JOSH 17

1 Aka ba kabilar Manassa, ɗan farin Yusufu, nata rabon gādo. Makir ɗan farin Manassa, uban Gileyad, aka ba shi Gileyad da Bashan domin shi jarumi ne.

2 Aka kuma raba wa sauran mutanen kabilar Manassa nasu rabon gādo bisa ga iyalansu, wato Abiyezer, da Helek, da Asriyel, da Shekem, da Hefer, da Shemida. Waɗannan su ne ‘ya’yan Manassa, maza, bisa ga iyalansu.

3 Zelofehad kuwa ɗan Hefer, ɗan Gileyad, ɗan Makir, ɗan Manassa ba shi da ‘ya’ya maza, sai dai mata. Sunayensu ke nan, Mala, da Nowa, da Hogla, da Milka, da Tirza.

4 Suka zo wurin Ele’azara firist, da Joshuwa ɗan Nun, da shugabannin, suka ce, “Ubangiji ya umarci Musa ya ba mu gādo tare da ‘yan’uwanmu maza.” Sai ya ba su gādo tare da ‘yan’uwan mahaifinsu bisa ga umarnin Ubangiji.

5 Saboda haka kuwa Manassa ya sami kashi goma banda ƙasar Gileyad da Bashan da yake hayin gabashin Urdun,

6 domin jikokin Manassa mata sun sami gādo tare da jikokinsa maza. Aka ba sauran mutanen kabilar Manassa ƙasar Gileyad.

7 Yankin ƙasar Manassa ya kai daga Ashiru zuwa Mikmetat wadda take gabas da Shekem. Iyakar kuma ta miƙa kudu zuwa mazaunan En-taffuwa.

8 Ƙasar Taffuwa tana hannun mutanen Manassa, amma mutanen Ifraimu ne suke da garin Taffuwa wanda yake iyakar yankin Manassa.

9 Iyakar kuma ta gangara zuwa rafin Kana. Waɗannan birane da suke kudancin rafin, na Ifraimu ne, ko da yake suna cikin biranen Manassa. Iyakar Manassa kuwa ta bi gefen arewacin rafin ta gangara a Bahar Rum.

10 Ƙasar wajen kudu ta Ifraimu ce, ta wajen arewa kuwa ta Manassa. Bahar Rum ita ce iyakarsu. Mutanen Ashiru suna wajen arewa, mutanen Issaka kuwa wajen gabas.

11 A yankin ƙasar Issaka da na Ashiru, Manassa yana da waɗannan wurare, Bet-sheyan da ƙauyukanta, da Ibleyam da ƙauyukanta, da mazaunan Dor da ƙauyukanta, da mazaunan Endor da ƙauyukanta, da mazaunan Ta’anak da ƙauyukanta, da mazaunan Magiddo da ƙauyukanta, da sulusin Nafat.

12 Amma mutanen Manassa ba su iya su mallaki waɗannan birane ba, don haka Kan’aniyawa suka yi zamansu a wuraren.

13 Amma sa’ad da Isra’ilawa suka yi ƙarfi sai suka tilasta su su yi musu aikin dole, amma ba su iya korarsu ba.

14 Kabilan Yusufu suka ce wa Joshuwa, “Me ya sa ka ba mu rabon gādo guda ɗaya? Ga shi kuwa, muna da jama’a mai yawa, gama Ubangiji ya sa mana albarka.”

15 Joshuwa kuwa ya amsa musu, ya ce, “Idan ku babbar jama’a ce, har ƙasar tuddai ta Ifraimu ta kāsa muku, to, sai ku shiga jeji ku sheme wa kanku wuri a ƙasar Ferizziyawa da ta Refayawa.”

16 Sai mutanen kabilan Yusufu suka ce, “Ƙasar tuddai ba ta ishe mu ba, ga kuma Kan’aniyawa da suke zaune a filin, da waɗanda suke a Bet-sheyan da ƙauyukanta, da waɗanda suke cikin Kwarin Yezreyel suna da karusan ƙarfe.”

17 Joshuwa kuma ya ce wa jama’ar gidan Yusufu, wato kabilar Ifraimu da ta Manassa, “Ku babbar jama’a ce, ga shi kuma, kuna da ƙarfi, ba kashi ɗaya kaɗai za ku samu ba,

18 amma ƙasar tuddai kuma za ta zama taku, ko da yake jeji ne. Sai ku sheme, ku mallaka duka. Gama za ku kori Kan’aniyawa, ko da yake su ƙarfafa ne, suna kuma da karusan ƙarfe.”