Idin Ƙetarewa
1 “Ku kiyaye watan Abib don ku yi Idin Ƙetarewa ga Ubangiji Allahnku, gama a watan Abib ne Ubangiji Allahnku ya fito da ku daga Masar da dad dare.
2 Sai ku miƙa hadayar ƙetarewa daga garkenku na tumaki da na shanu ga Ubangiji Allahnku a wurin da Ubangiji ya zaɓa domin ya tabbatar da sunansa.
3 Kada ku ci abinci mai yisti tare da hadayar. Kwana bakwai za ku riƙa cin abinci marar yisti tare da hadayar, gama abincin wahala ne, gama da gaggawa kuka fita daga ƙasar Masar, don haka za ku tuna da ranar da kuka fito daga ƙasar Masar dukan kwanakinku.
4 Kada a iske yisti a ƙasarku duka har kwana bakwai. Kada kuma ku ajiye naman hadayar da kuka miƙa da yamma a rana ta fari ya kwana har safiya.
5 “Kada ku miƙa hadayar ƙetarewa a kowane garin da Ubangiji Allahnku yake ba ku.
6 Amma ku miƙa ta a wurin da Ubangiji Allahnku zai zaɓa don ya tabbatar da sunansa. Nan za ku miƙa hadayar ƙetarewa da yamma da faɗuwar rana, daidai da lokacin da kuka fito daga Masar.
7 Sai ku dafa shi, ku ci a inda Ubangiji Allahnku zai zaɓa. Da safe sai ku koma alfarwanku.
8 Kwana shida za ku yi kuna cin abinci marar yisti, amma a rana ta bakwai sai ku yi muhimmin taro saboda Ubangiji Allahnku. Kada ku yi aiki a wannan rana.
Idin Makonni
9 “Sai ku ƙirga mako bakwai, wato ku fara ƙirga mako bakwai ɗin daga lokacin da kuka fara sa lauje don ku yanke hatsinku da suke tsaye.
10 Sa’an nan sai ku yi Idin Makonni domin Ubangiji Allahnku. Za ku ba da sadaka ta yardar rai gwargwadon albarkar da Ubangiji Allahnku ya sa muku.
11 Sai ku yi murna a gaban Ubangiji Allahnku a inda Ubangiji Allahnku ya zaɓa don ya tabbatar da sunansa, ku da ‘ya’yanku mata da maza, da barorinku mata da maza, da Balawen da suke zaune a garinku, da baƙo, da maraya, da gwauruwa ta gaske, waɗanda suke zaune tare da ku.
12 Ku tuna fa, ku dā bayi ne a Masar, domin haka ku lura, ku kiyaye waɗannan dokoki.
Idin Bukkoki
13 “Za ku yi Idin Bukkoki kwana bakwai bayan da kun gama tattara amfaninku daga masussukanku, da wurin matsewar ruwan inabinku.
14 Sai ku yi murna a cikin idin, ku da ‘ya’yanku mata da maza, da barorinku mata da maza, da Balawe, da baƙo, da maraya, da gwauruwa ta gaske, waɗanda suke zaune tare da ku.
15 Za ku kiyaye idin ga Ubangiji Allahnku har kwana bakwai a inda Ubangiji zai zaɓa, gama Ubangiji Allahnku zai yalwata dukan amfanin gonakinku, da dukan ayyukan hannunku don ku cika da murna.
16 “Sau uku a shekara dukan mazajenku za su zo, su hallara a gaban Ubangiji Allahnku a inda zai zaɓa, wato a lokacin idin abinci marar yisti, da lokacin idin makonni, da kuma a lokacin Idin Bukkoki. Kada su hallara a gaban Ubangiji hannu wofi.
17 Kowane mutum zai kawo irin abin da ya iya, gwargwadon albarkar da Ubangiji Allahnku ya sa masa.”
Yin Shari’ar Gaskiya
18 “Sai ku naɗa alƙalai da shugabanni domin garuruwanku waɗanda Ubangiji Allahnku ya ba ku bisa ga kabilanku. Sai su yi wa jama’a shari’a da adalci.
19 Kada ku ɓata shari’a, kada ku yi sonzuciya, kada kuma ku karɓi hanci, gama cin hanci yakan makantar da idanun mai hikima, ya karkatar da maganar adali.
20 Adalci ne kaɗai za ku sa gaba domin ku rayu, ku mallaki ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku.
21 “Kada ku dasa kowane irin itace na tsafi kusa da bagaden Ubangiji Allahnku, wanda za ku gina.
22 Kada kuma ku kafa al’amudi, abin da Ubangiji Allahnku yake ƙi.”