M. SH 11

Girman Ubangiji

1 “Sai ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, ku kiyaye faɗarsa, da dokokinsa da farillansa, da umarnansa kullum.

2 Yau fa ku sani ba da ‘ya’yanku nake magana ba, waɗanda ba su sani ba, ba su kuma ga hukuncin Ubangiji Allahnku ba, da girmansa, da ƙarfin ikon dantsensa,

3 da alamunsa, da ayyukan da ya yi a kan Fir’auna Sarkin Masar, da dukan ƙasar,

4 da irin abin da ya yi wa sojojin Masar, da dawakansu, da karusansu, da yadda ya sa ruwan Bahar Maliya ya haɗiye su, a sa’ad da suke bin sawunku, da yadda Ubangiji ya hallaka su ƙaƙaf,

5 da abin da ya yi muku a jeji kafin ku iso wannan wuri,

6 da abin da ya yi wa Datan, da Abiram, ‘ya’yan Eliyab, ɗan Ra’ubainu, yadda ƙasa ta buɗe a tsakiyar Isra’ilawa ta haɗiye su da dukan ‘ya’yansu, da alfarwansu, da dukan abu mai rai wanda yake tare da su.

7 Amma idanunku sun ga manyan ayyukan nan da Ubangiji ya aikata.”

Albarkun Ƙasar Alkawari

8 “Don haka fa, sai ku kiyaye dukan umarnan da na umarce ku da su yau domin ku sami ƙarfin da za ku haye, ku shiga, ku ci ƙasar da za ku mallaka,

9 domin kuma ku yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji ya rantse zai ba kakanninku da zuriyarsu, ƙasar da yake da yalwar abinci.

10 Gama ƙasar da za ku shiga garin ku mallake ta, ba kamar ƙasar Masar take ba inda kuka fito, inda kukan shuka iri sa’an nan ku yi ta zuwa kuna banruwa kamar lambu.

11 Amma ƙasar da za ku haye ku mallaka, ƙasa ce ta tuddai da kwaruruka wadda ruwan sama yake shayar da ita.

12 Ƙasa ce kuma wadda Ubangiji Allahnku yake lura da ita, Ubangiji Allahnku yana dubanta kullum, tun daga farkon shekara har zuwa ƙarshenta.

13 “Idan kun yi biyayya da umarnansa waɗanda ya umarce ku da su yau, kun ƙaunaci Ubangiji Allahnku, kun bauta masa da zuciya ɗaya da dukan ranku,

14 zai shayar da ƙasarku da ruwa a kan kari, da ruwan bazara da na kaka. Za ku tattara sabon hatsinku da sabon ruwan inabinku, da manku.

15 Zai sa ciyawa ta tsiro a saurukanku domin dabbobinku. Za ku ci ku ƙoshi.

16 Ku lura fa, kada zuciya ta ruɗe ku, har ku kauce, ku bauta wa waɗansu alloli, ku yi musu sujada,

17 don kada Ubangiji ya yi fushi da ku, ya rufe sammai, ku rasa ruwa, ƙasa kuma ta kāsa ba da amfaninta, da haka za ku murmutu nan da nan a kyakkyawar ƙasar da Ubangiji yake ba ku.

18 “Sai ku riƙe zantuttukan nan nawa a zuciyarku da ranku. Za ku ɗaura su alama a hannuwanku, da goshinku.

19 Za ku koya wa ‘ya’yanku su, ku yi ta haddace su, sa’ad da kuke zaune a gida, da sa’ad da kuke tafiya, da sa’ad da kuke kwance, da sa’ad da kuka tashi.

20 Za ku rubuta su a madogaran ƙofofin gidajenku, da bisa ƙofofinku,

21 don kwanakinku da kwanakin ‘ya’yanku su yi tsawo a ƙasar da Ubangiji ya rantse wa kakanninku zai ba su muddin samaniya tana bisa duniya.

22 “Idan dai za ku lura, ku kiyaye dukan umarnan nan waɗanda nake umartarku ku kiyaye, ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya a dukan hanyoyinsa, ku manne masa,

23 sa’an nan Ubangiji zai kori al’umman nan duka a gabanku. Za ku kori al’umman da suka fi ku yawa da ƙarfi.

24 Duk inda tafin ƙafarku ya taka kuma zai zama naku. Iyakarku za ta kama daga jeji zuwa Lebanon da kuma daga Kogin Yufiretis zuwa Bahar Rum.

25 Ba mutumin da zai iya tsayayya da ku. Ubangiji Allahnku zai sa ƙasar ta firgita, ta ji tsoronku a duk inda kuka sa ƙafa, kamar yadda ya faɗa muku.

26 “Ga shi, yau, na sa albarka da la’ana a gabanku.

27 Za ku sami albarka idan kun yi biyayya da umarnan Ubangiji Allahnku waɗanda nake umartarku da su yau.

28 Za ku zama la’anannu idan ba ku kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku ba, amma kuka kauce daga hanyar da nake umartarku da ita yau, har ku bi waɗansu alloli waɗanda ba ku san su ba.

29 Sa’ad da Ubangiji Allahnku ya kai ku cikin ƙasar da za ku shiga ku mallake ta, sai ku ɗibiya albarkar a Dutsen Gerizim, ku ɗibiya la’anar kuma a Dutsen Ebal.

30 Duka biyunsu suna hayin Urdun ne, yamma da hanya a ƙasar Kan’aniyawa, mazaunan Araba, kusa da Gilgal, wajen itacen oak na More.

31 Gama za ku haye Urdun, ku shiga ƙasar da za ku mallaka, wadda Ubangiji Allahnku yake ba ku. Sa’ad da kuka mallake ta, kuka zauna a ciki,

32 sai ku lura, ku aikata dukan dokoki da farillai waɗanda nake sawa a gabanku yau.”