A Wuri Ɗaya Kaɗai za a Yi Sujada
1 “Waɗannan su ne dokoki da farillai da za ku lura ku aikata a ƙasar da Ubangiji Allah na kakanninku ya ba ku, ku mallaka dukan kwanakinku a duniya.
2 Sai ku hallaka dukan wuraren da al’umman da za ku kora sukan bauta wa gumakansu, a bisa duwatsu masu tsawo, da bisa tuddai, da ƙarƙashin kowane itace mai duhu.
3 Sai ku rurrushe bagadansu, ku ragargaje al’amudansu, ku ƙone ginshiƙansu na tsafi, ku kuma sassare siffofin gumakansu, ku shafe sunayensu daga wuraren nan.
4 “Ba haka za ku yi wa Ubangiji Allahnku ba.
5 Amma sai ku nemi wurin da Ubangiji Allahnku zai zaɓa daga cikin kabilanku duka, inda zai sa sunansa, ya mai da shi wurin zamansa.
6 A can ne za ku tafi, a can ne kuma za ku kai hadayunku na ƙonawa, da sadakokinku, da zakarku, da hadayunku na ɗagawa, da hadayunku na wa’adi, da hadayunku na yardar rai, da ‘ya’yan farin garkenku na shanu, da na tumaki, da na awaki.
7 A nan, wato a gaban Ubangiji Allahnku, za ku ci, ku yi murna, ku da iyalanku, a kan dukan abin da Ubangiji Allahnku ya sa muku albarka da shi.
8 “Kada ku yi kamar yadda muke yi a nan yau, yadda kowa yake yin abin da ya ga dama.
9 Gama ba ku kai wurin hutawa wanda Ubangiji Allahnku zai ba ku gādo ba tukuna.
10 Amma sa’ad da kuka haye Urdun, kuka zauna a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku ita gādo, sa’ad da kuma ya ba ku hutawa daga maƙiyanku waɗanda suke kewaye da ku, kuka sami zaman lafiya,
11 sai ku kai dukan abin da na umarce ku ku kai, wato hadayu na ƙonawa, da sadakokinku, da zakarku, da hadayunku na ɗagawa, da hadayunku na wa’adi da kuka yi wa Ubangiji a wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa ya sa sunansa.
12 Ku yi murna a gaban Ubangiji Allahnku, ku da ‘ya’yanku mata da maza, da barorinku mata da maza tare da Lawiyawa waɗanda suke zaune cikinku tun da yake ba su da rabo ko gādo tare da ku.
13 Ku lura, kada ku miƙa hadayunku na ƙonawa ko’ina,
14 amma sai a wurin nan ɗaya wanda Ubangiji zai zaɓa daga cikin kabilanku, nan za ku miƙa hadayunku na ƙonawa, nan ne kuma za ku yi dukan abin da na umarce ku.
15 “Amma kwā iya yanka nama ku ci a garuruwanku duk lokacin da ranku yake so, bisa ga albarkar da Ubangiji yake sa muku. Mai tsarki da marar sarki za su ci abin da aka yanka kamar barewa da mariri.
16 Amma ba za ku ci jinin ba, sai ku zubar da shi a ƙasa kamar ruwa.
17 Kada ku ci waɗannan a garuruwanku, zakar hatsinku, ko ta inabinku, ko ta manku, ko ta ‘ya’yan fari na shanunku da tumakinku, ko hadayunku na wa’adi, da hadayunku na yardar rai, ko hadayarku ta ɗagawa.
18 Amma sai ku ci su a inda Ubangiji Allahnku zai zaɓa, ku da ‘ya’yanku mata da maza, da barorinku mata da maza, da Lawiyawa da suke a cikin garuruwanku. Sai ku yi murna a gaban Ubangiji Allah saboda duk abin da kuke yi.
19 Ku lura, kada ku manta da Lawiyawa muddin kuna zaune a ƙasarku.
20 “Sa’ad da Ubangiji Allahnku ya fāɗaɗa ƙasarku kamar yadda ya alkawarta muku, sa’an nan ku ce, ‘Ina so in ci nama,’ saboda kuna jin ƙawar nama, to, kuna iya cin nama yadda kuke so.
21 Idan wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa don ya sa sunansa ya yi muku nisa ƙwarai, to, sai ku yanka daga cikin garken shanunku, ko daga tumaki da awaki, waɗanda Ubangiji ya ba ku, kamar yadda na umarce ku. Za ku iya ci yadda kuke bukata a garuruwanku.
22 Kamar yadda akan ci barewa ko mariri haka za ku ci. Marar tsarki da mai tsarki za su iya cin naman.
23 Sai dai ku lura, kada ku ci jinin, gama jinin shi ne rai, kada ku ci ran tare da naman.
24 Kada ku ci jinin, sai ku zubar a ƙasa kamar ruwa.
25 Kada ku ci shi domin ku sami zaman lafiya, ku da zuriyarku a bayanku, gama za ku riƙa aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji.
26 Amma tsarkakakkun abubuwan da suke wajibanku da hadayunku na wa’adi, su ne za ku ɗauka ku kai wurin da Ubangiji ya zaɓa.
27 Sai ku miƙa nama da jinin hadayunku na ƙonawa a bisa bagaden Ubangiji Allahnku. Za ku zuba jinin sadakokinku a bisa bagaden Ubangiji Allahnku, amma za ku ci naman.
28 Ku lura, ku kasa kunne ga dukan umarnan da nake umartarku da su, don ku sami zaman lafiya, ku da zuriyarku a bayanku har abada, idan kun aikata abin da yake da kyau, daidai ne kuma a gaban Ubangiji Allahnku.”
Faɗakarwa a kan Gumaka
29 “Sa’ad da Ubangiji Allahnku ya kawar muku da al’umman nan waɗanda za ku shiga ƙasarsu don ku kore su, sa’ad da kuka kore su, kun zauna a ƙasarsu,
30 to, sai ku lura, kada ku jarabtu ku kwaikwaye su bayan da an riga an shafe su daga gabanku! Kada ku tambayi labarin kome na gumakansu, ku ce, ‘Ƙaƙa waɗannan al’ummai suka bauta wa gumakansu? Mu ma za mu yi kamar yadda suka yi.’
31 Kada ku yi wa Ubangiji Allahnku haka, gama sun yi wa gumakansu dukan abar ƙyamar da Ubangiji yake ƙi, har sun ƙona wa gumakansu ‘ya’yansu mata da maza.
32 “Ku lura, ku aikata dukan abin da na umarce ku da shi, kada ku ƙara, kada ku rage daga cikinsa.