ZAB 6

Addu’ar Neman Jinƙai a Lokacin Wahala

1 Ya Ubangiji, kada ka yi fushi, ka kuma tsauta mini!

Kada ka hukunta ni da fushinka!

2 Ka ji tausayina, gama na gaji tiƙis,

Ka wartsarkar da ni, gama na tafke sarai.

3 Duk na damu ƙwarai da gaske.

Sai yaushe wannan zai ƙare, ya Ubangiji?

4 Ya Ubangiji, ka zo ka cece ni,

Gama kana ƙaunata, ka kuɓutar da ni daga mutuwa.

5 Ba za a tuna da kai a lahira ba,

Ba wanda zai yabe ka a can!

6 Na gaji tiƙis saboda baƙin ciki,

Kowane dare gadona yakan jiƙe saboda kukana.

Matashin kaina ya yi sharkaf da hawaye.

7 Idanuna sun yi kumburi saboda yawan kuka,

Har da ƙyar nake iya gani,

Duk kuwa saboda abokan gābana!

8 Ku tafi daga nan, ku masu aikin mugunta!

Ubangiji yana jin kukana.

9 Yana kasa kunne ga kukana na neman taimako,

Yana kuwa amsa addu’o’ina.

10 Abokan gābana duka za su sha kunyar fāɗuwarsu,

Suna cikin matsanancin ruɗami,

Za a kwashe su farat ɗaya.