L. FIR 8

Keɓewar Haruna da ‘Ya’yansa Maza

1 Ubangiji ya ce wa Musa,

2 “Ɗauki Haruna da ‘ya’yansa maza, da rigunan, da man keɓewa, da bijimi na yin hadaya don zunubi, da raguna biyu, da kwandon abinci marar yisti.

3 Ka kuma tattara jama’a duka a ƙofar alfarwa ta sujada.”

4 Musa kuwa ya yi yadda Ubangiji ya umarce shi. Jama’ar kuwa suka tattaru a ƙofar alfarwa ta sujada.

5 Musa ya faɗa wa taron jama’ar cewa “Wannan shi ne abin da Ubangiji ya umarta a yi.”

6 Sai Musa ya fito da Haruna da ‘ya’yansa maza, ya yi musu wanka.

7 Ya sa wa Haruna zilaika, ya ɗaura masa ɗamara, ya sa masa taguwa, ya kuma sa masa falmaran, ya ɗaura masa ɗamarar falmaran wadda aka yi mata saƙar gwaninta.

8 Ya maƙala masa ƙyallen maƙalawa a ƙirji, sa’an nan ya sa Urim da Tummin, a kan ƙyallen.

9 Sai ya naɗa masa rawani, daga gaban rawanin ya sa allon zinariya, wato, kambi tsattsarka, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.

10 Sai Musa ya ɗauki man keɓewa ya shafa wa alfarwa ta sujada da dukan abin da yake cikinta, da haka ya tsarkake su.

11 Ya yayyafa wa bagaden mai sau bakwai, ya kuma shafa wa bagaden da dukan kayayyakinsa, da daron da gammonsa, don ya tsarkake su.

12 Ya zuba man keɓewa a kan Haruna, ya keɓe shi.

13 Sai Musa kuma ya kawo ‘ya’yan Haruna, maza, ya sa musu zilaiku, ya ɗaura musu ɗamaru, ya sa musu huluna kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.

14 Sa’an nan ya kawo bijimi na yin hadaya don zunubi, Haruna da ‘ya’yansa maza, suka ɗibiya hannuwansu a kan kan bijimin.

15 Sai Musa ya yanka shi, ya ɗibi jinin a yatsansa ya shafa wa zankayen bagaden a kewaye, ya tsarkake bagaden, ya zuba jinin a gindin bagaden, ya keɓe shi don ya yi kafara dominsa.

16 Sai ya ɗauki dukan kitsen da yake bisa kayan ciki da matsarmama, da ƙodoji biyu da kitsensu, ya ƙone su bisa bagaden.

17 Amma ya ƙone naman bijimin da fatarsa da tarosonsa a bayan zangon kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.

18 Sa’an nan ya kawo rago na yin hadaya ta ƙonawa. Haruna da ‘ya’yansa maza suka ɗibiya hannuwansu a kan kan ragon.

19 Sai ya yanka ragon, ya yayyafa jinin a bisa bagaden da kewayensa.

20 Da aka yanyanka ragon gunduwa gunduwa, sai Musa ya ƙone kan, da gunduwoyin, da kitsen.

21 Sa’ad da kuma aka wanke kayan ciki da ƙafafu da ruwa, sai ya ƙone ragon duka a bisa bagaden, hadaya ce ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.

22 Musa ya kawo ɗayan ragon keɓewa, sai Haruna da ‘ya’yansa maza suka ɗibiya hannuwansu a kan kan ragon.

23 Musa kuwa ya yanka shi, ya ɗibi jinin, ya sa a leɓatun kunnen dama na Haruna, da bisa babban yatsansa na hannun dama, da babban yatsa na ƙafar dama.

24 Sai aka kawo ‘ya’yan Haruna, maza, Musa kuma ya sa jinin a leɓatun kunnensu na dama, da manyan yatsotsi na hannuwansu na dama, da manyan yatsotsin ƙafafu na dama. Sa’an nan ya yayyafa jinin kewaye da bagaden.

25 Ya kuma ɗauki kitsen, da wutsiya mai kitse, da dukan kitsen da yake bisa kayan ciki, da matsarmama da ƙodoji biyu da kitsensu, da cinyar dama.

26 Daga cikin kwandon abinci marar yistin da yake a gaban Ubangiji, ya ɗauki waina guda marar yisti, da waina guda da aka yi da mai, da ƙosai guda. Sai ya ɗibiya su a bisa kitsen da cinyar dama.

27 Ya sa waɗannan abubuwa duka a tafin hannuwan Haruna da na ‘ya’yansa maza, ya miƙa abubuwan nan domin hadayar kaɗawa ga Ubangiji.

28 Sa’an nan ya karɓe su daga tafin hannuwansu, ya ƙone su tare da hadaya ta ƙonawa a bisa bagaden don hadayar keɓewa, hadaya ce da aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.

29 Ya kuma ɗauki ƙirjin, ya kaɗa shi don hadayar kaɗawa ga Ubangiji. Wannan shi ne rabon Musa daga cikin ragon keɓewar, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.

30 Sa’an nan Musa ya ɗiba daga cikin man keɓewa da jinin da yake bisa bagaden, ya yayyafa wa Haruna da rigunansa, da ‘ya’yansa maza da rigunansu. Da haka ya tsarkake Haruna da rigunansa, da ‘ya’yansa maza da rigunansu.

31 Sai Musa ya ce wa Haruna da ‘ya’yansa maza, “Ku dafa naman a ƙofar alfarwa ta sujada, ku ci shi a wurin, da abincin da yake a cikin kwandon hadayar keɓewa, kamar yadda Ubangiji ya umarta, cewa, Haruna da ‘ya’yansa maza za su ci shi.

32 Sauran abin da ya ragu daga naman da abincin, sai ku ƙone su.

33 Ba za ku fita daga cikin alfarwa ta sujada ba har kwana bakwai, wato, sai kwanakin keɓewarku sun cika, gama keɓewarku za ta ɗauki kwana bakwai.

34 Abin da aka yi a wannan rana haka Ubangiji ya umarta a yi domin kafararku.

35 A ƙofar alfarwa ta sujada za ku zauna dare da rana har kwana bakwai, kuna kiyaye umarnin Ubangiji don kada ku mutu, gama haka Ubangiji ya umarta.”

36 Sai Haruna da ‘ya’yansa maza suka yi dukan abin da Ubangiji ya umarta ta wurin Musa.