L. FIR 7

Hadaya domin Laifi

1 Waɗannan su ne ka’idodin hadaya don ramuwa, hadaya ce tsattsarka.

2 Za a yanka dabbar hadayar a arewa da bagaden inda akan yanka hadaya don ƙonawa. Sai a yayyafa jinin a kan bagaden da kewayensa.

3 Za a miƙa kitsen abin hadaya duka, da wutsiya mai kitse, da kitsen da yake rufe da kayan ciki,

4 da ƙodoji biyu da kitsen da yake bisansu wajen kwiɓi, da matsarmama wadda za a cire tare da ƙodojin.

5 Firist zai ƙone su a bisa bagaden, gama hadaya ce da akan ƙone da wuta ga Ubangiji, hadaya ce don laifi.

6 Kowane namiji a cikin firistoci zai iya ci. Sai a wuri mai tsarki za a ci, gama tsattsarkan abu ne.

7 Hadaya don laifi kamar hadaya don zunubi take, saboda haka ka’idar yinsu iri ɗaya ce. Firist wanda ya yi kafarar, zai ɗauki abin da ya ragu.

8 Firist kuma wanda ya miƙa hadaya ta ƙonawa ta wani mutum, zai ɗauki fatar abin da aka yi hadayar da shi.

9 Kowace hadaya ta gari da aka toya cikin tanda, da duk wadda aka yi a tukunya ko a kaskon tuya, za su zama na firist wanda ya miƙa hadaya.

10 Kowace hadaya ta gari kuma wadda aka kwaɓa da mai, ko wadda ba a kwaɓa ba, za ta zama rabon ‘ya’yan Haruna, maza duka, kowa da kowa.

Hadaya domin Zumunci

11 Waɗannan su ne ka’idodin hadaya ta salama wadda za a miƙa wa Ubangiji.

12 Idan domin godiya mutum ya miƙa hadaya, sai ya miƙa ta tare da abinci marar yisti, wadda aka kwaɓa da mai, da wadda aka shafa wa mai, da kuma ƙosai.

13 Tare da hadayarsa ta salama don godiya, sai ya kawo dunƙulen abincin da aka sa masa yisti.

14 Daga cikin wannan zai miƙa waina ɗaya daga kowace hadaya don hadaya ta ɗagawa ga Ubangiji. Wannan zai zama na firist wanda ya yayyafa jinin hadaya ta salama.

15 Za a ci naman hadayarsa ta salama da aka miƙa don godiya a ranar da aka miƙa ta. Kada a bar naman ya kai safe.

16 Amma idan hadayarsa ta cika wa’adi ce, ko ta yardar rai ce, sai a ci ta a ranar da aka miƙa ta, kashegari kuma a ci abin da ya ragu.

17 Amma idan ba a cinye naman hadayar ba har ya kai kwana uku, kada a ci, sai a ƙone shi da wuta.

18 Idan aka ci naman hadayarsa ta salama a rana ta uku, ba za a karɓi wanda ya ba da hadayar har ya sami fa’idar hadayar ba, naman zai zama abin ƙyama, duk wanda ya ci ya yi laifi.

19 Kada a ci naman da ya taɓa wani abu marar tsarki, sai a ƙone shi da wuta.

Duk wanda yake da tsarki zai iya cin nama.

20 Amma wanda ya ci naman hadaya ta salama ga Ubangiji lokacin da ba shi da tsarki, za a raba shi da mutenensa.

21 Idan wani mutum ya taɓa abu marar tsarki, ko mutum ne, ko dabba ce, ko wani abu na banƙyama, ya kuma ci naman hadaya ta salama ga Ubangiji, za a raba wannan mutum da mutanensa.

22 Ubangiji kuma ya ce wa Musa,

23 ya faɗa wa mutanen Isra’ila cewa, kada su ci kitsen sa, ko na tunkiya, ko na akuya.

24 Kitsen dabbar da ta mutu mushe, da kitsen dabbar da namomin jeji suka yayyaga, za a iya yin wani amfani da shi, amma kada a kuskura a ci.

25 Duk mutumin da ya ci kitsen dabbar da aka miƙa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji, za a raba shi da mutanensa.

26 Ko kaɗan, ba za a yi abinci da jini ba, ko na tsuntsu, ko na dabba, a inda suke duka.

27 Duk mutumin da ya karya wannan doka za a raba shi da mutanensa.

28 Ubangiji kuma ya ba Musa waɗannan ka’idodi

29 don mutanen Isra’ila, cewa, wanda zai miƙa hadayarsa ta salama ga Ubangiji, sai ya kawo hadayarsa ga Ubangiji daga cikin hadayu na salama.

30 Sai shi kansa ya kawo hadayar da za a ƙona. Zai kawo kitsen da ƙirjin. Za a yi hadaya ta kaɗawa da ƙirjin a gaban Ubangiji.

31 Firist zai ƙone kitsen a bisa bagaden, amma ƙirjin zai zama rabon Haruna da ‘ya’yansa maza.

32 Za a ba firist cinya ta dama, don hadaya ta ɗagawa daga cikin hadayu na salama.

33 Cinyar ƙafar dama za ta zama rabon ɗan Haruna wanda ya miƙa jinin da kitsen hadaya ta salama.

34 Gama Ubangiji ya ba Haruna da ‘ya’yansa maza, ƙirjin da aka kaɗa da cinyar da aka ɗaga, su zama rabonsu daga cikin hadayu na salama na Isra’ilawa. Ya ba Haruna, firist, da ‘ya’yansa maza, su zama rabonsu har abada daga cikin hadayu na Isra’ilawa.

35 Wannan shi ne rabon da aka keɓe wa Haruna da ‘ya’yansa maza, daga cikin hadayun da ake yi da wuta ga Ubangiji, tun a ranar da aka keɓe su firistoci na Ubangiji.

36 Ubangiji ya umarci Isra’ilawa su ba firistoci wannan a ranar da aka keɓe su. Wannan hakkinsu ne a dukan zamanansu.

37 Waɗannan su ne ka’idodin hadaya ta ƙonawa, da hadaya ta gari, da hadaya don zunubi, da hadaya don laifi, da hadaya don keɓewa, da hadaya ta salama.

38 Waɗannan su ne umarnan da Ubangiji ya ba Musa a Dutsen Sina’i, can cikin hamada, a ranar da ya faɗa wa Isra’ilawa su kawo hadayunsu gare shi.