1 TAS 1

Gaisuwa

1 Daga Bulus, da Sila, da Timoti, zuwa ga Ikkilisiyar Tasalonikawa, wadda take ta Allah uba da Ubangiji Yesu Almasihu.

Alheri da salama su tabbata a gare ku.

Bangaskiyar Tasalonikawa da Irin Zamansu

2 A kullum muna gode wa Allah saboda ku duka, koyaushe muna ambatonku a cikin addu’armu,

3 ba ma fāsa tunawa da aikinku na bangaskiya a gaban Allahnmu, Ubanmu, da famar da kuke yi domin ƙauna, da kuma begen ku mara gushewa ga Ubangijinmu Yesu Almasihu.

4 Domin mun sani, ‘yan’uwa, ƙaunatattu na Allah, shi ya zaɓe ku,

5 domin bishararmu ba da magana kawai ta zo muku ba, amma da iko, da Ruhu Mai Tsarki, da kuma matuƙar tabbatarwa. Kun dai san irin zaman da muka yi a cikinku domin ku amfana,

6 har kuka zama masu koyi da mu, da kuma Ubangiji, kuka kuma karɓi Maganar Allah game da farin cikin da Ruhu Mai Tsarki yake sawa, ko da yake ta jawo muku tsananin wahala.

7 Ku ma har kuka zama abin koyi ga dukan masu ba da gaskiya a ƙasar Makidoniya da ta Akaya.

8 Domin daga gare ku ne aka baza Maganar Ubangiji, ba ma a ƙasar Makidoniya da ta Akaya kaɗai ba, har ma a ko’ina bangaskiyarku ga Allah ta shahara, har ma ya zamana, ba sai lalle mun faɗa ba.

9 Domin su da kansu suke ba da labarin irin ziyartarku da muka yi, da kuma yadda kuka rabu da gumaka, kuka juyo ga Allah, domin ku bauta wa Allah Rayayye na gaskiya,

10 ku kuma saurari komowar Ɗansa daga Sama, wanda ya tasa daga matattu, wato Yesu, mai kuɓutar da mu daga fushin nan mai zuwa.