M. SH 10

Allunan Dutse na Biyu

1 “A lokacin nan kuwa Ubangiji ya ce mini, ‘Ka sassaƙa alluna biyu na dutse kamar na farko, ka hau zuwa wurina a bisa dutsen, ka kuma yi akwati na itace.

2 Ni kuma zan rubuta a allunan maganar da take kan alluna na farko waɗanda ka farfashe. Za ka ajiye su cikin akwatin.’

3 “Sai na yi akwati da itacen ƙirya, na kuma sassaƙa alluna biyu na dutse kamar na farko. Sai na hau dutsen da alluna biyu a hannuna.

4 Ubangiji kuwa ya sāke rubuta dokoki goma a allunan kamar na farko, wato dokoki goma ɗin nan da Ubangiji ya faɗa muku a dutse ta tsakiyar wuta a ranar taron. Sai Ubangiji ya ba ni su.

5 Na sauko daga dutsen, na ajiye allunan cikin akwatin da na yi, a nan suke kamar yadda Ubangiji ya umarce ni.”

6 (Isra’ilawa suka kama tafiya daga rijiyoyin Bene-ya’akan suka zo Mosera. Nan ne Haruna ya rasu, aka binne shi. Sai ɗansa Ele’azara, ya gāje shi a matsayinsa na firist.

7 Daga nan suka tafi Gudgoda, daga Gudgoda kuma suka tafi Yotbata, ƙasa mai rafuffukan ruwa.

8 A wannan lokaci ne Ubangiji ya keɓe kabilar Lawi domin su riƙa ɗaukar akwatin alkawari na Ubangiji, su kuma tsaya a gaban Ubangiji, su riƙa yi masa aiki, su kuma sa albarka da sunan Ubangiji kamar yadda yake a yau.

9 Domin haka kabilar Lawi ba su da rabo ko gādo tare da ‘yan’uwansu, Ubangiji shi ne gādonsu kamar yadda Ubangiji Allahnku ya faɗa musu.)

10 “Na sāke yin dare arba’in da yini arba’in a kan dutsen kamar dā. Ubangiji kuwa ya amsa addu’ata a lokacin kuma, ya janye hallaka ku.

11 Sai Ubangiji ya ce mini, ‘Tashi, ka tafi, ka kama tafiyarka a gaban jama’an nan domin su je, su shiga, su mallaki ƙasar da na rantse wa kakanninsu, zan ba su.’ ”

Abin da Ubangiji Yake So

12 “Yanzu fa, ya Isra’ilawa ga abin da Ubangiji Allahnku yake so a gare ku. Sai ku ji tsoron Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya cikin hanyoyinsa, ku ƙaunace shi, ku bauta wa Ubangiji Allahnku da zuciya ɗaya da dukan ranku.

13 Ku kiyaye umarnan Ubangiji da dokokinsa waɗanda nake umurtarku da su yau don amfanin kanku.

14 Duba, saman sammai, da duniya, da dukan abin da yake cikinta na Ubangiji Allahnku ne.

15 Duk da haka Ubangiji ya ƙaunaci kakanninku ya zaɓi zuriyarsu a bayansu daga cikin dukan sauran al’umma, kamar yadda yake a yau.

16 Saboda haka sai ku kame zukatanku, kada ku ƙara yin taurinkai.

17 Gama Ubangiji Allahnku, Allahn alloli ne, da Ubangijin iyayengiji. Shi Allah mai girma ne, mai iko, mai bantsoro, wanda ba ya son zuciya, ba ya karɓar hanci.

18 Yakan yi wa marayu da gwauraye na gaske shari’a da adalci. Yana ƙaunar baƙo, yakan ba shi abinci da sutura.

19 Sai ku ƙaunaci baƙo, gama dā ku baƙi ne a ƙasar Masar.

20 Sai kuma ku ji tsoron Ubangiji Allahnku, ku bauta masa. Ku manne masa, ku yi rantsuwa da sunansa.

21 Shi ne abin yabonku, shi ne Allahnku, wanda ya yi muku waɗannan al’amura masu girma, masu bantsoro waɗanda kuka gani da idanunku.

22 Kakanninku saba’in ne suka gangara zuwa Masar, amma yanzu Ubangiji Allahnku ya riɓaɓɓanya ku, kuka yi yawa kamar taurarin sama.”