NEH 4

Ma’aikata sun Tsare Kansu

1 Sa’ad da Sanballat ya ji muna ginin garun, sai ya husata ƙwarai, ya yi wa Yahudawa ba’a.

2 Ya yi magana a gaban ‘yan’uwansa da sojojin Samariya ya ce, “Mene ne waɗannan Yahudawa kumamai suke yi? Za su mai da abubuwa yadda suka a dā ne? Za su miƙa hadayu ne? Za su gama ginin a rana ɗaya ne? Za su iya samun duwatsun gini daga tsibin matattun duwatsu?”

3 Tobiya Ba’ammone yana kusa da shi, ya ce, “Ai, garun da suke ginawa da duwatsu, ko dila ya hau, sai ya rushe shi!”

4 Sai ni, Nehemiya, na yi addu’a, na ce, “Ka ji, ya Allahnmu, gama ana raina mu, ka sa ba’arsu ta koma kansu, ka sa a washe su a kai su ƙasar bauta.

5 Kada ka shafe laifinsu, kada kuwa ka gafarta musu, gama sun ci mutuncinmu, mu da muke gini.”

6 Muka gina garun, har ya kai rabin tsayinta, domin mutane sun himmatu da aikin.

7 Amma sa’ad da Sanballat, da Tobiya, da Larabawa, da Ammonawa, da mutanen Ashdod, suka ji yadda ginin garun Urushalima yake ci gaba, ana kuma tattoshe tsattsaguwa, sai suka husata.

8 Dukansu suka ƙulla za su zo, su yi yaƙi da Urushalima, su ta da hankali a cikinta.

9 Sai muka yi addu’a ga Allahnmu, muka sa masu tsaro su yi mana tsaro dare da rana saboda su.

10 Mutanen Yahuza kuwa suka ce,

“Ƙarfin ma’aikata yana kāsawa,

Akwai komatsai da yawa da za a kwashe,

Yaya za mu iya gina garun yau?”

11 Abokan gābanmu kuma suka ce, “Ba za su sani ba, ba kuwa za su gan mu ba, sai dai kawai su gan mu a cikinsu, za mu karkashe su, mu tsai da aikin.”

12 Da Yahudawan da suke zaune kusa da su suka zo, suka yi ta nanata mana irin shirin abokan gabanmu, wato za su zo su fāɗa mana.

13 Saboda haka na sa jama’a su ja ɗamara bisa ga iyalinsu a bayan garu, a wuraren da ba a gina ba. Suna riƙe da takuba, da māsu, da bakuna.

14 Da na ga mutane sun damu, sai na tashi na yi magana da shugabanni, da sauran jama’a, na ce, “Kada ku ji tsoro, ku tuna da Ubangiji mai iko, mai banrazana, ku yi yaƙi domin ‘yan’uwanku, da ‘ya’yanku mata da maza, da matanku, da gidajenku.”

15 Da abokan gābanmu suka ji mun san shirinsu, Ubangiji kuwa ya wargaje shirinsu, sai dukanmu muka koma wurin garun, kowa ya kama aikinsa.

16 Daga wannan rana, sai rabin barorina suka yi ta gini, rabi kuwa suna riƙe da māsu, da garkuwoyi, da bakuna, da sulke. Shugabannin kuwa suka goyi bayan dukan Yahudawa sosai.

17 Masu ginin garun da masu ɗaukan kaya suna yi da hannu ɗaya, hannu ɗaya kuma na riƙe da makami.

18 Kowane magini yana rataye da takobinsa sa’ad da yake gini. Mai busa ƙaho yana kusa da ni.

19 Sai na ce wa manya da shugabanni, da sauran jama’a, “Aikin nan babba ne, mai yawa kuma, ga shikuwa, muna rarrabe a kan garun nesa da juna.

20 Duk inda kuka ji an busa ƙaho, sai ku taru a wurin. Allahnmu zai yi yaƙi dominmu.”

21 Haka kuwa muka yi aikin, rabinmu na riƙe da māsu tun daga wayewar gari har zuwa fitowar taurari.

22 A wannan lokaci kuma na ce wa jama’a, kowane mutum tare da baransa ya kwana a Urushalima domin a yi tsaro da dare, da safe kuma a kama aiki.

23 Saboda haka ni, da ‘yan’uwana, da barorina, da matsaran da suke tare da ni, ba wanda ya tuɓe tufafinsa. Kowa yana riƙe da makami.