Yaƙi da Mutanen Biliyaminu
1 Dukan jama’ar Isra’ila fa suka fito tun daga Dan a arewa har zuwa Biyer-sheba a kudu da kuma Gileyad daga gabas. Suka hallara gaba ɗaya a gaban Ubangiji a Mizfa.
2 Dukan shugabannin kabilar Isra’ila suna cikin wannan taron jama’ar Allah. Sojojin ƙafa yawansu ya kai dubu ɗari huɗu (400,000).
3 Mutanen Biliyaminu kuwa sun ji labari sauran Isra’ilawa sun haura zuwa Mizfa. Isra’ilawa suka tambayi Balawen suka ce, “Ka faɗa mana yadda wannan mugun abu ya auku.”
4 Balawe, mai ƙwarƙwarar da ka kashe, ya amsa ya ce, “Ni da ƙwarƙwarata muna biyo Gibeya ta Biliyaminu mu kwana.
5 Sai mutanen Gibeya suka kewaye gidan da nake da dare, suna neman kashe ni, da ba su same ni ba, sai suka yi wa ƙwarƙwarata faɗe har ya kai ta ga mutuwa.
6 Ni kuwa na ɗauki gawarta na yanyanka gunduwa gunduwa na aika cikin ƙasar gādon Isra’ila duka, gama waɗannan mutane sun aikata abin ƙyama da abin kunya ga dukan Isra’ila.
7 Dukanku nan Isra’ilawa ne, me za mu yi a kan wannan al’amari?”
8 Dukan jama’a kuwa suka tashi gaba ɗaya, suna cewa, “Daga cikinmu ba wanda zai koma alfarwarsa ko kuwa gidansa.
9 Wannan shi ne abin da za mu yi wa Gibeya, mu zaɓi waɗansunmu su fāɗa mata da yaƙi.
10 Kashi ɗaya daga goma na Isra’ilawa su ba da abinci ga sojoji. Sauran jama’a kuwa su je su hukunta Gibeya saboda muguntar da ta aikata cikin Isra’ila.”
11 Saboda haka dukan mutanen Isra’ila suka taru niyya ɗaya domin su fāɗa wa garin da yaƙi.
12 Kabilar Isra’ila kuwa suka aiki manzanni ga kabilar Biliyaminu suka ce, “Wace irin mugunta ce wannan da kuka aikata?
13 Yanzu sai ku ba da mutanen nan ‘yan iska da take cikin Gibeya don mu kashe su, mu kawar da mugunta daga cikin Isra’ila.” Amma mutanen Biliyaminu ba su kula da maganar ‘yan’uwansu, Isra’ilawa ba.
14 Mutanen Biliyaminu kuwa suka fita daga Gibeya gaba ɗaya domin su yi yaƙi da jama’ar Isra’ila.
15 A ran nan mutanen Biliyaminu suka tattaru daga garuruwansu, mutum dubu ashirin da shida (26,000). Banda waɗannan, sai da mazaunan Gibeya suka tara zaɓaɓɓun mutane ɗari bakwai.
16 Daga cikin waɗannan duka akwai zaɓaɓɓun mutane bakwai, bahagwai. Kowannensu yana iya ya baraci gashi guda da majajjawa ba kuskure.
17 Isra’ilawa kuwa banda kabilar Biliyaminu, suka tara mayaƙa dubu ɗari huɗu (400,000) horarru.
Yaƙi da Mutanen Biliyaminu
18 Isra’ilawa suka tashi suka tafi Betel. A can suka yi tambaya ga Allah suka ce, “Wace kabila ce daga cikinmu za ta fara faɗa wa kabilar Biliyaminu?”
Ubangiji ya ce, “Kabilar Yahuza ce za ta fara.”
19 Sa’an nan Isra’ilawa suka tashi da safe suka kafa sansani kusa da Gibeya.
20 Suka kuwa fita su yi yaƙi da mutanen Biliyaminu, suka jā dāgar yaƙi suna fuskantar Gibeya.
21 Mutanen Biliyaminu kuwa suka fito daga birnin suka hallakar da mutum dubu ashirin da biyu (22,000), daga cikin mutanen Isra’ila a ranar.
22-23 Mutanen Isra’ila suka tafi inda ake sujada suka yi makoki a gaban Ubangiji har zuwa dare. Suka tambaye shi suka ce, “Mu sāke zuwa domin mu yi yaƙi da ‘yan’uwanmu mutanen Biliyaminu?”
Ubangiji ya ce musu, “I, ku tafi.”
Saboda haka sai sojojin Isra’ilawa suka ƙarfafa, suka sāke jān dāga a inda suka jā ta dā.
24 Sai mutanen Isra’ila suka tafi su kara da mutanen Biliyaminu a rana ta biyu.
25 Mutanen Biliyaminu kuwa suka fito daga birnin suka hallakar da mutum dubu goma sha takwas (18,000) daga cikin Isra’ilawa. Dukan waɗannan da aka hallaka horarru ne.
