FIT 27

Bagade

1 “Za ku yi bagaden da itacen ƙirya, mai tsawo kamu biyar, da fāɗi kamu biyar, tsayinsa kamu uku. Bagaden zai zama murabba’i.

2 A yi masa zankaye a kusurwoyinsa. Za ku haɗa zankayen da jikin bagaden. Za ku dalaye bagaden duka da tagulla.

3 Za ku ƙera kwanoni domin tokar bagade, da manyan cokula da daruna, da cokula masu yatsotsi, da kuma farantai domin wuta. Za ku ƙera dukan kayayyakin bagaden da tagulla.

4 Za ku kuma yi wa bagaden raga da tagulla, sa’an nan ku sa wa ragar ƙawane a kusurwoyinta huɗu.

5 Za ku sa ragar a cikin bagaden a tsakiya.

6 Ku yi wa bagaden sanduna da itacen ƙirya, sa’an nan ku dalaye su da tagulla.

7 Za a zura sandunan a ƙawanen da suke gyaffan bagade don ɗaukarsa.

8 Za ku yi bagaden da katakai, sa’an nan ku roɓe cikinsa. Ku yi shi bisa ga fasalin da na nuna maka bisa dutsen.

Farfajiyar Alfarwar

9 “Za ku yi wa alfarwa farfajiya. A kudancin farfajiyar, sai ku rataye labule mai tsawo kamu ɗari wanda aka saƙa da lallausan zaren lilin.

10 Za ku yi masa dirkoki guda ashirin, da kwasfansu guda ashirin da tagulla, amma ku yi wa dirkokin maratayai da maɗaurai da azurfa.

11 A wajen arewa kuma, sai ku rataya labule mai tsawon kamu ɗari. Ku yi masa dirkoki da kwasfansu guda ashirin da tagulla, amma ku yi wa dirkokin maratayai da maɗaurai da azurfa.

12 Fāɗin labulen a wajen yamma na farfajiyar, zai zama kamu hamsin. A yi wa labulen dirkoki goma, a kuma yi wa dirkokin kwasfa goma.

13 Fāɗin labulen wajen gabas na farfajiyar zai zama kamu hamsin.

14 Labulen ƙofa na gefe ɗaya zai zama kamu goma sha biyar, da dirkoki uku tare da kwasfansu uku.

15 Haka kuma labulen ƙofa na wancan gefe zai zama kamu goma sha biyar, da dirkoki uku tare da kwasfansu uku.

16 Za a saƙa labule mai kamu ashirin da lallausan zaren lilin mai launi shuɗi, da shunayya, da mulufi domin ƙofar farfajiyar. Za a sa wa ƙofar dirkoki huɗu tare da kwasfansu huɗu.

17 Za a yi wa dukan dirkokin da suke kewaye da farfajiyar maɗaurai da maratayai na azurfa, da kwasfa ta tagulla.

18 Tsawon farfajiyar zai zama kamu ɗari, fāɗinta kamu hamsin, tsayinta kamu biyar. Za a saƙa labulenta da lallausan zaren lilin, a kuma yi kwasfanta da tagulla.

19 Da tagulla kuma za a yi turakun alfarwar, da turakun farfajiyar, da dukan kayayyakin da za a yi amfani da su a cikin alfarwar.”

Kulawa da Fitila

20 “Sai a umarci Isra’ilawa su kawo tsabtataccen man zaitun tatacce domin fitilar. Za a kunna fitilar ta yi ta ci koyaushe.

21 Za a ajiye ta a cikin alfarwar a gaban labule na wurin shaida. Haruna da ‘ya’yansa za su lura da ita daga safiya har maraice. Wannan zai zama ka’ida har abada ga Isra’ilawa.”