Albarkun Biyayya
1 “Idan kun yi biyayya da maganar Ubangiji Allahnku, kuna aikata dukan umarnansa waɗanda nake umartarku da su yau, to, Ubangiji Allahnku zai fifita ku fiye da dukan sauran al’umma.
2 Idan kun yi biyayya da maganar Ubangiji Allahnku, dukan albarkun nan za su sauko muku, su zama naku.
3 “Za ku zama masu albarka, ko kuna cikin gari, ko kuna cikin karkara.
4 “’Ya’yanku za su zama masu albarka, haka nan kuma amfanin gonakinku, da ‘ya’yan dabbobinku, da ‘ya’yan shanunku, da ‘ya’yan tumakinku da awakinku.
5 “Kwandunanku da makwaɓan za su yalwata ƙullunku.
6 “Da albarka za ku shiga, da albarka kuma za ku fita.
7 “Ubangiji zai sa ku fatattaki abokan gābanku a gabanku waɗanda suke tasar muku. Ta hanya guda za su auka muku, amma ta hanyoyi bakwai za su gudu daga gabanku.
8 “Ubangiji zai sa wa abin da yake cikin rumbunanku albarka da dukan aikin hannuwanku. Zai sa muku albarka a ƙasar da yake ba ku.
9 “Ubangiji zai sa ku zama tsattsarkar jama’arsa kamar yadda ya rantse muku, idan za ku kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya cikin tafarkunsa.
10 Dukan mutanen duniya za su gane ku na Ubangiji ne, za su ji tsoronku.
11 Ubangiji zai arzuta ku ƙwarai da ‘ya’ya, da ‘ya’yan dabbobi, da amfanin gona, a ƙasar da Ubangiji ya rantse wa kakanninku zai ba ku.
12 Ubangiji zai buɗe muku taskarsa ta sammai, don ya ba ƙasarku ruwa a kan kari, zai kuma sa albarka a kan dukan aikin hannuwanku. Al’ummai da yawa za su karɓi rance a wurinku, amma ku, ba za ku karɓi rance ba.
13 Ubangiji zai sa ku zama kai, ba wutsiya ba. Kullum ci gaba za ku yi, ba baya ba, idan kuka yi biyayya da umarnan Ubangiji Allahnku waɗanda nake umartarku da su yau, in kun lura, kun yi aiki da su,
14 idan kuma ba ku kauce zuwa dama ko hagu daga maganar da na umarce ku da ita yau ba, wato don ku bi waɗansu gumaka, ku bauta musu.”
Sakamakon Rashin Biyayya
15 “Amma idan ba za ku yi biyayya da Ubangiji Allahnku ba, ko kuwa ba ku lura kuka aikata umarnansa da dokokinsa waɗanda nake umartar da su yau ba, to, dukan waɗannan la’ana za su auko muku, su same ku.
16 “La’anannu za ku zama a gari da karkara.
17 “La’anannu ne kwandunanku da makwaɓan ƙullunku.
18 “La’anannu ne ‘ya’yanku, da amfanin gonakinku, da ‘ya’yan shanunku, da ‘ya’yan tumakinku da na awakinku.
19 “Da la’ana za ku shiga, da la’ana kuma za ku fita.
20 “Ubangiji zai aiko muku da la’ana, da ruɗewa, da damuwa cikin dukan abin da za ku yi, har ya hallaka ku, ku lalace da sauri saboda mugayen ayyukanku, domin kuma kuka rabu da ni.
21 Ubangiji zai aiko muku da annoba wadda za ta manne muku, ta cinye ku cikin ƙasar da za ku shiga, ku mallake ta.
22 Ubangiji zai buge ku da ciwon fuka, da zazzaɓi, da ciwon kumburi, da zafi mai tsanani, da fari, da burtuntuna, da fumfuna. Waɗannan za su yi ta damunku har ku lalace.
23 Samaniya da take bisa kanku za ta zama tagulla, ƙasar kuma da kuke a bisa kanta ta zama baƙin ƙarfe.
24 Ubangiji zai mai da ruwan sama na ƙasarku gāri da ƙura, zai zubo muku da shi daga sama har ku hallaka.
25 “Ubangiji zai sa abokan gabanku su rinjaye ku cikin yaƙi. Ta hanya guda za ku auka musu, amma ta hanyoyi bakwai za ku gudu daga gabansu. Za ku zama abin ƙi ga dukan mulkokin duniya.
