JOSH 16

Yankin Ƙasar da Aka Ba Ifraimu da Manassa

1 Rabon zuriyar Yusufu ya milla tun daga Urdun zuwa wajen Yariko, gabas da ruwan Yariko zuwa jejin. Ya haura daga Yariko zuwa ƙasar tuddai zuwa Betel.

2 Daga Betel ya miƙa zuwa Luz, sa’an nan ya zarce zuwa Atarot, karkarar Arkiyawa.

3 Sai ya gangara yamma zuwa karkarar Yafletiyawa har zuwa karkarar Bet-horon wadda take cikin kwari. Ya zarce kuma zuwa Gezer, sa’an nan ya gangara a teku.

4 A nan ne jama’ar Yusufu, wato Manassa da Ifraimu, suka sami nasu gādo.

5 Karkarar jama’ar Ifraimu, bisa ga iyalansu, ita ce iyakar gādonsu a wajen gabas, wato ita ce Atarot-addar har zuwa Bet-horon wadda take kan tudu.

6 Daga can iyakar ta miƙa zuwa teku ta bar Mikmetat a wajen arewa. A wajen gabas kuwa iyakar ta karkata zuwa Ta’anat-Shilo, daga can sai ta zarce gaba a wajen gabas zuwa Yanowa.

7 Daga Yanowa sai ta gangara zuwa Atarot da Nayaran, ta kuma gegi Yariko, sa’an nan ta gangara a Urdun.

8 Daga Taffuwa, sai iyakar ta yi yamma zuwa rafin Kana, sa’an nan ta gangara a teku. Wannan shi ne gādon Ifraimawa bisa ga iyalansu,

9 tare da garuruwan da ƙauyukan da aka keɓe wa Ifraimawa daga cikin gādon jama’ar Manassa.

10 Amma ba su kori Kan’aniyawa da suke zaune a Gezer ba, don haka Kan’aniyawa ka zauna tare da Ifraimawa har wa yau, amma Kan’aniyawa suka zama bayi masu yin aikin dole.