L. FIR 6

1 Ubangiji kuma ya ba Musa ka’idodin nan.

2 Idan wani mutum ya yi laifi na cin amana gāba da Ubangiji, wato, ya yaudari maƙwabcinsa a kan ajiya, ko jingina, ko ƙwace, ko ya zalunce shi,

3 ko ya yi tsintuwa, amma ya yi mūsu har ya rantse da ƙarya, duk dai irin abubuwan da akan aikata na laifi,

4 sa’ad da mutum ya yi laifi, ya kuwa tabbata mai laifi ne, sai ya mayar da abin da ya ƙwace, ko abin da ya samu ta hanyar zalunci, ko abin da aka ba shi ajiya, ko abin da ya tsinta,

5 ko kowane abin da ya rantse a kansa da ƙarya. Zai mayar wa mai abin da abinsa a yadda yake, har ya ƙara da humushin tamanin abin. A ranar da zai yi hadaya don laifinsa, a ranar ce zai mayar wa mai abin da abinsa.

6 Zai kuwa kai wa firist rago marar lahani daga garken tumaki don yin hadaya ga Ubangiji saboda laifinsa. Za a kimanta tamanin ragon daidai da tamanin hadaya don laifi.

7 Firist kuwa zai yi kafara dominsa a gaban Ubangiji, za a kuwa gafarta masa irin laifin da ya yi.

Hadayun da Za A Ƙone Ƙurmus

8 Ubangiji kuma ya umarci Musa,

9 ya ba Haruna da ‘ya’yansa maza ka’idodin hadayu na ƙonawa. Hadaya ta ƙonawa za ta kwana bisa bagaden, wutar bagaden kuma ta kwana tana ci har safe.

10 Firist zai sa rigarsa ta lilin, ya ɗaura mukurunsa na lilin, sa’an nan ya kwashe tokar hadaya ta ƙonawa daga bagaden, ya zuba a gefensa.

11 Firist ɗin kuma zai tuɓe rigunansa, ya sa waɗansu, sa’an nan ya kwashe tokar ya kai bayan zango ya zuba a wani wuri mai tsabta.

12 Sai a bar wutar bagaden ta yi ta ci, kada a kashe ta. Firist ɗin ya yi ta iza wutar kowace safiya, ya shimfiɗa hadaya ta ƙonawa a jere a bisa wutar, ya kuma ƙone kitsen hadaya ta salama a bisanta.

13 Sai wuta ta yi ta ci a bisa bagaden kullum, kada ta mutu.

Hadaya ta Gari

14 Wannan ita ce dokar hadaya ta gari. ‘Ya’yan Haruna, maza, za su miƙata a gaban Ubangiji daga gaban bagaden.

15 Ɗaya daga cikinsu zai ɗibi lallausan garin hadayar wanda aka zuba masa mai da lubban cike da tafin hannunsa. Zai ƙona wannan a bisa bagaden, hadaya ce mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji don tunawa.

16 Haruna da ‘ya’yansa maza za su ci ragowar garin. Za a ci shi ba tare da yisti ba a wuri mai tsarki na farfajiyar alfarwa ta sujada.

17 Ba za a sa masa yisti a toya shi ba. Wannan Ubangiji ne ya ba su ya zama rabonsu daga cikin hadayun da ake ƙonawa da wuta, abu ne mafi tsarki, kamar hadaya don zunubi da laifi.

18 Kowane ɗa namiji cikin ‘ya’yan Haruna zai iya ci daga cikin hadayun Ubangiji waɗanda akan yi da wuta. Wannan madawwamiyar doka ce cikin zamananku duka. Duk wanda ya taɓa hadayu zai tsarkaka.

19 Sai Ubangiji ya ba Musa waɗannan ka’idodi,

20 domin keɓe firist, wato, zuriyar Haruna. A ranar da za a keɓe shi zai kawo humushin garwar gari mai laushi (kamar yadda akan kawo na hadaya ta gari), za a miƙa rabinsa da safe, rabin kuma da maraice.

21 Za a shirya shi da mai a kwanon tuya. A kwaɓa shi sosai, a toya shi dunƙule dunƙule kamar hadaya ta gari, sa’an nan a kawo shi a miƙa shi don ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji.

22 Wanda aka keɓe daga zuriyar Haruna, shi ne zai miƙa wannan hadaya ga Ubangiji. Za a ƙone ta duka. Wannan farilla ce har abada.

23 Kowace hadaya ta gari ta firist, za a ƙone ta ɗungum, ba za a ci ba.

Hadayu domin Zunubi

24 Sai Ubangiji ya umarci Musa

25 ya ba Haruna da ‘ya’yansa maza waɗannan ka’idodi domin hadaya don zunubi. A inda ake yanka hadaya ta ƙonawa, a nan ne za a yanka hadaya don zunubi a gaban Ubangiji, hadaya ce mai tsarki.

26 Firist wanda ya miƙa hadaya don zunubi zai ci daga ciki a wuri mai tsarki a cikin farfajiyar alfarwa ta sujada.

27 Duk wanda ya taɓa naman zai tsarkaka, in kuma jinin ya ɗiga a riga, sai a wanke rigar a wuri mai tsarki.

28 Sai a fasa tukunyar ƙasa wadda aka dafa naman a ciki, amma in a cikin tukunyar tagulla aka dafa, sai a kankare ta a ɗauraye da ruwa.

29 Kowane namiji a cikin firistoci zai iya cin naman, gama abu ne mafi tsarki.

30 Amma ba za a ci naman hadaya don zunubi ba wanda aka shigar da jininsa a alfarwa ta sujada domin yin kafara a Wuri Mai Tsarki. Sai a ƙone shi da wuta.