FIT 8

Annobar Kwaɗi

1 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Tafi wurin Fir’auna, ka ce masa, ‘Ubangiji ya ce ka saki jama’arsa domin su yi masa sujada.

2 Idan ka ƙi sakinsu, zai hore ka da kwaɗi.

3 Nilu zai cika da kwaɗi, za su tashi, su shiga cikin fādarka, da ɗakin kwanciyarka, da gadonka, har da gidajen fadawanka da jama’arka. Za su kuma shiga matuyanka da kwanon tuwonka,

4 har ma za su hau bisa kanka, da jama’arka, da dukan fādawanka.’ ”

5 Sai Ubangiji ya ce wa Musa ya faɗa wa Haruna ya miƙa sandansa a bisa koguna, da rufuffuka, da tafkuna don ya sa kwaɗi su fito, su rufe ƙasar Masar.

6 Haruna ya miƙa sandansa a bisa ruwayen Masar, kwaɗi kuwa suka fito, suka rufe ƙasar Masar.

7 Masu sihiri kuma suka sa kwaɗi su fito a bisa ƙasar Masar ta wurin sihirinsu.

8 Sai Fir’auna ya kirawo Musa da Haruna, ya ce su roƙi Ubangiji ya kawar masa da kwaɗin, shi da mutanensa, sa’an nan zai saki jama’ar, su tafi su miƙa wa Ubangiji hadaya.

9 Musa ya ce wa Fir’auna, “In ka yarda, a wane lokaci ne kake so in roƙa maka, kai da barorinka da jama’arka domin a kawar da kwaɗin daga gidajenku, a hallakar muku da su, sai dai na cikin Kogin Nilu za a bari?”

10 Fir’auna ya ce, “Gobe ne.”

Musa kuwa ya ce, “Za a yi kamar yadda ka faɗa, domin ka sani babu wani allah kamar Ubangiji Allahnmu.

11 Kwaɗin za su rabu da ku, da kai, da gidanka, da fādawanka, da jama’arka, sai na cikin Nilu kaɗai za a bari.”

12 Da Musa da Haruna suka fita daga gaban Fir’auna, sai Musa ya roƙi Ubangiji ya kawar da kwaɗin nan da suka azabta wa Fir’auna.

13 Ubangiji kuwa ya karɓi addu’ar Musa, sai kwaɗin da suke cikin gida da waɗanda suke kewaye da gida, da waɗanda suke cikin saura suka mutu.

14 Aka tsiba su tsibi tsibi. Suka sa ƙasar ta yi ɗoyi.

15 Da Fir’auna ya ga an kawar masa da kwaɗin, sai ya taurare zuciyarsa, ya ƙi jinsu kamar yadda Ubangiji ya riga ya faɗa.

Annobar Kwarkwata

16 Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa ya faɗa wa Haruna ya miƙa hannunsa ya bugi ƙurar ƙasar, ta zama kwarkwata a ƙasar Masar.

17 Haka kuwa suka yi. Haruna ya miƙa sandansa ya bugi ƙurar ƙasa, sai ta zama kwarkwata a bisa ‘yan adam, da bisa dabbobi. Dukan ƙurar ta zama kwarkwata ko’ina cikin ƙasar Masar.

18 Masu sihiri suka ƙokarta su sa kwarkwata ta bayyana ta wurin sihirinsu, amma ba su iya ba. Kwarkwata kuma ta yayyaɓe ‘yan adam da dabbobi.

19 Sai masu sihiri suka ce wa Fir’auna, “Ai, wannan aikin Allah ne.” Amma zuciyar Fir’auna ta taurare, har da bai kasa kunne ga Musa da Haruna ba, kamar yadda Ubangiji ya riga ya faɗa.

Annobar Ƙudaje

20 Ubangiji ya ce wa Musa, “Tashi da sassafe ka sami Fir’auna a daidai lokacin da ya fita za shi rafi, ka ce masa, ‘Ni Ubangiji na ce ka saki jama’ata domin su yi mini sujada.

21 In kuwa ka ƙi sakin jama’ata, sai in koro maka ƙudaje, da kai da fādawanka, da jama’arka, da gidajen Masarawa, har ma duk da ƙasa inda suke takawa.

22 A wannan rana fa zan keɓe ƙasar Goshen inda jama’ata suke don kada ƙudaje su taɓa wurin, ta haka ne za ka sani ni Ubangiji ina nan a duniya.

23 Zan sa iyaka tsakanin jama’ata da jama’arka. Gobe ne wannan mu’ujiza za ta auku.”’

24 Haka kuwa Ubangiji ya aikata. Ƙudaje masu yawa suka shiga gidan Fir’auna, da gidan fādawansa, da ko’ina a ƙasar Masar. Ƙasar kuwa ta lalace saboda ƙudaje.

25 Sa’an nan Fir’auna ya kirawo Musa da Haruna, ya ce, “Tafi, ku yi wa Allahnku hadaya a ƙasan nan.”

26 Amma Musa ya ce, “Ba zai kyautu a yi haka ba, gama irin dabbobin da za mu miƙa wa Ubangiji Allahnmu hadaya da su, haramu ne ga Masarawa. Idan fa muka miƙa hadaya da waɗannan dabbobi da suke haramu a idon Masarawa za su jajjefe mu da duwatsu.

27 Za mu yi tafiya kwana uku a jeji kafin mu miƙa hadaya ga Ubangiji Allahnmu kamar yadda ya umarce mu.”

28 Sai Firauna ya ce, “Zan bar ku ku tafi, ku miƙa wa Ubangiji Allahnku hadaya a jeji, sai dai kada ku tafi da nisa. Ku kuma yi mini addu’a.”

29 Musa kuwa ya ce, “Nan da nan da tashina daga gabanka, zan yi addu’a ga Ubangiji, ƙudajen kuwa za su rabu da kai, da fādawanka, da jama’arka gobe, kada ka sāke yin ruɗi, ka ƙi barin jama’ar su tafi, su miƙa wa Ubangiji hadaya.”

30 Musa ya fita daga wurin Fir’auna, ya roƙi Ubangiji.

31 Ubangiji kuwa ya aikata bisa ga roƙon Musa. Ƙudajen suka rabu da Fir’auna, da fādawansa, da jama’arsa. Ko ƙuda ɗaya bai ragu ba.

32 Duk da haka Fir’auna ya taurare zuciyarsa a wannan lokaci kuma, ya ƙi sakin jama’ar.