Isra’ilawa Sun Ci Og na Bashan
1 “Muka ci gaba da tafiyarmu muka nufi Bashan. Sai Og, Sarkin Bashan, tare da dukan jama’arsa suka fito su yi yaƙi da mu a Edirai.
2 Sai Ubangiji ya ce mini, ‘Kada ka ji tsoronsu, gama da shi, da jama’arsa duka, da ƙasarsa, zan bashe su a hannunka. Sai ka yi masa kamar yadda ka yi wa Sihon, Sarkin Amoriyawa, wanda yake zaune a Heshbon.’
3 “Haka fa Ubangiji Allahnmu ya ba da Og, Sarkin Bashan, da dukan jama’arsa a hannunmu. Muka karkashe su duka, ba wanda muka bari da rai.
4 Muka ƙwace dukan garuruwansa a wannan lokaci. Ko gari guda ɗaya, ba mu bar musu ba, garuruwa sittin, da dukan yankin Argob, da mulkin Og a Bashan.
5 Dukan garuruwan nan masu dogo garu ne, da ƙofofi masu ƙyamaren ƙarfe. Banda waɗannan kuma akwai garuruwa da yawa marasa garu.
6 Muka hallaka su ƙaƙaf kamar yadda muka yi da Sihon, Sarkin Heshbon. Muka hallaka kowane gari, da mata da maza, da yara.
7 Amma muka riƙe dabbobi da dukiyar da muka kwaso daga garuruwan, ganima.
8 “A lokacin ne fa muka ƙwace wannan ƙasa daga hannun sarakunan nan biyu na Amoriyawa, wato ƙasa wadda take a hayin Urdun, daga kwarin kogin Arnon zuwa Dutsen Harmon.”
9 (Sidoniyawa suka kira Harmon, Siriyon, amma Amoriyawa suna ce da shi Senir.)
10 “Wato dukan garuruwa na ƙasar tudu, da dukan ƙasar Gileyad, da ta Bashan har zuwa Salka da Edirai, garuruwa na mulkin Og ke nan cikin ƙasar Bashan.”
11 (Sai Og, Sarkin Bashan, ne kaɗai ya ragu daga cikin Refayawa. Gadonsa na ƙarfe ne. Gadon yana nan a Rabbah ta Ammonawa. Tsawonsa kamu tara, faɗinsa kuma kamu huɗu ne.)
Ra’ubainu, da Gad, da Rabin Kabilar Manassa Sun Zauna a Gabashin Urdun
12 “Sa’ad da muka mallaki ƙasar a wannan lokaci, sai na ba Ra’ubainawa da Gadawa yankin ƙasar daga Arower wadda take gefen kwarin kogin Arnon, da rabin ƙasar tuddai ta Gileyad tare da garuruwanta.
13 Sauran ƙasar Gileyad, da dukan ƙasar Bashan wadda take ƙarƙashin mulkin Og, wato dukan yankin ƙasar Argob.”
(Duk dai yankin ƙasan nan wadda ake kira ƙasar Refayawa.) “Na ba da ita ga rabin kabilar Manassa.”
14 (Yayir na zuriyar Manassa ya karɓi dukan yankin ƙasar Argob a Bashan har zuwa iyakar Geshurawa da Ma’akatiyawa. Sai ya kira ƙauyukan wurin da sunansa, Hawot-yayir.)
15 “Na ba Makir Gileyad.
16 Na ba Ra’ubainawa da Gadawa yankin ƙasar da ta tashi daga Gileyad har zuwa kwarin Arnon, tsakiyar kwarin shi ne iyakar har zuwa kwarin kogin Yabbok wanda ya yi iyaka da Ammonawa.
17 Na kuma ba su Araba, Urdun shi ne iyaka daga Kinneret, har zuwa Tekun Araba, wato Tekun Gishiri, a gangaren gindin Dutsen Fisga wajen gabas.
18 “A wancan lokaci ne na yi muku umarni, na ce, ‘Ubangiji Allahnku ya ba ku wannan ƙasa, ku mallake ta. Dukan mayaƙanku za su haye da shirin yaƙi a gaban ‘yan’uwanku, Isra’ilawa.
19 Amma matanku, da ‘ya’yanku, da dabbobinku, na sani kuna da dabbobi da yawa, su ne za ku bari a garuruwan da na ba ku,
20 har lokacin da Ubangiji ya zaunar da ‘yan’uwanku kamar yadda ya zamshe ku, su ma su mallaki ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba su a hayin Urdun, sa’an nan kowa zai koma ga mallakarsa.’
21 “A lokacin kuwa na umarci Joshuwa na ce, ‘Ai, da idonka ka ga dukan abin da Ubangiji Allahnku ya yi wa waɗannan sarakuna biyu. Haka nan kuwa Ubangiji zai yi wa mulkoki waɗanda za ku haye zuwa wurinsu.
22 Kada kuwa ku ji tsoronsu, gama Ubangiji Allahnku ne zai yi yaƙi dominku.’ ”
Ba a Yarda wa Musa Ya Shiga Kan’ana Ba
23 “Sa’an nan kuma na roƙi Ubangiji, na ce,
24 ‘Ya Ubangiji Allah, kai ne ka fara nuna wa baranka ɗaukakarka da ikonka. Ba wani Allah a Sama ko a duniya da zai aikata ayyuka na banmamaki irin naka.
25 Ka yarje mini, ina roƙonka in haye in ga wannan kyakkyawar ƙasa a hayin Urdun, ƙasan nan mai kyau ta tuddai, da Lebanon.’
26 “Amma Ubangiji ya yi fushi da ni saboda ku, don haka bai ji ni ba. Ya ce mini, ‘Ya isa. Kada ma ka sāke yi mini magana a kan wannan al’amari.
27 Ka hau kan ƙwanƙolin Dutsen Fisga, ka dubi gabas, da yamma, da kudu, da arewa. Ka dubi ƙasar da idanunka, gama ba za ka haye Urdun ba.
28 Amma ka umarci Joshuwa, ka ƙarfafa shi. Shi ne zai jagorar jama’ar nan, su haye, shi ne kuma wanda zai rarraba musu gādon ƙasar da za ka gani.’
29 “Sai muka zauna a kwari daura da Bet-feyor.”