FIT 35

Ka’idodin Ranar Hutawa

1 Sai Musa ya tattara dukan taron jama’ar Isra’ila, ya ce musu, “Waɗannan su ne abubuwan da Ubangiji ya umarce ku ku yi.

2 Cikin kwana shida za a yi aiki, amma rana ta bakwai Asabar ce tsattsarka ta Ubangiji ta hutawa sosai. Duk wanda ya yi kowane irin aiki a cikinta, sai a kashe shi.

3 Ba za ku hura wuta a ranar Asabar a wuraren zamanku ba.”

Sadaka domin Yin Alfarwa ta Sujada

4 Musa kuma ya ce wa taron jama’ar Isra’ila duka, “Wannan shi ne abin da Ubangiji ya umarta,

5 ku karɓi sadaka daga cikinku saboda Ubangiji. Duk wanda ya yi niyya, bari ya kawo wa Ubangiji sadaka ta zinariya, da azurfa, da tagulla,

6 da zane na shuɗi, da na shunayya, da na mulufi, da na lallausan zaren lilin, da gashin awaki,

7 da fatun raguna da aka rina suka zama ja, da fatun awaki, da itacen ƙirya,

8 da man fitila, da kayan yaji domin man keɓewa da turaren ƙonawa,

9 da duwatsu masu tamani, da duwatsun da za a mammanne a falmaran da ƙyallen maƙalawa a ƙirji.”

Kayayyakin Alfarwa ta Sujada

10 “Bari dukan wanda yake da fasaha a cikinku ya zo, ya yi aikin da Ubangiji ya umarta a yi,

11 wato aikin alfarwa ta sujada, da alfarwarta da murfinta, da maratayai, da katakanta da sandunanta, da dirkokinta, da kwasfanta,

12 da akwati da sandunansa, da murfinsa, da labulen ƙofar.

13 Da tebur da sandunansa, da kayayyakinsa duka, da gurasar ajiyewa,

14 da alkuki don haske, da kayayyakinsa, da fitilunsa, da man fitila,

15 da bagaden turaren ƙonawa da sandunansa, da man keɓewa mai ƙanshi, da turaren ƙonawa, da labulen ƙofar alfarwa ta sujada,

16 da bagaden ƙona hadaya da ragarsa ta tagulla da sandunansa, da kayayyakinsa duka, da daro da gammonsa,

17 da labulen farfajiya da dirkokinsa da kwasfansu, da labulen ƙofar farfajiyar,

18 da turakun alfarwa, da turakun farfajiyar, da igiyoyinsu,

19 da saƙaƙƙun tufafi na yin aiki a Wuri Mai Tsarki, da tsarkakakkun tufafin Haruna firist, da tufafin ‘ya’yansa maza na aikin firist.”

Jama’a sun Kawo Sadaka

20 Sa’an nan dukan taron jama’ar Isra’ila suka tashi daga wurin Musa.

21 Duk wanda ya yi niyya, da wanda ruhunsa ya iza shi ya kawo wa Ubangiji sadaka don yin alfarwa ta sujada, da dukan ayyukansa, da tsarkakakkun tufafi.

22 Sai dukan mata da maza waɗanda suke da niyya, suka kawo kayayyakin ƙawanya, wato da ‘yan kunne, da ƙawane, da mundaye, da kayayyakin zinariya iri iri. Kowane mutum ya ba da sadaka ta zinariya ga Ubangiji.

23 Kowane mutum da aka iske shi yana da shuɗi, ko shunayya, ko mulufi, ko lallausan lilin, ko gashin awaki, ko fatun raguna da aka rina suka zama ja, ko fatun awaki, ya kawo su.

24 Kowane ne wanda ya iya, ya ba da sadaka ta azurfa, da ta tagulla ga Ubangiji. Duka kuma wanda aka iske shi yana da itacen ƙirya wanda zai yi amfani a cikin aikin, ya kawo shi.

25 Dukan mata masu hikima suka kaɗa zare da hannuwansu, suka kawo zaren da suka kaɗa na shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan lilin.

26 Sai kuma dukan mata masu hikima, waɗanda zuciyarsu ta iza su, suka kaɗa zare da gashin awaki.

27 Su shugabanni suka kawo duwatsu masu daraja da za a jera a kan falmaran da ƙyallen maƙalawa a ƙirji.

28 Suka kuma kawo kayan yaji, da man fitila, da man keɓewa, da turaren ƙonawa.

29 Sai dukan mata da maza na Isra’ilawa waɗanda zuciyarsu ta iza su, suka kawo kowane irin abu domin yin aikin da Ubangiji ya umarci Musa. Suka kawo sadaka ta yardar rai ga Ubangiji.

Waɗanda Suka Yi Aikin Alfarwa ta Sujada

30 Sai Musa ya ce wa Isra’ilawa, “Ga shi, Ubangiji ya zaɓi Bezalel ɗan Uri, ɗan Hur, na kabilar Yahuza.

31 Ya cika shi da ruhu na hikima, da basira, da sani, da fasaha na iya yin kowane irin aiki.

32 Domin ƙirƙiro zāne-zāne na gwaninta, waɗanda za a yi da zinariya, da azurfa, da tagulla.

33 Haka kuma wajen sassaƙar duwatsu na jerawa, da sassaƙar itace, da kowane irin aiki na gwaninta.

34 Ubangiji ya ba Bezalel, da Oholiyab ɗan Ahisamak, na kabilar Dan, hikimar koya wa waɗansu sana’a.

35 Gama ya cika su da hikima ta yin kowane irin aiki na sassaƙa da na zāne-zāne, da na yin ɗinke-ɗinke da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan lilin, da na yin saƙa. Sun iya yin kowane irin aiki da yin zāne-zāne.