26 Gawawwakinku za su zama abinci ga dukan tsuntsayen sama, da namomin duniya. Ba wanda zai kore su.
27 Ubangiji zai buge ku da marurai irin na Masar, da basur, da ƙazwa, da ƙaiƙayi waɗanda ba za su warke ba.
28 Ubangiji kuma zai buge ku da ciwon hauka, da makanta, da rikicewar hankali.
29 Da tsakar rana za ku riƙa lalubawa kamar makaho, ba za ku yi arziki cikin ayyukanku ba. Za a riƙa zaluntarku, ana yi muku ƙwace kullum, ba wanda zai cece ku.
30 “Za ku yi tashin yarinya, wani ne zai kwana da ita. Za ku gina gida, wani ne zai zauna a ciki. Za ku dasa inabinku, wani ne zai girbe amfanin.
31 Za a yanka sanku a idonku, amma ba za ku ci ba. Za a ƙwace jakinku ƙiri ƙiri a idonku, ba za a mayar muku da shi ba. Za a ba magabtanku tumakinku, ba wanda zai cece ku.
32 A idonku za a ba da ‘ya’yanku mata da maza ga wata al’umma dabam, za ku yi ta jin kewarsu, amma a banza, gama ba ku da ikon yin kome.
33 Mutanen da ba ku sani ba, su za su ci amfanin gonakinku da dukan amfanin wahalarku. Za a zalunce ku, a murƙushe ku kullum.
34 Abubuwan da idanunku za su gani za su sa ku zama mahaukata.
35 Ubangiji zai bugi gwiwoyinku da ƙafafunku da marurai tun daga tafin ƙafarku har zuwa ƙoƙwan kanku.
36 “Ubangiji zai bashe ku, ku da sarkin da kuka naɗa wa kanku ga wata al’ummar da ku da kakanninku ba ku sani ba. Can za ku bauta wa gumakan itace da na duwatsu.
37 Za ku zama abin ƙi, da abin karin magana, da abin habaici a cikin dukan mutane inda Ubangiji zai kora ku.
38 “Za ku shuka iri da yawa a gonakinku, amma kaɗan za ku girbe gama fara za su cinye.
39 Za ku dasa gonakin inabi, ku nome su, amma ba za ku sha ruwan inabin, ko ku tsinke ‘ya’yan inabin ba, gama tsutsa za ta cinye shi.
40 Za ku sami itatuwan zaitun ko’ina cikin ƙasarku, amma ba za ku sami man da za ku shafa ba, gama ‘ya’yan za su kakkaɓe.
41 Za ku haifi ‘ya’ya mata da maza, amma ba za su zama naku ba, gama za a kai su bauta.
42 Ƙwari za su cinye dukan itatuwanku da dukan amfanin ƙasarku.
43 “Baƙin da suke tare da ku za su yi ta ƙaruwa, ku kuwa za ku yi ta komawa baya baya.
44 Za ku karɓi rance a wurinsu, su ba za su karɓi rance a wurinku ba. Su za su zama kai, ku kuwa za ku zama wutsiya.
45 “Dukan waɗannan la’anoni za su auko muku, su bi ku, su same ku, har ku hallaka, domin ba ku yi biyayya da Ubangiji Allahnku ba, ba ku kiyaye umarnai da dokoki da ya umarce ku da su ba.
46 Za su zama alama da abin mamaki a kanku da zuriyarku har abada.
47 Ba ku bauta wa Ubangiji Allahnku da murna da farin ciki ba, saboda dukan abin da ya ba ku a yalwace,
48 domin haka za ku bauta wa magabtanku waɗanda Ubangiji zai turo muku. Za ku bauta musu da yunwa, da ƙishirwa, da tsiraici, da talauci. Za su sa karkiyar ƙarfe a wuyanka har su hallaka ku.
49 Ubangiji zai kawo wata al’umma daga nesa, wato daga bangon duniya, mai kai sura kamar gaggafa, wadda za ta yi gāba da ku. Al’ummar da ba ku san harshenta ba,
50 al’umma mai zafin hali, wadda ba ta kula da tsofaffi, ba ta kuma jin tausayin yara.
