ZAB 23

Ubangiji Makiyayina Ne

1 Ubangiji makiyayina ne,

Ba zan rasa kome ba.

2 Yana sa ni in huta a saura mai ɗanyar ciyawa,

Yana bi da ni a tafkuna masu daɗin ruwa, suna kwance lif.

3 Yana ba ni sabon ƙarfi.

Yana bi da ni a hanyar da suke daidai kamar yadda ya alkawarta.

4 Ko da hanyan nan ta bi ta tsakiyar duhu na mutuwa,

Ba zan ji tsoro ba, ya Ubangiji,

Gama kana tare da ni!

Sandanka na makiyayi da kerenka

Suna kiyaye lafiyata.

5 Ka shirya mini liyafa

Inda maƙiyana duk za su iya ganina,

Ka marabce ni, ka shafe kaina da mai,

Ka cika tanduna fal da mai.

6 Hakika, alherinka da ƙaunarka

Za su kasance tare da ni muddin raina.

Haikalinka zai zama gidana har abada.