya a kowane gefe. Ku yi su ta yadda za su zama ɗaya da murfin.

20 Fikafikan kerubobin za su miƙe bisa domin su inuwantar da murfin, za su fuskanci juna, suna duba murfin.

21 Za ku sa murfin bisa akwatin. A cikin akwatin kuwa za ku sa allunan da suke da dokokin da zan ba ka.

22 A nan zan zo in sadu da kai, in yi magana da kai, wato tsakanin kerubobi biyu da suke bisa akwatin alkawari. Zan ba ka umarnaina duka don Isra’ilawa.”

Teburin Gurasar Ajiyewa ga Ubangiji

23 “Ku yi tebur da itacen ƙirya, tsawonsa kamu biyu, fāɗinsa kamu ɗaya, tsayinsa kuma kamu ɗaya da rabi.

24 Ku dalaye shi da zinariya tsantsa, ku kuma yi masa ado kewaye da gurun zinariya.

25 Za ku yi wa tebur ɗin dajiya mai fāɗin tafin hannu, ku kuma yi wa dajiyar ado da gurun zinariya.

26 Za ku yi ƙawanya huɗu da zinariya, ku sa a kusurwa huɗu na ƙafafun teburin.

27 Ƙawanen za su kasance kusa da dajiyar don su riƙe sandunan ɗaukar teburin.

28 Ku yi sanduna da itacen ƙirya, sa’an nan ku dalaye su da zinariya. Da su za a riƙa ɗaukar teburin.

29 Da zinariya tsantsa kuma za ku yi farantansa, da kwanonin tuya, da butocinsa, da kwanoninsa domin yin hadayu na sha.

30 Kullum za ku riƙa ajiye gurasar da kuke kawo mini a bisa teburin.”

Alkuki

31 “Ku kuma yi alkuki da zinariya tsantsa. Ku yi gindinsa da gorar jikinsa da ƙerarriyar zinariya. Ƙoƙuna, da mahaɗai, da furanninsa a haɗe da shi za ku yi su.

32 Alkukin ya kasance da rassa shida, rassa uku a kowane gefe.

33 A kowane reshe na alkuki za a yi ƙoƙuna uku masu kamar tohon almond. Ya kasance kuma da mahaɗai da furanni.

34 Za a yi wa gorar alkukin ƙoƙuna huɗu masu kamar tohon almond, da mahaɗai da furanni.

35 A gindin kowane reshe biyu za a yi mahaɗi ɗaya.

36 Da mahaɗai da rassan za su kasance a haɗe da alkukin. Da ƙerarriyar zinariya za a yi su.

37 Ku kuma yi fitilu bakwai, ku sa su a bisa alkukin ta yadda za su haskaka wajen da suka fuskanta.

38 Ku kuma yi hantsuka da farantai da zinariya tsantsa.

39 Da zinariya tsantsa na talanti ɗaya za ku yi alkukin da waɗannan abubuwa duka.

40 Sai ku lura, ku yi waɗannan abubuwa duka bisa ga fasalin da aka nuna maka a bisa dutsen.”