Musa Ya Gargaɗi Isra’ilawa Su Yi Biyayya
1 “Yanzu, ya Isra’ilawa, sai ku kiyaye dokoki da farillai da nake koya muku don ku rayu, ku shiga ku kuma mallaki ƙasar da Ubangiji Allah na kakanninku suke ba ku.
2 Kada ku ƙara, ko ku rage kome daga cikin abin da na umarce ku, amma ku kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku, waɗanda nake umartarku da su.
3 Idanunku sun ga abin da Ubangiji ya yi a Ba’al-feyor, yadda Ubangiji Allahnku ya hallaka dukan mutane daga cikinku da suka bauta wa Ba’al-feyor.
4 Amma ku da kuka dogara ga Ubangiji Allahnku, a raye kuke har yau.
5 “Ga shi, na koya muku dokoki da farillai, yadda Ubangiji Allah ya umarce ni, don ku kiyaye su a ƙasa wadda kuke shiga ku mallake ta.
6 Ku kiyaye su, ku aikata su, gama yin haka zai tabbatar wa sauran al’ummai, kuna da hikima da ganewa. Sa’ad da al’ummai za su ji waɗannan dokoki, za su ce, ‘Ba shakka, wannan babbar al’umma tana da hikima da ganewa.’
7 “Gama babu wata babbar al’umma wadda allahnta yake kusa da ita kamar yadda Ubangiji Allahnmu yake kusa da mu sa’ad da muka kira gare shi.
8 Ko kuwa, da akwai wata babbar al’umma wadda take da dokoki da farillai na adalci kamar waɗannan dokoki da na sa a gabanku yau?”
An Tuna wa Isra’ilawa abin da ya Same su a Horeb
9 “Sai ku lura, ku kiyaye kanku sosai, don kada ku manta da abubuwan da kuka gani da idonku kada kuma su fita a ranku dukan kwanakinku. Ku sanar wa ‘ya’yanku da jikokinku da su,
10 da yadda kuma a waccan rana kuka tsaya a gaban Ubangiji Allahnku a Horeb, sa’ad da Ubangiji ya ce mini, ‘Ka tattara mini jama’a domin su ji maganata, su koyi tsorona dukan kwanakinsu a duniya, su kuma koya wa ‘ya’yansu.’
11 “Sai kuka matso kusa, kuka tsaya a gindin dutsen sa’ad da dutsten yake cin wuta har zuwa sararin sama, ga kuma girgije baƙi ƙirin yana rufe da dutsen.
12 Ubangiji kuwa ya yi magana da ku ta tsakiyar wuta. Kuka ji hurcin kalmomin, amma ba ku ga siffar kome ba, sai dai murya kaɗai kuka ji.
13 Shi ne ya hurta muku shari’ar da ya umarce ku ku kiyaye, wato dokokin nan goma. Ya rubuta su a allunan dutse guda biyu.
14 Duk da haka Ubangiji ya umarce ni in koya muku dokokin da farillan don ku aikata su a ƙasar da kuke hayewa zuwa ciki don ku mallake ta.”
Faɗakarwa a kan Gumaka
15 “Domin haka, sai ku kula da kanku sosai, gama ba ku ga siffar kome ba sa’ad da Ubangiji Allahnku ya yi magana da ku a Horeb ta tsakiyar wuta.
16 don kada ku yi mugunta, ku sassaƙa wa kanku wata siffar kowane abu, ko siffar mace ko ta namiji,
17 ko siffar dabbar da take a duniya, ko siffar tsuntsun da yake tashi a sararin sama,
18 ko siffar kowane abu mai jan ciki bisa ƙasa, ko siffar kifin da yake cikin ruwa ƙarƙashin ƙasa.
19 Ku lura fa, sa’ad da kuka dubi sama, kuka ga rana, da wata, da taurari, da dai dukan rundunar sama, don kada fa ku jarabtu, ku yi musu sujada, ko ku bauta musu. Ubangiji Allahnku ya sa waɗannan saboda dukan al’ummai.
20 Amma ku, Ubangiji ya fisshe ku daga gidan bauta mai zafi, wato Masar, don ku zama jama’arsa ta musamman kamar yadda kuke a yau.
21 Amma Ubangiji ya yi fushi da ni sabili da ku, har ya rantse, cewa ba zan haye Urdun in shiga kyakkyawar ƙasan nan wadda yake ba ku abar gādo ba.
22 Gama a nan ƙasar zan mutu, ba zan haye Urdun ba, amma ku za ku haye, ku mallaki wannan kyakkyawar ƙasa.
23 Saboda haka, ku lura fa, kada ku manta da alkawarin da Ubangiji Allahnku ya yi da ku, don haka kada ku sassaƙa wa kanku wata siffar kowane irin kamanni wanda Ubangiji Allahnku ya hana ku.
