1 KOR 1

Gaisuwa

1 Daga Bulus, manzo kirayayye na Almasihu Yesu da yardar Allah, da kuma ɗan’uwanmu Sastanisu,

2 zuwa ga ikkilisiyar Allah da take a Koranti, wato, su waɗanda aka keɓe a cikin Almasihu Yesu, tsarkaka kirayayyu, tare da dukan waɗanda a ko’ina suke addu’a, da sunan Ubangijinmu Yesu Almasihu, Ubangijinsu da namu duka.

3 Alheri da salama na Allah Ubanmu, da na Ubangiji Yesu Almasihu su tabbata a gare ku.

Godiya saboda Bayebaye na Ruhu

4 Kullum nakan gode wa Allah dominku, saboda alherin Allah da aka yi muku baiwa ta hanyar Almasihu Yesu,

5 har ta kowace hanya aka wadata ku a cikinsa, a wajen yin magana duka da ilimi duka–

6 domin kuwa an tabbatar da shaida a kan Almasihu a cikinku.

7 Har ma ku ba kāsassu ba ne a wajen samun kowace baiwar Allah, kuna zuba ido ga bayyanar Ubangijinmu Yesu Almasihu.

8 wanda zai tabbatar da ku har ya zuwa ƙarshe, ku kasance marasa abin zargi a ranar Ubangijinmu Yesu Almasihu.

9 Allah mai alkawari ne, shi ne kuma ya kira ku ga tarayya da Ɗansa Yesu Almasihu Ubangijinmu.

Tsattsaguwa a Ikkilisiya

10 Na roƙe ku ‘yan’uwa, saboda sunan Ubangijinmu Yesu Almasihu, cewa dukanku bakinku yă zama ɗaya, kada wata tsaguwa ta shiga a tsakaninku, sai dai ku haɗa kai, kuna da nufi ɗaya, ra’ayinku ɗaya.

11 Don kuwa, ya ‘yan’uwana, mutanen gidan Kuluwi sun ba ni labari, cewa akwai jayayya a tsakaninku.

12 Abin da nake nufi, shi ne kowannenku yana faɗar abu dabam, “Ni na Bulus ne,” wani kuwa, “Ni na Afolos ne,” wani kuwa, “Ni na Kefas ne,” ko kuwa, “ni na Almasihu ne.”

13 Ashe, Almasihu a rarrabe yake? Ko Bulus ne aka gicciye dominku? Ko kuwa an yi muku baftisma ne da sunan Bulus?

14 Na gode Allah da ban yi wa waninku baftisma ba, banda Kirisbus da Gayus,

15 kada wani ya ce da sunana ne aka yi muku baftisma.

16 Ai, kuwa lalle na yi wa jama’ar gidan Istifanas ma. Amma banda waɗannan ban san ko na yi wa wani baftisma ba.

17 Ai, ba don in yi baftisma Almasihu ya aiko ni ba, sai dai in sanar da bishara, ba kuwa da gwanintar iya magana ba, domin kada a wofinta ƙarfin gicciyen Almasihu.

Almasihu Ikon Allah Ne, da Hikimarsa

18 Maganar gicciye, maganar wauta ce ga waɗanda suke hallaka, amma ƙarfin Allah ce a gare mu, mu da ake ceto.

19 Domin a rubuce yake cewa,

“Zan rushe hikimar mai hikima,

Zan kuma shafe haziƙancin haziƙi.”

20 To, ina masu hikima suke? Ina kuma masana? Ina masu muhawwarar zamanin nan? Ashe, Allah bai fallashi hikimar duniyar nan a kan wauta ce ba?

21 Da yake bisa ga hikimar Allah, duniya ba ta san Allah ta wurin hikimarta ba, sai Allah ya ji daɗin ceton masu ba da gaskiya, ta wurin wautar shelar bishara.

22 Yahudawa kam, mu’ujiza suke nema su gani, Helenawa kuwa hikima suka nema su samu,

23 mu kuwa muna wa’azin Almasihu gicciyeyye, abin sa yin tuntuɓe ga Yahudawa, wauta kuma ga al’ummai,

24 amma ga waɗanda suke kirayayyu, ko Yahudawa ko al’ummai duka biyu, Almasihu ikon Allah ne, da hikimar Allah.

25 Domin abin da aka zata wauta ce ta Allah, ya fi hikimar ɗan adam, abin da kuma aka zata rauni ne na Allah, ya fi duk ƙarfin ɗan adam.

26 Ku dubi kiranku da aka yi, ya ku ‘yan’uwa, a cikinku, ai, ba a kira masu hikima irin ta duniya da yawa ba, masu iko kuma ba su da yawa, haka ma masu asali ma ba yawa.

27 Amma Allah ya zaɓi abin da yake wauta a duniya, domin ya kunyata masu hikima. Allah ya zaɓi abin da yake rarrauna a duniya, domin ya kunyata ƙaƙƙarfa.

28 Allah ya zaɓi abin da yake ƙasƙantacce, wulakantacce a duniya, har ma abubuwan da ba su, domin yă shafe abubuwan da suke akwai.

29 Wannan kuwa duk don kada wani ɗan adam yă yi fariya a gaban Allah ne.

30 Gama Allah ne ya sa kuka zama na Almasihu Yesu, Allah ne kuma ya sa Almasihu ya zama hikima a gare mu. Ta wurin Almasihu ne kuma muka sami adalci, da tsarkakewa da fansa.

31 Saboda haka, “Duk mai yin alfarma, yă yi da Ubangiji” (abin da yake a rubuce ke nan).