M. SH 29

Alkawarin Ubangiji da Isra’ilawa a Ƙasar Mowab

1 Waɗannan ne zantuttukan alkawari da Ubangiji ya umarci Musa ya faɗa wa Isra’ilawa a ƙasar Mowab, wato banda alkawarin da ya yi da su a bisa Dutsen Horeb.

2 Sai Musa ya kira dukan Isra’ilawa ya ce musu, “Ai, kun ga dukan abin da Ubangiji ya yi wa Fir’auna da barorinsa a dukan ƙasar Masar.

3 Idanunku sun ga manyan wahalai, da alamu, da mu’ujizai masu girma.

4 Duk da haka har wa yau Ubangiji bai ba ku zuciyar ganewa, ko idanun gani, ko kunnuwan ji ba.

5 Shekara arba’in na bi da ku cikin jeji. Rigunanku da takalmanku ba su tsufa ba.

6 Ba ku ci hatsi ba, ba ku kuma sha ruwan inabi ba, ko barasa, don ku sani shi ne Ubangiji Allahnku.

7 Sa’ad da kuka isa wannan wuri, sai Sihon Sarkin Heshbon, da Og, Sarkin Bashan, suka fito su yi yaƙi da mu, amma muka ci su.

8 Muku ƙwace ƙasarsu, muka ba Ra’ubainawa, da Gadawa, da rabin kabilar Manassa, su gāda.

9 Saboda haka sai ku kiyaye, ku aikata dukan zantuttukan wannan alkawari don ku arzuta a cikin dukan abin da za ku yi.

10 “Yau, ga ku nan tsaye, dukanku a gaban Ubangiji Allahnku, shugabannin kabilanku, da dattawanku, da shugabannin sojojinku, da dukan mazajen Isra’ila,

11 da ‘ya’yanku, da matanku, da baƙin da suke a zangonku, da mai yi muku faskare ko mai ɗebo muku ruwa.

12 Don ku ƙulla alkawari da Ubangiji Allahnku, alkawarin da Ubangiji Allahnku yake yi da ku yau.

13 Don ya mai da ku jama’arsa yau, shi kuma ya zama Allahnku kamar yadda ya yi muku magana, da yadda kuma ya rantse wa kakanninku, wato Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu.

14 Ba da ku kaɗai nake yin wannan alkawari ba,

15 amma da wanda ba ya nan tare da mu yau, da shi wanda yake tare da mu a nan yau, a gaban Ubangiji Allahnmu.

16 “Kun sani dai yadda muka zauna a ƙasar Masar, da yadda muka yi ta ratsawa ta tsakiyar al’ummai muka wuce.

17 Kun ga abubuwan da suke da su masu banƙyama, wato gumakansu na itace, da na dutse, da na azurfa, da na zinariya.

18 Kada zuciyar wani mutum, ko ta wata mata ko na wani iyali, ko wata kabila cikinku yau, ta bar bin Ubangiji Allahnku, ta koma ga bauta wa gumakan al’umman nan. Kada a iske wani tushe a cikinku mai ba da ‘ya’ya masu dafi, masu ɗaci.

19 Idan wani mutum ya ji zantuttukan la’anan nan sa’an nan ya sa wa kansa albarka a zuciyarsa, yana cewa, ‘Ba abin da zai same ni ko na bi taurin zuciyata,’ wannan zai haddasa lalacewar ɗanye da busasshe gaba ɗaya.

20 Ubangiji ba zai gafarce shi ba, amma fushin Ubangiji da kishinsa za su auko a kan wannan mutum, dukan la’anar kuma da aka rubuta a littafin nan za ta bi ta kansa, Ubangiji kuma zai shafe sunansa daga duniya.

21 Ubangiji zai ware mutumin nan daga dukan kabilan Isra’ila, don ya hukunta shi bisa ga dukan la’anar da aka rubuta a wannan littafin dokoki.

22 “Tsararraki masu zuwa nan gaba, wato ‘ya’yan da za su gaje ku, da baƙon da ya zo daga ƙasa mai nisa, za su ga annobar ƙasar, da cuce-cucen da Ubangiji zai ɗora mata.

23 Dukan ƙasa za ta zama kibritu da gishiri, ba shuka, ba amfani, ciyawa kuma ba ta tsirowa, kamar yadda Ubangiji ya kabantar da Saduma da Gwamrata, da Adam da Zeboyim, da zafin fushinsa.

24 Dukan al’ummai za su ce, ‘Me ya sa Ubangiji ya yi haka da wannan ƙasa? Me ya sa ya yi fushi mai tsanani haka?’

25 Sa’an nan jama’a za su ce, ‘Saboda sun yi watsi da alkawarin Ubangiji Allah na kakanninsu, wato alkawarin da ya yi da su sa’ad da ya fisshe su daga ƙasar Masar.

26 Suka tafi suka bauta wa gumaka, suka yi musu sujada, gumakan da ba su san su ba, ba Ubangiji ne ya ba su ba.

27 Saboda haka Ubangiji ya husata da wannan ƙasa, ya kawo mata kowace irin la’anar da aka rubuta a wannan littafin.

28 Ubangiji ya tumɓuke su da zafin fushinsa, da babbar hasala, daga ƙasarsu, ya watsa su cikin wata ƙasa dabam kamar yadda suke a yau.’

29 “Sanin gaibu na Ubangiji Allahnmu ne, amma abubuwan da aka bayyana namu ne, mu da ‘ya’yanmu har abada, don mu kiyaye dukan maganar dokokin nan.”