Gādon Firistoci da Lawiyawa
1 “Lawiyawa da firistoci, wato dukan kabilar Lawi, ba su da rabo ko gādo tare da mutanen Isra’ila. Hadayun Ubangiji da dukan abin da ake kawo masa, su ne za su zama abincinsu.
2 Ba za su sami gādo tare da ‘yan’uwansu ba, Ubangiji ne gādonsu kamar yadda ya alkawarta musu.
3 “To, ga rabon da jama’a za su ba firistoci daga hadayun da suka miƙa, ko sā ne ko tunkiya ce, sai su ba firistoci kafaɗar, da kumatun, da tumbin.
4 Sai kuma ku ba su nunan fari na hatsinku, da ruwan inabinku, da manku, da kuma gashin tumakinku wanda kuka fara sausaya.
5 Gama Ubangiji Allahnku ya zaɓe su, su da ‘ya’yansu, daga dukan kabilanku don su yi aiki da sunan Ubangiji har abada.
6 “Balawe yana da dama ya tashi daga kowane gari na Isra’ila inda yake zaune ya je wurin da Ubangiji ya zaɓa.
7 Idan ya zo, sai ya yi aiki saboda sunan Ubangiji Allahnku kamar sauran ‘yan’uwansa Lawiyawa waɗanda suke aiki a gaban Ubangiji a can.
8 Zai sami rabon abincinsa daidai da saura, har da abin da yake na kakanninsa wanda ya sayar.”
Faɗakarwa a kan Ayyukan Arna
9 “Sa’ad da kuka shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, to, kada ku shiga kwaikwayon ayyuka na banƙyama na waɗannan al’ummai.
10 Kada a tarar da wani daga cikinku wanda zai sa ‘yarsu ko ɗansu ya wuce ta tsakiyar wuta, ko mai duba, ko mai maita, ko mai bayyana gaibi, ko mai sihiri,
11 ko boka, ko mabiya, ko maye, ko mai sha’ani da matattu.
12 Ubangiji yana ƙyamar mai yin waɗannan abubuwa. Saboda waɗannan ayyuka masu banƙyama shi ya sa Ubangiji Allahnku yake korar waɗannan al’ummai a gabanku.
13 Sai ku zama marasa aibu a gaban Ubangiji Allahnku.
Allah ya yi Alkawari zai Ta da wani Annabi kamar Musa
14 “Gama waɗannan al’ummai da za ku kora suna kasa kunne ga masu maita da masu duba, amma ku, Ubangiji Allahnku bai yarda muku ku yi haka ba.
15 “Ubangiji Allahnku zai tayar muku da wani annabi kamata daga cikin jama’arku, sai ku saurare shi.
16 “Wannan shi ne abin da kuka roƙa a wurin Ubangiji Allahnku a Horeb, a ranar taron, gama kun ce, ‘Kada ka bar mu mu ƙara jin muryar Ubangiji Allahnmu, ko mu ƙara ganin wannan babbar wuta, don kada mu mutu,’
17 Ubangiji kuwa ya ce mini, ‘Abin da suka faɗa daidai ne.
18 Zan tayar musu da wani annabi kamarka daga cikin ‘yan’uwansu. Zan sa magana a bakinsa, zai faɗa musu duk abin da na umarce shi.
19 Duk wanda bai saurari maganata wadda zai faɗa da sunana ba, ni da kaina zan nemi hakkinta a gare shi.
20 Amma duk wani annabin da ya yi izgili yana magana da sunana, ni kuwa ban umarce shi ba, ko kuwa yana magana da sunan gumaka, wannan annabi zai mutu.’
21 “Ya yiwu ku ce a zuciyarku, ‘Ƙaƙa za mu san maganar da Ubangiji bai faɗa ba?’
22 Sa’ad da annabi ya yi magana da sunan Ubangiji, idan abin da ya faɗa bai faru ba, bai zama gaskiya ba, to, wannan magana ba Ubangiji ne ya faɗa ba. Wannan annabi ya yi izgili ne kawai, kada ku ji tsoronsa.”