ZAB 24

Sarkin Ɗaukaka

1 Duniya da dukan abin da yake cikinta na Ubangiji ne,

Duniya da dukan mazaunanta nasa ne.

2 Ya gina ta a bisa ruwa mai zurfi na ƙarƙashin ƙasa,

Ya kuma kafa harsashinta a zurfin teku.

3 Wa yake da iko yă hau tudun Ubangiji?

Wa yake da iko ya shiga Haikalinsa tsattsarka?

4 Sai wanda yake da tsarki cikin aiki, da tunani,

Wanda ba ya yi wa gumaka sujada,

Ko kuma yă yi alkawarin ƙarya.

5 Ubangiji zai sa masa albarka,

Allah Mai Cetonsa zai kuɓutar da shi.

6 Su ne irin mutanen da suke zuwa wurin Allah,

Waɗanda suke zuwa a gaban Allah na Yakubu.

7 A buɗe ƙofofi sosai,

A buɗe daɗaɗɗun ƙofofi,

Babban Sarki kuwa zai shigo!

8 Wane ne wannan babban Sarki?

Ubangiji ne mai ƙarfi mai iko,

Ubangiji mai nasara cikin yaƙi!

9 A buɗe ƙofofi sosai,

A buɗe daɗaɗɗun ƙofofi,

Babban Sarki kuwa zai shigo!

10 Wane ne wannan babban Sarki?

Ubangiji Mai Runduna, shi ne babban Sarki!