JOSH 3

Isra’ilawa Sun Haye Urdun

1 Joshuwa kuwa ya tashi da sassafe, da shi da dukan jama’ar Isra’ila, suka kama hanya daga Shittim zuwa Urdun, inda suka sauka kafin su haye.

2 Bayan kwana uku sai shugabannin jama’a suka bibiya zango,

3 suna umartar jama’ar suna cewa, “Sa’ad da kuka ga akwatin alkawari na Ubangiji Allahnku, sai ku tashi daga inda kuke, ku bi shi,

4 domin ku san hanyar da za ku bi, gama ba ku taɓa bin hanyar ba. Sai dai tsakaninku da shi za ku bar rata misalin nisan kamu dubu biyu, kada ku kusace shi.”

5 Sai Joshuwa ya ce wa jama’a, “Ku tsarkake kanku, gama gobe Ubangiji zai aikata abin al’ajabi a tsakiyarku.”

6 Ya kuma ce wa firistocin, “Ku ɗauki akwatin alkawari ku wuce gaban jama’ar.” Sai suka ɗauki akwatin alkawari suka wuce gaban jama’a.

7 Ubangiji kuwa ya ce wa Joshuwa, “A yau ɗin nan zan fara ɗaukaka ka a gaban dukan Isra’ilawa domin su sani, kamar yadda na kasance tare da Musa, haka kuwa zan kasance tare da kai.

8 Ka umarci firistocin da suke ɗauke da akwatin alkawari cewa, ‘Sa’ad da kuka shiga gefen ruwan Urdun, sai ku tsaya cik a wurin.’ ”

9 Joshuwa kuma ya ce wa Isra’ilawa, “Ku kusato ku ji zantuttukan Ubangiji Allahnku.”

10 Joshuwa kuma ya ƙara da cewa, “Ta haka za ku sani Allah mai rai yana tsakiyarku, ba makawa kuwa zai kori Kan’aniyawa, da Hittiyawa, da Hiwiyawa, da Ferizziyawa, da Girgashiyawa, da Amoriyawa, da Yebusiyawa a gabanku.

11 Ga shi, akwatin alkawari na Ubangijin dukkan duniya yana wucewa a gabanku zuwa cikin Urdun.

12 Yanzu fa, ku ɗauki mutum goma sha biyu daga kabilanku, wato mutum ɗaya daga kowace kabila.

13 A sa’ad da firistocin da suke ɗauke da akwatin alkawarin Ubangiji, Ubangijin dukkan duniya, suka tsoma tafin sawunsu cikin ruwan Urdun, ruwan Urdun zai yanke, ruwan da yake gangarowa zai tsaya tsibi guda.”

14-15 (Da kaka Urdun yakan yi cikowa makil.) Jama’a fa, suka tashi daga alfarwansu don su haye Urdun. Firistocin da suke ɗauke da akwatin alkawari suna gaba. Da firistocin suka tsoma ƙafafunsu cikin ruwa daga gefe,

16 sai ruwan da yake gangarowa ya tsaya, ya tattaru wuri ɗaya, ya yi soro daga nesa kusa da Adam, birnin da yake kusa da Zaretan. Ruwan kuma da yake gangarowa zuwa Tekun Araba, wato Tekun Gishiri, aka yanke shi ɗungum. Jama’a kuwa suka haye daura da Yariko.

17 A sa’ad da Isra’ilawa duka suna tafiya a kan sandararriyar ƙasa a cikin Urdun, firistoci kuwa waɗanda suke ɗauke da akwatin alkawari na Ubangiji suka yi ta tsayawa a bisa sandararriyar ƙasa a tsakiyar Urdun har al’ummar ta gama hayewa.