24 Gama Ubangiji Allahnku wuta ne mai cinyewa, shi kuma mai kishi ne.
25 “Sa’ad da kuka haifi ‘ya’ya, kuka sami jikoki, kuka kuma daɗe cikin ƙasar, idan kuka yi abin da yake haram, wato kuka yi gunki na sassaƙa na kowace irin siffa, kuka kuma aikata mugunta a gaban Ubangiji Allahnku har kuka tsokane shi ya yi fushi,
26 to, yau na kira sama da duniya su shaida a kanku, cewa lalle za ku hallaka nan da nan cikin ƙasar da za ku haye Urdun zuwa cikinta don ku mallake ta. Ba za ku daɗe cikinta ba, amma za a shafe ku ƙaƙaf.
27 Ubangiji zai warwatsa ku cikin al’ummai. Za ku ragu kaɗan daga cikin al’ummai inda Ubangiji ya warwatsa ku.
28 Can za ku bauta wa gumaka na itace, da na duwatsu, aikin hannuwan mutum, waɗanda ba su gani, ko ji, ko ci, ko sansana.
29 Amma idan kun nemi Ubangiji Allahnku a can inda kuke, za ku same shi muddin kun neme shi da zuciya ɗaya, da dukan ranku.
30 Sa’ad da wahala ta same ku, waɗannan abubuwa kuma suka auko muku nan gaba, za ku juyo wurin Ubangiji Allahnku, ku yi masa biyayya.
31 Ubangiji Allahnku, Allah mai jinƙai ne. Faufau, ba zai kunyata ku ba, ba kuwa zai hallaka ku ba, ba kuma zai manta da alkawarin da ya rantse wa kakanninku ba.
32 “Ku tambaya mana, ko a kwanakin dā kafin zamaninku, tun ma daga lokacin da Allah ya yi mutum a duniya, ku tantambaya daga wannan kusurwa ta samaniya zuwa waccan, ko wani babban abu irin wannan ya taɓa faruwa, ko kuma an taɓa jin labarin irinsa?
33 Akwai wata jama’a da ta taɓa jin muryar wani allah tana magana ta tsakiyar wuta kamar yadda kuka ji, har suka rayu?
34 Ko kuma, da akwai wani allah wanda ya taɓa ƙoƙarin fitar da al’umma saboda kansa daga cikin tsakiyar wata al’umma ta wurin wahalai, da alamu, da mu’ujizai, da yaƙi, da nuna iko, da babbar razana kamar yadda Ubangiji Allahnku ya yi dominku a ƙasar Masar a kan idonku duka?
35 An nuna muku wannan don ku sani Ubangiji shi ne Allah, banda shi, ba wani kuma.
36 Ya sa ku ji muryarsa daga Sama don ya horar da ku. Ya kuma sa ku ga babbar wutarsa a duniya, kuka kuma ji muryarsa daga cikin wutar.
37 Saboda ya ƙaunaci kakanninku shi ya sa ya zaɓi zuriyarsu a bayansu, shi kansa kuma ya fisshe ku daga Masar da ikonsa mai girma.
38 Ya kori al’ummai a gabanku waɗanda suka fi ku girma da iko, ya kawo ku a ƙasarsu, ya ba ku ita abar gādo kamar yadda yake a yau.
39 Domin haka, yau sai ku sani, ku kuma riƙe a zuciyarku, cewa Ubangiji shi kaɗai ne Allah a sama da duniya. Banda shi, ba wani kuma.
40 Sai ku kiyaye dokokinsa da umarnansa waɗanda na umarce ku da su yau, don zaman lafiyarku da na ‘ya’yanku a bayanku, domin kuma ku yi tsawon rai a ƙasa wadda Ubangiji Allahnku yake ba ku har abada.”
Biranen Mafaka a Hayin Gabashin Urdun
41 Sai Musa ya keɓe birane uku a hayin gabashin Urdun,
42 domin wanda ya yi kisankai ya gudu zuwa can, wato wanda ya kashe mutum ba da niyya ba, babu kuma ƙiyayya tsakaninsu a dā. In ya gudu zuwa ɗaya daga cikin biranen zai tsirar da kansa.
43 Biranen su ne, Bezer cikin jeji a kan tudu domin Ra’ubainawa, da Ramot cikin Gileyad domin Gadawa, da Golan cikin Bashan domin Manassawa.
Gabatarwa a kan Maimaita Dokoki
44 Waɗannan su ne dokokin da Musa ya ba Isra’ilawa,
45 su ne kalmomi, da dokoki, da farillai, waɗanda Musa ya faɗa wa jama’ar Isra’ila, bayan da sun fito Masar,
46 a hayin Urdun a kwari daura da Bet-feyor, a ƙasar Sihon, Sarkin Amoriyawa, mazaunan Heshbon, waɗanda Musa da Isra’ilawa suka ci da yaƙi sa’ad da suka fita daga ƙasar Masar.
47 Suka mallaki ƙasar Sihon, da ƙasar Og, Sarkin Bashan, sarakuna biyu na Amoriyawa waɗanda suke a hayin gabashin Urdun.
48 Ƙasar ta kama daga Arower wanda yake a kwarin kogin Arnon zuwa dutsen Siriyon, wato Harmon,
49 da dukan Araba a hayin gabashin Urdun, har zuwa tekun Araba a gindin gangaren Fisga.