26 Dukan rundunan Isra’ilawa suka haura zuwa Betel, suka yi makoki, suka zauna a gaban Ubangiji suka yi azumi har maraice. Sa’an nan suka miƙa wa Ubangiji hadayu na ƙonawa da na salama.
27-28 Suka sāke yin tambaya ga Ubangiji suka ce, “Mu sāke tafiya mu yi yaƙi da ‘yan’uwanmu, mutanen Biliyaminu, ko kuwa mu bari?”
Ubangiji kuwa ya ce musu, “Ku je, gama gobe zan ba da su gare ku.” A lokacin nan akwatin alkawari na Ubangiji yana nan. Finehas ɗan Ele’azara, ɗan Haruna, shi ne mai aiki a gabansa.
29 Isra’ilawa kuwa suka sa ‘yan kwanto kewaye da Gibeya.
30 Sa’an nan suka tafi su kara da mutanen Biliyaminu a rana ta uku. Suka jā dāgar yaƙi gaba da Gibeya kamar dā.
31 Mutanen Biliyaminu kuma suka fito, suka tasar musu. Aka jawo su nesa da birnin. Suka fara kashe Isra’ilawa kamar yadda suka yi a dā, suka kashe wajen mutum talatin a kan karauka wadda ta nufi Betel da wadda ta nufi Gibeya, da filaye.
32 Sai mutanen Biliyaminu suka ce, “Mun fatattake su kamar dā.”
Amma Isra’ilawa suka ce, “Mu gudu don mu jawo su nesa da birnin zuwa karauka.”
33 Isra’ilawa duka suka tashi daga wurin da suke, suka jā dāga a Ba’altamar. Mutanensu da suke kwanto a yammacin Gibeya suka fito.
34 Horarrun sojojin Isra’ila, su dubu goma (10,000), suka faɗa wa Gibeya. Yaƙi kuwa ya yi zafi, amma mutanen Biliyaminu ba su san masifa tana gab da su ba.
35 Ubangiji kuwa ya fatattake mutanen Biliyaminu a gaban Isra’ilawa. Isra’ilawa kuwa suka hallaka mutanen Biliyaminu dubu ashirin da biyar da ɗari ɗaya (25,100) a wannan rana, waɗannan duka kuwa mayaƙa ne.
36 Mutanen Biliyaminu kuwa suka gane an ci su da yaƙi.
Mutanen Isra’ila kuwa suka yi ta ja da baya daga mutanen Biliyaminu domin sun dogara ga mutanensu da suka yi wa Gibeya kwanto.
37 Sai ‘yan kwanto suka gaggauta suka faɗa wa Gibeya, suka kutsa suka kashe dukan waɗanda suke a birnin.
38 Alamar da mayaƙan Isra’ila da na ‘yan kwantonsu suka daidaita a tsakaninsu, ita ce murtukewar hayaƙi a cikin birnin.
39 Idan mutanen Isra’ila sun hangi hayaƙin, sai su juya su fāɗa wa mutanen Biliyaminu da yaƙi. Kafin alamar hayaƙin sai mutanen Biliyaminu suka fara kashe wa Isra’ilawa wajen mutum talatin. Suka ce, “Ai, suna shan ɗibga a hannunmu kamar yadda suka sha da fari.”
40 Amma sa’ad da alamar hayaƙin ta fara murtukewa a cikin birnin, sai mutanen Biliyaminu suka juya, suka duba, suka ga hayaƙi ya murtuke cikin birnin, ya yi sama.
41 Da mutanen Isra’ila suka juyo kansu, sai mutanen Biliyaminu suka tsorata, gama sun ga masifa ta auko musu.
42 Don haka suka juya suka kama gudu suka nufi hamada, amma ba su tsira ba. Aka datse su tsakanin ‘yan kwanto da sauran sojojin Isra’ilawa.
43 Suka yi wa mutanen Biliyaminu tarko, suka runtume su ba tsayawa tun daga Menuha har zuwa daura da Gibeya daga gabas.
44 Aka kashe jarumawan mutanen Biliyaminu mutum dubu goma sha takwas (18,000).
45 Sauran suka juya, suka gudu, suka nufi wajen hamada zuwa Dutsen Rimmon. A kan hanyoyi, aka kashe musu mutum dubu biyar. Aka kuma runtumi sauran da suka ragu har zuwa Gidom inda suka kashe mutum dubu biyu.
46 Mutanen Biliyaminu da aka kashe a ran nan dubu ashirin da biyar (25,000) ne. Dukansu kuwa jarumawa ne.
47 Amma mutum ɗari shida suka juya, suka gudu suka nufi hamada zuwa Dutsen Rimmon inda suka zauna har wata hu:du.
48 Mutanen Isra’ila kuma suka komo, suka fāɗa wa sauran mutanen Biliyaminu. Suka karkashe su, mutane, da dabbobi, da dukan abin da suka iske. Suka ƙone garuruwan wannan yankin ƙasa.