1 TAS 2

Hidimar Bulus a Tasalonika

1 Ai, ku da kanku kun sani, ‘yan’uwa, ziyartarku da muka yi, ba a banza take ba.

2 Amma ko da yake dā ma can mun sha wuya, an kuma wulakanta mu a Filibi, kamar yadda kuka sani, duk da haka da taimakon Allahnmu muka sanar da ku bisharar Allah gabagaɗi, amma sai da matsanancin fama.

3 Ai, gargaɗin da muke yi muku babu bauɗewa ko munafunci a ciki, balle yaudara,

4 sai dai kamar yadda Allah ya yarda da mu, ya damƙa mana amanar bishara, haka muke sanar da ita, ba domin mu faranta wa mutane rai ba, sai dai domin mu faranta wa Allah, shi da yake jarraba zukatanmu.

5 Yadda kuka sani, ba mu taɓa yin daɗin baki ko kwaɗayi ba. Allah kuwa shi ne shaida.

6 Ba mu kuwa taɓa neman girma ga mutane ba, ko a gare ku, ko ga waɗansu, ko da yake da muna so, da mun mori ikon nan namu na manzannin Almasihu.

7 Amma mun nuna taushin hali a cikinku, kamar yadda mai goyo take kula da goyonta.

8 Saboda kuma muna Kaunarku ƙwarai da gaske ne shi ya sa muke jin daɗin ba da har rayukanmu ma saboda ku, ba yi muku bisharar Allah kaɗai ba, don kun shiga ranmu da gaske.

9 Ya ku ‘yan’uwa, kuna iya tunawa da wahala da famar da muka sha, har muna aiki dare da rana, don kada mu nauyaya wa kowane ɗayanku, duk sa’ad da muke yi muku bisharar Allah.

10 Ku shaidu ne, haka kuma Allah, game da irin halin da muka nuna muku, ku masu ba da gaskiya, wato halin tsarki da na adalci da na rashin aibu.

11 Domin kun san yadda muka yi wa kowannenku gargaɗi kamar uba da ‘ya’yansa ne, muna ta’azantar da ku, muna kuma ƙarfafa muku umarnin, cewa

12 ku yi zaman da ya cancanci bautar Allah, wanda yake kiranku ga mulkinsa da ɗaukakarsa.

13 Saboda wannan ne kuma muke gode wa Allah ba fasawa, domin sa’ad da kuka karɓi Maganar Allah ta bakinmu, ba ku karɓe ta kamar maganar mutum ce ba, sai dai ainihin yadda take, Maganar Allah, wadda take aiki a cikin zuciyarku, ku masu ba da gasikya.

14 ‘Yan’uwa, ku ne kuka zama masu koyi da ikilisiyoyin Allah da suke na Almasihu Yesu, waɗanda suke a ƙasar Yahudiya, don ku ma kun sha wuya a hannun mutanen ƙasarku, kamar yadda ikilisiyoyin nan ma suka sha a hannun Yahudawa,

15 waɗanda suka kashe Ubangiji Yesu da annabawa, suka kuma kore mu, ba sa yin aikin da Allah yake so, masu gāba ne kuma da dukan mutane,

16 suna hana mu yi wa al’ummai wa’azi, don kada su sami ceto. Ta haka a kullum suke cika mudun zunubansu. Amma fa fushin Allah ya aukar musu.

Nufin Bulus Ya Sāke Ziyartar Ikkilisiya

17 Ya ku ‘yan’uwa, ko da yake mun yi kewarku saboda an raba mu a ɗan lokaci kaɗan, duk da haka kuna cikin zukatanmu, mun kuwa ƙara ɗokanta mu gan ku ido da ido, matuƙar ɗoki.

18 Mun dai yi niyyar zuwa wurinku, ni Bulus, ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba, amma Shaidan ya hana.

19 Su wane ne abin sa zuciyarmu, da abin farin cikinmu, da kuma abin taƙamarmu a gaban Ubangiji Yesu a ranar komowarsa, in ba ku ba?

20 Ai, ku ne abin taƙamarmu, da abin farin cikinmu.