M. SH 17

1 “Kada ku miƙa wa Ubangiji Allahnku hadaya da sa ko da tunkiyar da take da lahani ko naƙasa, gama wannan abar ƙyama ce ga Ubangiji Allahnku.

2 “Idan aka sami wata, ko wani, daga cikin wani gari da Ubangiji Allahnku yake ba ku, yana aikata abin da yake mugu a gaban Ubangiji Allahnku, yana karya alkawarinsa,

3 har ya je, ya bauta wa gumaka, ya yi musu sujada, ko rana, ko wata, ko ɗaya daga cikin rundunar sama, ya yi abin da na hana,

4 idan aka faɗa muku, ko kuwa kun ji labarinsa sai ku yi cikakken bincike. Idan gaskiya ce, aka kuma tabbata an yi wannan mugun abu cikin Isra’ilawa,

5 to, ku kawo macen, ko mutumin, da ya aikata wannan mugun abu a bayan ƙofar garinku, nan za ku jajjefe shi da duwatsu har ya mutu.

6 Bisa ga shaidar mutum biyu ko uku za a kashe shi, amma ba za a kashe mutum a kan shaidar mutum ɗaya ba.

7 Sai shaidun su fara jifansa sa’an nan sauran jama’a su jajjefe shi. Ta haka za a kawar da mugunta daga cikinsu.

8 “Idan aka kawo muku shari’a mai wuyar yankewa a ɗakin shari’arku, ko ta kisankai ce, ko ta jayayya ce, ko ta cin mutunci ce, ko kowace irin shari’a mai wuyar yankewa, sai ku tashi, ku tafi wurin da Ubangiji Allahnku zai zaɓa.

9 Za ku kai maganar wurin Lawiyawan da suke firistoci, ko kuma a wurin alƙalin da yake aiki a lokacin. Za ku tambaye su, za su faɗa muku yadda za a yanke shari’a.

10 Sai ku yanke shari’ar yadda suka faɗa muku daga wurin da Ubangiji ya zaɓa. Ku lura fa, ku yi yadda suka faɗa muku.

11 Dole ne ku yi yadda suka koya muku, da yadda suka yanke shari’ar. Kada ku kauce dama ko hagu daga maganar da suka faɗa muku.

12 Duk wanda ya yi izgili, ya ƙi yin biyayya da firist wanda yake a can, yana yi wa Ubangiji Allahnku hidima, ko kuma ya ƙi yi wa alƙalin biyayya, to, lalle sai a kashe wannan mutum. Ta haka za ku kawar da mugunta daga cikin Isra’ilawa.

13 Sa’an nan duk jama’a za su ji, su kuwa ji tsoro. Ba za su ƙara yin izgilanci ba kuma.”

Ka’idodin Zaman Sarki

14 “Sa’ad da kuka shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku don ku mallake ta, ku zauna a ciki, sa’an nan ku yi tunanin naɗa wa kanku sarki, kamar al’umman da suke kewaye da ku,

15 to, kwā iya naɗa wa kanku sarki wanda Ubangiji Allahnku ya zaɓa. Sai ku naɗa wa kanku sarki daga cikin jama’arku. Kada ku naɗa wa kanku baƙo wanda ba ɗan’uwanku ba.

16 Amma kada sarkin ya tattara wa kansa dawakai, kada kuma ya sa mutane su tafi Masar don su ƙaro masa dawakai, tun da yake Ubangiji ya riga ya yi muku kashedi da cewar, ‘Kada ku sāke komawa can.’

17 Kada kuma ya auri mata da yawa don kada zuciyarsa ta karkace. Kada kuma ya tattara wa kansa kuɗi da yawa.

18 Sa’ad da ya hau gadon sarautar, sai ya sa a rubuta masa dokoki daga cikin littafin dokoki wanda yake wurin Lawiyawan da suke firistoci.

19 Kada ya rabu da littafin, amma ya riƙa karanta shi dukan kwanakinsa domin ya koyi tsoron Ubangiji Allahnsa ta wurin kiyaye dukan dokoki da umarnai,

20 don kada zuciyarsa ta kumbura, har ya ga ya fi ‘yan’uwansa, don kuma kada ya karkace daga bin umarni zuwa dama ko hagu, don shi da ‘ya’yansa su daɗe, suna mulki a Isra’ila.”