51 Za ta ci shanunku da amfanin ƙasarku har ku hallaka. Ba za ta bar muku hatsi ko ruwan inabi, ko mai, ko ‘ya’yan shanunku, ko na tumaki da na awakinku ba, har ta lalatar da ku.
52 Za su kewaye garuruwanku da yaƙi, har dogayen garukanku, da kagaranku waɗanda kuke dogara gare su, su rurrushe. Za su kewaye garuruwan ƙasarku da yaƙi a ƙasar da Ubangiji Allahnku ya ba ku.
53 Za ku ci naman ‘ya’yanku, mata da maza, waɗanda Ubangiji Allahnku ya ba ku, saboda irin tsananin kewayewar da magabtanku suka yi muku da yaƙi.
54 Nagarin mutum mai taushin zuciya wanda yake tare da ku, zai ƙi ɗan’uwansa, da matarsa, da ‘ya’yansa da suka ragu,
55 domin kada ya ba wani daga cikinsu naman ‘ya’yansa wanda yake ci, gama ba abin da ya rage masa saboda irin tsananin kewayewar garuruwanku da yaƙi wanda abokan gabanku suka kawo muku.
56 Matar kirki mai taushin zuciya wadda take tare da ku wadda ba za ta sa tafin ƙafarta a ƙasa ba saboda taushin zuciyarta da kyakkyawan halinta, za ta ƙi ƙaunataccen mijinta, da ɗanta, da ‘yarta.
57 A ɓoye za ta ci mahaifar da take biyo bayan ta haihu, da ‘ya’yan da za ta haifa, saboda ba ta da wani abinci lokacin da magabtanku za su kewaye garuruwanku da yaƙi mai tsanani.
58 “Idan ba ku lura, ku aikata dukan maganar dokokin nan da aka rubuta a wannan littafi ba, domin ku ji tsoron sunan nan mai ɗaukaka, mai kwarjini, wato sunan Ubangiji Allahnku,
59 to, Ubangiji zai aukar muku, ku da zuriyarku, da munanan masifu waɗanda ba su kawuwa, da mugayen cuce-cuce marasa warkewa.
60 Sai ya sāke kawo muku cuce-cuce irin na Masar, waɗanda kuka ji tsoronsu, za su kuwa manne muku.
61 Har yanzu kuma Ubangiji zai kawo muku kowace irin cuta, da kowace irin annoba, waɗanda ba a ambace su a littafin dokokin nan ba, har ku hallaka.
62 Ko da yake kuna da yawa kamar taurarin sama, za ku zama ‘yan kaɗan, domin ba ku yi biyayya da maganar Ubangiji Allahnku ba.
63 Kamar yadda Ubangiji ya ji daɗi ya arzuta ku, ya riɓaɓɓanya ku, haka nan kuma zai ji daɗi ya lalatar da ku, ya hallaka ku. Za a fitar da ku daga ƙasar da za ku shiga, ku mallaka.
64 “Ubangiji zai warwatsa ku cikin dukan al’ummai daga wannan bangon duniya zuwa wancan. Can za ku bauta wa gumakan itace da na dutse waɗanda ku da kakanninku ba ku san su ba.
65 Ba za ku sami zaman lafiya wurin waɗannan al’ummai ba, ko tafin ƙafarku ma ba zai sami wurin hutawa ba. Ubangiji kuma zai sa fargaba a zuciyarku, ya sa idanunku su lalace, ranku zai yi suwu.
66 Kullum ranku zai kasance da damuwa, za ku zauna da tsoro dare da rana, kuna tsoron abin da zai sami ranku.
67 Da safe za ku ce, ‘Da ma maraice ne.’ Da maraice kuma za ku ce, ‘Da ma safiya ce,’ saboda tsoron da yake a zuciyarku, da abubuwan da idanunku suke gani.
68 Ubangiji zai komar da ku Masar cikin jiragen ruwa, ko da yake na ce ba za ku ƙara tafiya can ba. Can za ku sayar da kanku bayi mata da maza, amma ba wanda zai saye ku.”