1 KOR 7

Damuwar da take a cikin Aure

1 To, a yanzu, a game da abin da kuka rubuto, yana da kyau mutum ya zauna ba aure.

2 Amma don gudun fasikanci sai kowane mutum ya kasance da matarsa, kowace mace kuma da mijinta.

3 Miji yă ba matarsa hakkinta na aure, haka kuma matar ga mijinta.

4 Matar kuwa ba ta da iko da jikinta, sai dai mijin, haka kuma mijin ba shi da iko da jikinsa, sai dai matar.

5 Kada ɗayanku yă ƙaurace wa ɗaya, sai ko da yardar juna zuwa wani ɗan lokaci kaza, don ku himmantu ga addu’a, sa’an nan ku sāke haɗuwa, kada Shaiɗan yă zuga ku ta wajen rashin kamewa.

6 Na fadi wannan ne bisa ga shawara, ba bisa ga umarni ba.

7 Da ma a ce kowa kamar ni yake mana! Sai dai kowa da irin baiwar da Allah ya yi masa, wani iri kaza, wani kuma iri kaza.

8 Abin da na gani ga waɗanda ba su yi aure ba, da kuma mata gwauraye, ya kyautu a gare su su zauna ba aure kamar yadda nake.

9 In kuwa ba za su iya kamewa ba, to, sai su yi aure. Ai, gwamma dai a yi aure da sha’awa ta ci rai.

10 Masu aure kuwa ina yi musu umarni, ba kuwa ni ba, Ubangiji ne, cewa kada mace ta rabu da mijinta

11 (in kuwa ta rabu da shi, sai ta zauna haka ba aure, ko kuwa ta sāke shiryawa da mijinta), miji kuma kada ya saki matarsa.

12 Ga sauran, ni nake faɗa, ba Ubangiji ba, in wani ɗan’uwa yana da mace marar ba da gaskiya, ta kuma yarda su zauna tare, to, kada yă rabu da ita.

13 Mace kuma mai miji marar ba da gaskiya, ya kuwa yarda su zauna tare, to, kada ta rabu da shi.

14 Don miji marar ba da gaskiya, a tsarkake yake a wajen matarsa. Mace marar ba da gaskiya kuma, a tsarkake take a wajen mijinta. In ba haka ba, zai zamana ‘ya’yanku ba masu tsarki ba ne, amma ga hakika masu tsarki ne.

15 In kuwa shi, ko ita, marar ba da gaskiya ɗin yana son rabuwa, to, sai su rabu. A wannan hali, ɗan’uwa ko ‘yar’uwa mai bi, ba tilas a kansu, domin Allah ya kira mu ga zaman lafiya.

16 Ke mace, ina kika sani ko za ki ceci mijinki? Kai miji, ina ka sani ko za ka ceci matarka?

Zaman da Ubangiji Ya Nufa

17 Sai dai kowa yă yi zaman da Ubangiji ya sa masa, wanda kuma Allah ya kira shi a kai. Haka nake umarni a dukan Ikilisiyoyi.

18 Duk wanda Allah ya kira, wanda dā ma yake da kaciya, to, kada yă nemi zama marar kaciya. Wanda kuwa ya kira yana marar kaciya, to, kada yă nema a yi masa kaciya.

19 Don kaciya da rashin kaciya ba sa hassala kome, sai dai kiyaye umarnin Allah.

20 Kowa yă zauna a maƙamin da Allah ya kiraye shi.

21 In ya kira ka kana bawa, kada ka damu. In kuwa kana iya samun ‘yanci, ai, sai ka samu.

22 Wanda aka kiraye shi ga tafarkin Ubangiji yana bawa, ai, ‘yantacce ne na Ubangiji. Kuma, wanda aka kira shi yana ɗa, bawa ne na Almasihu.

23 Da tamani aka saye ku. Kada fa ku zama bayin mutane.

24 To, ‘yan’uwa, duk halin da aka kira mutum a ciki, sai yă zauna a kai, yana zama tare da Allah.

Marasa Aure da Mata Gwauraye

25 A game da matan da ba su yi aure ba kuwa, ba ni da wani umarnin Ubangiji, amma ina ba da ra’ayina ne a kan ni amintacce ne, bisa ga jinƙan Ubangiji.

26 Na dai ga ya yi kyau mutum yă zauna yadda yake, saboda ƙuncin nan da yake gabatowa.

27 In da igiyar aure a wuyanka, to, kada ka nemi tsinkewa. In kuwa ba igiyar aure a wuyanka, to, kada ka nemi aure.

28 Amma kuwa in ka yi aure, ba ka yi zunubi ba, ko budurwa ma ta yi aure, ba ta yi zunubi ba. Duk da haka dai, duk masu yin aure za su ji jiki, niyyata kuwa in sawwaƙe muku.

29 Abin da nake nufi ‘yan’uwa, lokacin da aka ƙayyade ya ƙure. A nan gaba masu mata su zauna kamar ba su da su,

30 masu kuka kamar ba kuka suke yi ba, masu farin ciki ma kamar ba farin ciki suke yi ba, masu saye kuma kamar ba su riƙe da kome,

31 masu moron duniya kuma, kada su ba da ƙarfi ga moronta. Don yayin duniyar nan mai shuɗewa ne.

32 Ina so ku ‘yantu daga damuwa. Mutum marar aure yakan tsananta kula da sha’anin Ubangiji, yadda zai faranta wa Ubangiji rai.

33 Mutum mai aure kuwa, yakan tsananta kula da sha’anin duniya, yadda zai faranta wa matarsa rai.

34 Hankalinsa ya rabu biyu ke nan. Mace marar aure, ko budurwa, takan tsananta kula da sha’anin Ubangiji, yadda za ta kasance tsattsarka a jiki, da kuma a rai. Mace mai aure kuwa takan tsananta kula da sha’anin duniya, yadda za ta faranta wa mijinta rai.

35 Na faɗi haka ne, don in taimake ku, ba don in ƙuntata muku ba, sai dai don in kyautata zamanku, da nufin ku himmantu ga bautar Ubangiji ba da raba hankali ba.

36 Ga zancen ‘ya budurwa, wadda ta zarce lokacin aure, idan mahaifinta ya ga bai kyauta mata ba, in kuwa hali ya yi, sai yă yi abin da ya nufa, wato, a yi mata aure, bai yi zunubi ba.

37 In kuwa ya zamana ba lalle ne yă yi wa ‘yar tasa budurwa aure ba, amma ya tsai da shawara bisa ga yadda ya nufa, ya kuma ƙudura sosai a ransa, a kan tsare ta, to, haka daidai ne.

38 Wato, wanda ya yi wa ‘yar tasa budurwa aure, ya yi daidai, amma wanda bai aurar da ita ba, ya fi shi.

39 Igiyar aure tana wuyan mace, muddin mijinta yana da rai. In kuwa mijinta ya mutu, to, tana da dama ta auri wanda take so, amma fa, sai mai bin Ubangiji.

40 Amma a nawa ra’ayi, za ta fi farin ciki, in ta zauna a yadda take. A ganina kuwa ina da Ruhun Allah.