1 KOR 6

Kada a Kai Ƙara Gaban Marasa Bi

1 In waninku yana da wata ƙara a game da ɗan’uwansa, ashe, zai yi ƙurun kai maganar a gaban marasa adalci, ba a gaban tsarkaka ba?

2 Ashe, ba ku sani ba, tsarkaka ne za su yi wa duniya shari’a? In kuwa ku ne za ku yi wa duniya shari’a, ashe, ba za ku iya shari’ar ƙananan al’amura ba?

3 Ba ku sani ba, za mu yi wa mala’iku shari’a, balle al’amuran da suka shafi zaman duniyar nan?

4 In kuwa kuna da irin waɗannan ƙararraki, don me kuma kuke kai su gaban waɗanda su ba kome ba ne, a game da Ikkilisiya?

5 Na faɗi wannan ne don ku kunyata. Ashe, wato, ba ko mutum ɗaya mai hikima a cikinku, da zai iya sasanta tsakanin ‘yan’uwa?

6 Amma ɗan’uwa yakan kai ƙarar ɗan’uwa, gaban marasa ba da gaskiya kuma?

7 Ku yi ƙarar juna ma, ai, hasara ce a gare ku. Ba gara ku haƙura a cuce ku ba? Ku kuma haƙura a zambace ku?

8 Amma, ga shi, ku da kanku kuna cuta, kuna zamba, har ma ‘yan’uwanku kuke yi wa!

9 Ashe, ba ku sani ba, marasa adalci ba za su sami gādo a cikin Mulkin Allah ba? Kada fa a yaudare ku! Ba fasikai, ko matsafa, ko mazinata, ko masu luɗu da maɗugo,

10 ko ɓarayi, ko makwaɗaita, ko mashaya, ko masu zage-zage, ko mazambata, da za su sami gādo a cikin Mulkin Allah.

11 Waɗansunku ma dā haka suke, amma an wanke ku, an tsarkake ku, an kuma kuɓutar da ku, da sunan Ubangiji Yesu Almasihu, da kuma Ruhun Allahnmu.

Ku Ɗaukaka Allah da Jikinku

12 “Dukan abubuwa halal ne a gare ni,” amma ba dukan abubuwa ne masu amfani ba. “Abu duka halal na a gare ni,” amma ba zan zama bawan kome ba.

13 “Abinci don ciki aka yi shi, ciki kuma don abinci”–Allah kuma zai hallaka duka biyu, wannan da wancan. Jiki kam, ba don fasikanci yake ba, sai dai domin Ubangiji, Ubangiji kuma domin jiki.

14 Allah ya ta da Ubangiji daga matattu, haka mu ma zai ta da mu da ikonsa.

15 Ashe, ba ku sani ba jikinku gaɓoɓin Almasihu ne? Ashe kuma, sai in ɗauki gaɓoɓin Almasihu in mai da su gaɓoɓin karuwa? Faufau!

16 Ashe, ba ku sani ba, duk wanda ya tara da karuwa, sun zama jiki ɗaya ke nan? Domin a rubuce yake cewa, “Su biyun za su zama jiki ɗaya.”

17 Duk wanda kuwa yake haɗe da Ubangiji, sun zama ɗaya a ruhu ke nan.

18 Ku guji fasikanci. Duk sauran zunubin da mutum yake yi bai shafi jikinsa ba, amma mai yin fasikanci, yana ɗaukar alhalin jikinsa ne.

19 Ashe, ba ku sani ba, jikinku Haikali ne na Ruhu Mai Tsarki wanda yake a zuciyarku, wanda kuka kuma samu a gun Allah? Ai, ku ba mallakar kanku ba ne.

20 Sayenku aka yi da tamani. To, sai ku ɗaukaka Allah da jikinku.