L. FIR 27

Ka’idodin Keɓewa

1 Ubangiji ya ba Musa

2 waɗannan ka’idodi domin Isra’ilawa. Idan an ba da mutum ga Ubangiji don cikar babban wa’adi za a iya fansarsa ta wurin biya waɗannan kuɗi.

3-7 Abin da aka ƙayyade za su biya bisa ga ma’aunin kuɗin da ake aiki da shi.

Maza masu shekara 20-60 Shekel hamsin
Mata masu shekara 20-60 Shekel talatin
Maza masu shekara 5-20 Shekel ashirin
Mata masu shekara 5-20 Shekel goma sha biyar
Maza masu wata guda zuwa shekara 5 Shekel biyar
Mata masu wata guda zuwa shekara 5 Shekel uku
Tsohon da ya fi shekara 60 Shekel goma sha biyar
Tsohuwar da ta fi shekara 60 Shekel goma

8 Idan mutumin ya cika talauci har ya kasa biyan tamanin da aka kimanta, sai ya kawo mutumin da aka yi wa’adi a kansa a gaban firist, firist ɗin zai kimanta tamaninsa daidai da ƙarfin wanda ya yi wa’adin.

9 Idan kuwa dabba ce irin wadda mutane kan miƙa hadaya ga Ubangiji, dukan irin wannan da mutum yakan bayar ga Ubangiji zai zama tsattsarka.

10 Ba zai musaya shi da wani abu ba, ba zai musaya mai kyau da marar kyau, ko marar kyau da mai kyau ba. Idan kuwa ya musaya dabba da dabba, sai duka biyu, abar da aka musaya, da wadda aka musayar, za su zama tsarkakakku.

11 Idan kuwa dabbar marar tsarki ce, irin wadda ba a miƙa ta hadaya ga Ubangiji, sai mutumin ya kai dabbar a wurin firist.

12 Firist ɗin zai kimanta tamanin dabbar daidai darajarta, kamar yadda firist ya kimanta, haka zai zama.

13 Amma idan mutumin yana so ya fansa, sai ya yi ƙarin humushin tamanin da aka kimanta.

14 Idan mutum ya keɓe gidansa ga Ubangiji, sai firist ya kimanta tamanin gidan daidai darajarsa, ko gidan mai tsada ne, ko mai araha ne. Yadda shi firist ya kimanta tamaninsa, haka zai zama.

15 Idan shi wanda ya keɓe gida nasa yana so ya fansa, sai ya ƙara kashi ɗaya daga cikin biyar na tamanin da aka kimanta, gidan kuwa zai zama nasa.

16 Idan mutum ya keɓe wa Ubangiji wani sashi daga cikin gonarsa ta gādo, sai ka kimanta tamanin gonar daidai da yawan irin da zai rafa. Gonar da za a yafa iri wajen garwa ashirin na sha’ir tamaninta zai zama wajen shekel hamsin.

17 Idan ya keɓe gonarsa daga shekara ta hamsin ta murna, ba za a rage kome daga cikin tamanin gonar da aka kimanta ba.

18 Amma idan ya keɓe ta bayan shekara ta hamsin ta murna, sai firist ya kimanta yawan kuɗin bisa ga yawan shekarun da suka ragu kafin shekara ta hamsin ta murna ta kewayo. Sai a rage kuɗin tamanin gonar.

19 Idan shi wanda ya keɓe gonar yana so ya fanshe ta, to, sai ya ƙara kashi ɗaya daga cikin biyar na tamanin kuɗin gonar, gonar kuwa za ta zama tasa.

20 Amma idan ba ya so ya fanshi gonar, ko kuwa ya riga ya sayar wa wani da gonar, faufau, ba zai sāke fansarta ba.

21 Sa’ad da aka mayar da gonar a shekara ta hamsin ta murna, za ta zama tsattsarka ta ubangiji kamar gonar da aka keɓe. Firist ne zai mallaka ta.

22 Idan kuwa ya keɓe wa Ubangiji gonar da ya saya, wadda ba ta gādo ba,

23 sai firist ya kimanta tamaninta har zuwa shekara ta hamsin ta murna. Shi mutumin zai ba da yawan abin da aka kimanta a ranar, abu mai tsarki ne ga Ubangiji.

24 A cikin shekara ta hamsin ta murna, sai a mayar da gonar ga wanda aka saye ta a hannunsa, wanda gonarsa ce ta gādo.

25 Sai a kimanta tamanin kowane abu bisa ga ma’aunin kuɗin da ake aiki da shi.

26 Kowane ɗan fari na dabba na Ubangiji ne, kada wani ya fanshi sa ko tunkiya, gama na Ubangiji ne.

27 Idan dabbar marar tsarki ce, sai mai ita ya kimanta tamanin kuɗinta, ya ƙara da humushin kuɗin, ya saya. Idan ba a fansa ba, sai a sayar bisa ga tamaninta.

28 Amma iyakar abin da mutum ya ba Ubangiji ɗungum daga cikin abubuwan da yake da su, ko mutum ko dabba, ko gonarsa ta gādo, ba za a sayar ko a fansar ba, gama kowane abu da aka keɓe mafi tsarki ne ga Ubangiji.

29 Ko da mutum ne aka ba Ubangiji ɗungum, ba za a fanshe shi ba, sai a kashe shi.

30 Dukan ushirin amfanin ƙasar, ko na hatsi ne, ko na ‘ya’yan itatuwa ne, na Ubangiji ne, gama tsattsarka ne ga Ubangiji.

31 Idan wani yana so ya fanshi ushiri na kowane iri, sai ya ƙara humushin tamanin ushirin.

32 Dukan ushiri na shanu, da na tumaki da awaki, duk dai dabbar da ta zama ta goma bisa ga ƙirgar makiyayan, keɓaɓɓiya ce, ta Ubangiji ce.

33 Ba ruwan kowa da kyanta ko rashin kyanta. Kada kuma a musaya ta. Idan kuwa an musaya ta, sai dai su zama tsarkakakku ga Ubangiji, ita da abar da aka yi musayar. Ba za a fanshe su ba.

34 Waɗannan su ne umarnan da Ubangiji ya ba Musa a kan Dutsen Sinai saboda isra’ilawa.