RUT 1

Elimelek da Iyalinsa a Mowab

1 A zamanin da mahukunta suke mulkin Isra’ila, aka yi yunwa a ƙasar. Sai wani mutumin Baitalami a Yahudiya ya yi ƙaura zuwa ƙasar Mowab, shi da matarsa, da ‘ya’yansa maza biyu.

2 Sunan mutumin, Elimelek, matarsa kuwa Na’omi, ‘ya’yanta maza kuma Malon da Kiliyon. Su Efratawa ne daga Baitalami ta Yahudiya. Suka tafi Mowab suka zauna a can.

3 Elimelek, mijin Na’omi, ya rasu, aka bar Na’omi da ‘ya’yansu maza biyu.

4 Sai suka auri ‘yan matan Mowab, Orfa da Rut. Bayan da suka yi wajen shekara goma a can,

5 sai kuma Malon da Kiliyon suka rasu, Na’omi kuwa ta rasa mijinta da kuma ‘ya’yanta maza biyu.

Na’omi da Rut sun Komo Baitalami

6 Daga can Mowab, Na’omi ta ji cewa, Ubangiji ya taimaki mutanensa, ya ba su abinci, sai ta tashi daga ƙasar Mowab tare da surukanta.

7 Suka kama hanya zuwa ƙasar Yahudiya.

8 Amma a hanya, sai Na’omi ta ce wa surukanta, “Bari ko waccenku ta koma gidan iyayenta. Ubangiji ya yi muku alheri kamar yadda kuka yi mini alheri, ni da marigayan.

9 Ya sa kuma ko waccenku ta yi aure, ta sami hutawa a gidan miji.” Sa’an nan ta yi bankwana da su ta sumbace su.

Sai suka fashe da kuka,

10 suka ce mata, “A’a, mā tafi tare da ke wurin mutanenki.”

11 Amma Na’omi ta ce musu, “Ku koma, ‘ya’yana, don me za ku tafi tare da ni? Ina da sauran ‘ya’ya maza a cikina ne da za su zama mazajenku?

12 Sai ku koma, ‘ya’yana, gama na tsufa da yawa, ba kuma zan sami miji ba. Ko da a ce ina fata in yi aure, a ce ma zan yi aure a daren nan, in haifi ‘ya’ya maza,

13 za ku yi ta jira har su yi girma? Ai, ba zai yiwu ba, ‘ya’yana. Ina baƙin ciki ƙwarai saboda abin da ya same ku, da yadda Ubangiji ya yi gāba da ni.”

14 Suka sāke fashewa da kuka. Sai Orfa ta yi wa surukarta, sumba, ta yi bankwana da ita, amma Rut ta manne mata.

15 Na’omi ta ce wa Rut, “Kin ga, ‘yar’uwarki ta koma wurin mutanenta da wurin gumakanta, sai ki koma, ki bi ‘yar’uwarki.”

16 Amma Rut ta ce, “Kada ki yi ta roƙona in rabu da ke, ko in bar binki, gama inda za ki tafi, ni ma can zan tafi, inda kuma za ki zauna, ni ma can zan zauna. Mutanenki za su zama mutanena, Allahnki kuma zai zama Allahna.

17 Inda za ki rasu, ni ma can zan rasu, a binne ni. Idan na bar wani abu ya raba ni da ke, in dai ba mutuwa ba, to, Ubangiji ya yi mini hukunci mai zafi!”

18 Da Na’omi ta ga Rut ta ƙudura ta tafi tare da ita, sai ta ƙyale ta.

19 Su biyu kuwa suka kama hanya har suka isa Baitalami. Da suka isa Baitalami, sai dukan garin ya ruɗe saboda su. Mata suka ce, “Na’omi ce wannan?”

20 Ita kuwa ta ce musu, “Kada ku kira ni Na’omi, wato mai farin ciki, sai dai Mara, wato mai baƙin ciki, gama Mai Iko Dukka ya wahalshe ni ƙwarai.

21 Na tafi a wadace, ga shi, Ubangiji ya komo da ni hannu wofi. Don me kuke kirana mai farin ciki da yake Ubangiji Mai Iko Dukka ya wahalshe ni, ya kuma aukar mini da masifa?”

22 Haka Na’omi ta koma daga ƙasar Mowab tare da surukarta Rut, mutuniyar Mowab. Suka isa Baitalami a farkon kakar sha’ir.