Dawuda Ya ji Labarin Rasuwar Saul da Jonatan
1 Bayan rasuwar Saul, sa’ad da Dawuda ya komo daga karkashe Amalekawa, ya yi kwana biyu a Ziklag.
2 Kashegari sai ga wani mutum ya zo daga sansanin Saul, da tufafinsa a yayyage, da ƙura kuma a kansa. Da ya zo wurin Dawuda sai ya fāɗi ƙasa, ya yi gaisuwa.
3 Sai Dawuda ya tambaye shi, ya ce, “Daga ina ka zo?”
Ya ce, “Na tsere ne daga sansanin Isra’ilawa.”
4 Dawuda ya ce masa, “Faɗa mini abin da ya faru.”
Sai ya ce, “Mutane sun gudu daga bakin dāga, an kuma kashe galibin mutanenmu. Saul da ɗansa Jonatan kuma sun mutu.”
5 Dawuda ya ce wa mutumin, “Ta yaya ka sani Saul da ɗansa, Jonatan, sun mutu?”
6 Mutumin kuwa ya amsa ya ce, “Ya zama fa ina kan dutsen Gilbowa, sai ga Saul ya jingina a māshinsa. Karusai da mahayan dawakan abokan gāba sun rutsa shi.
7 Da ya waiga, ya gan ni, sai ya kira ni, ni kuwa na amsa, na ce, ‘Ga ni.’
8 Ya ce mini, ‘Wane ne kai?’ Na ce masa, ‘Ni Ba’amaleke ne.’
9 Sai ya ce mini, ‘Zo ka kashe ni gama ina cikin azaba, amma raina bai fita ba.’
10 Sai na tafi na kashe shi domin na tabbata ba zai yi rai ba bayan ya fāɗi. Na kuma cire kambin da yake kansa da ƙarau da yake a dantsensa. Ga su, na kawo wa ubangijina.”
11 Sai Dawuda ya yayyage tufafinsa. Dukan mutanen da suke tare da shi kuma suka yayyage nasu.
12 Suka yi makoki, da kuka, da azumi har maraice saboda Saul, da Jonatan ɗansa, da mutanen Ubangiji, da gidan Isra’ila domin an Karkashe su a yaƙi.
13 Dawuda ya ce wa mutumin nan da ya kawo labarin, “Daga ina ka zo?”
Sai ya ce masa, “Ai, ni ɗan wani baƙo ne, Ba’amaleke.”
14 Dawuda ya ce, “Me ya sa ba ka ji tsoro ka miƙa hannunka, ka hallaka wanda Ubangiji ya keɓe ba?”
15 Sai Dawuda ya kira ɗaya daga cikin samarin, ya ce masa, “Ka kashe shi.” Ya dai buge shi, ya mutu.
16 Dawuda kuwa ya ce, “Alhakin jininka yana bisa kanka tun da yake da bakinka ka ce, ‘Ni ne na kashe wanda Ubangiji ya keɓe.’ ”
Dawuda Ya Yi Makoki domin Saul da Jonatan
17 Sai Dawuda ya raira waƙar makoki domin Saul da Jonatan, ɗansa.
18 Ya umarta a koya wa mutanen Yahuza wannan waƙa. (An rubuta ta a littafin Yashar.)
19 “An kashe darajarki, ya Isra’ila, a kan tuddanki!
Jarumawan sojojinmu sun fāɗi!
20 Kada a ba da labarin a Gat,
Ko a titin Ashkelon.
Kada ku sa matan Filistiyawa su yi murna,
Kada ku sa ‘yan matan arna su yi farin ciki.
21 “Kada ruwan sama ko raɓa su zubo kan tuddan Gilbowa.
Da ma gonakinta su zama marasa ba da amfani.
Gama a can ne aka zube garkuwoyin jarumawa a wulakance,
Tsatsa ta rufe garkuwar Saul.
22 Bakan Jonatan mai kisa ne,
Takobin Saul ba shi da jinƙai,
Yana kashe masu iko, yana kuma kashe abokan gāba.
23 “Saul da Jonatan ƙaunatattu ne, suna da bansha’awa,
A raye suna tare, haka kuma a mace suna tare.
Sun fi gaggafa sauri,
Sun fi zaki ƙarfi.
24 “Ku ‘yan matan Isra’ila, ku yi makoki domin Saul!
Ya suturta ku da mulufi mai ƙayatarwa,
Ya yi muku adon lu’ulu’u da zinariya.
25 “Jarumawa sun fāɗi,
An kashe su a bakin dāga.
Jonatan na kwance matacce a tuddai.
26 “Na damu ƙwarai saboda kai, ɗan’uwana Jonatan,
Ƙaunatacce kake a gare ni!
Ƙaunarka a gare ni abar al’ajabi ce,
Ta fi ƙaunar mace.
27 “Jarumawa sun fāɗi,
Makamansu ba su da sauran amfani.”