ZAB 20

Addu’ar Neman Nasara

1 Ubangiji ya amsa maka a ranar wahala!

Allah na Yakubu ya kiyaye ka!

2 Ya aiko maka da taimako daga Haikalinsa,

Ya kawo maka gudunmawa daga Sihiyona.

3 Ya karɓi hadayunka,

Ya kuma ji daɗin dukan sadakokinka.

4 Ya ba ka abin da kake bukata,

Ya sa dukan shirye-shiryenka su yi nasara.

5 Mu kuma, sai mu yi sowa ta farin ciki saboda ka ci nasara,

Mu yi bikin cin nasara da ka yi,

Da yabon Ubangiji Allahnmu.

Allah ya amsa dukan roƙe-roƙenka!

6 Yanzu dai na sani Ubangiji yakan ba da nasara ga zaɓaɓɓen sarkinsa,

Yakan amsa masa daga samaniyarsa mai tsarki,

Da ikonsa mai girma yakan sa shi yă yi nasara.

7 Waɗansu ga karusan yaƙinsu suke dogara,

Waɗansu kuwa ga dawakansu,

Amma mu, ga ikon Ubangiji Allahnmu muke dogara!

8 Za su yi tuntuɓe su fāɗi,

Amma mu za mu tashi mu tsaya daram!

9 Ka ba sarki nasara, ya Ubangiji,

Ubangiji zai amsa mana sa’ad da muka yi kira.