L. MAH 21

Mata domin Mutanen Biliyaminu

1 Mutanen Isra’ila kuwa suka yi wa Ubangiji ƙaƙƙarfan alkawari a Mizfa cewa, “Ba wani daga cikinmu da zai ba da ‘yarsa aure ga mutumin Biliyaminu.”

2 Sai mutanen Isra’ila suka zo Betel, suka zauna a nan a gaban Allah har maraice. Suka yi makoki mai zafi.

3 Suka ce, “Ya Ubangiji Allah na Isra’ila, me ya sa wannan abu ya faru a cikin Isra’ila, har da za a rasa kabila guda ta Isra’ila?”

4 Kashegari mutanen suka tashi da safe, suka gina bagade a can. Suka miƙa hadayun ƙonawa da na salama.

5 Suka kuma ce, “Daga cikin kabilar Isra’ila, wace ce ba ta halarci wannan taro na gaban Ubangiji ba?” Gama sun riga sun yi ƙaƙƙarfan alkawari cewa, “Duk wanda bai hauro zuwa wurin Ubangiji a Mizfa ba, za a kashe shi.”

6 Jama’ar Isra’ila kuwa suka yi juyayin ‘yan’uwansu, mutanen Biliyaminu, suka ce, “Yau an hallaka kabila guda daga cikin Isra’ila.

7 Ƙaƙa za mu yi don mutanen da suka ragu su sami mata. Ga shi, mum riga mu rantse da Ubangiji ba za mu ba su ‘ya’yanmu mata su aura ba?”

8 Sa’an nan suka ce, “Wace kabila ce daga cikin kabilar Isra’ila ba ta hauro zuwa wurin Ubangiji a Mizfa ba?.. Sai suka ga, ashe, ba wani daga Yabesh-gileyad da ya halarci taron.

9 Gama sa’ad da aka tattara mutanen, aka ga ba wani daga cikin mazaunan Yabesh-gileyad a wurin.

10 Taron jama’a kuma suka aiki jarumawansu mutum dubu goma sha biyu (12,000) zuwa Yabesh-gileyad. Suka umarce su cewa, “Ku je ku karkashe mazaunan Yabesh duka har da mata da yara.

11 Abin da za ku yi ke nan, ku je ku kashe dukan maza, da kowace mace wadda ba budurwa ba ce.”

12 Suka sami budurwai ɗari huɗu daga mutanen Yabesh-gileyad, sai suka kawo su zango a Shilo, wadda take a ƙasar Kan’ana.

13 Sa’an nan taron jama’a suka aika wa mutanen Biliyaminu da suke a Dutsen Rimmon, cewa, yaƙi ya ƙare, sai salama.

14 Mutanen Biliyaminu kuwa suka komo, aka ba su budurwan nan da aka bar su da rai aka kawo su Yabesh-gileyad, amma budurwan ba su ishe su ba.

15 Sai mutanen suka yi juyayin mutanen Biliyaminu domin Ubangiji ya naƙasa kabila daga kabilar Isra’ila.

16 Saboda haka dattawan taron jama’a suka ce, “Ƙaƙa za mu yi da waɗanda suka ragu da ba su sami mata ba, da yake an hallaka matan kabilar Biliyaminu?”

17 Sai suka ce, “Tilas, waɗanda suka ragu daga mutanen Biliyaminu su sami gādo domin kada a shafe kabila daga cikin Isra’ila,

18 amma fa ba za mu iya aurar musu da ‘ya’yanmu mata ba.” Sun faɗi haka ne kuwa, domin sun riga sun rantse cewa, “Duk wanda ya aurar da ‘yarsa ga mutumin Biliyaminu la’ananne ne.”

19 Suka kuma ce, “Ga shi, idin Ubangiji na shekara shekara a Shilo ya kusa.” (Shilo tana arewacin Betel, kudu da Lebona, gabas da hanyar da take tsakanin Betel da Shekem.)

20 Suka umarci mutanen Biliyaminu suka ce, “Ku tafi ku yi kwanto a gonakin inabi,

21 ku lura, idan ‘yan matan Shilo sun fito domin su yi rawa, sai ku fito daga cikin gonakin inabi, kowa ya kama daga cikin ‘yan matan da ƙarfi, ya sami mata ke nan, ya tafi da ita a ƙasar Biliyaminu.

22 Sa’ad da iyayensu ko ‘yan’uwansu sun kawo ƙara gare mu, za mu ce musu, ‘Ku bar mana su, muna roƙonku, domin ba daga wurin yaƙi muka kamo su domin su zama matanmu ba. Amma tun da ba ku ba mu su ba, ba ku da laifin ta da alkawari.’ ”

23 Haka kuwa mutanen Biliyaminu suka yi. Suka kama budurwai gwargwadon yawansu daga cikin masu rawa. Sa’an nan suka koma zuwa yaƙin ƙasarsu ta gādo. Suka sāke gina garuruwansu, suka zauna.

24 Haka nan kuma sauran mutanen Isra’ila suka tashi daga can. Kowa ya tafi wurin kabilarsa, da iyalinsa, da abin da ya mallaka.

25 A lokacin ba sarki a Isra’ila, sai kowa ya yi ta yin abin da ya ga dama.