KOL 4

1 Ku iyayengiji kuma, ku riƙi bayinku da gaskiya da daidaita, da yake kun sani ku ma kuna da Ubangiji a Sama.

2 Ku lazamci yin addu’a, kuna zaune a faɗake a kanta sosai, tare da gode wa Allah,

3 mu ma ku yi mana addu’a Allah ya buɗe mana hanyar yin Maganarsa, mu sanar da asirin Almasihu, wanda saboda shi ne nake a ɗaure,

4 domin in bayyana shi sosai, kamar yadda ya kamata in faɗa.

5 Ku tafiyar da al’amuranku da hikima a cikin zamanku tare da marasa bi, kuna matuƙar amfani da lokaci.

6 A kullum maganarku ta zama mai ƙayatarwa, mai daɗin ji, domin ku san irin amsar da ta dace ku ba kowa.

Gaisuwa

7 Tikikus zai sanar da ku duk abin da nake ciki. Shi ƙaunataccen ɗan’uwa ne, amintaccen mai hidima, abokin bautarmu kuma a cikin Ubangiji.

8 Na aiko shi a gare ku musamman, domin ku san yadda muke, yă kuma ƙarfafa muku zuciya.

9 Ga kuma Unisimas a nan tare da shi, amintaccen ɗan’uwa ƙaunatacce, wanda shi ma a cikinku yake. Su za su gaya muku duk abin da ya faru a nan.

10 Aristarkus, abokin ɗaurina, yana gaishe ku, haka kuma Markus, wanda kakansu ɗaya ne da Barnaba. Shi ne aka riga aka yi muku umarni a game da shi. In dai ya zo wurinku, ku karɓe shi.

11 Yasuwa kuma da ake kira Yustus yana gaishe ku. Wato, cikin abokan aikina ga Mulkin Allah, waɗannan su kaɗai ne daga cikin Yahudawa masu bi, sun kuwa sanyaya mini zuciya.

12 Abafaras wanda yake ɗaya daga cikinku, bawan Almasihu Yesu, yana gaishe ku, a kullum yana yi muku addu’a da himma, ku dage, kuna cikakku, masu haƙƙaƙewa cikin dukkan nufin Allah.

13 Na shaide shi, lalle ya yi muku aiki ƙwarai da gaske, da kuma waɗanda suke na Lawudikiya da na Hirafolis.

14 Luka, ƙaunataccen likitan nan, da Dimas suna gaishe ku.

15 A gayar mini da ‘yan’uwa na Lawudikiya, da kuma Nimfa da ikilisiyar da take taruwa a gidanta.

16 Sa’ad da aka karanta wasiƙar nan a gabanku, ku sa a karanta ta kuma a gaban ikilisiyar da take a Lawudikiya, ku kuma ku karanta tasu, wato ta Lawudikiyawa.

17 Ku kuma faɗa wa Arkibus ya mai da hankali ya cika hidimar da Ubangiji ya sa shi.

18 Ni Bulus, ni nake rubuta gaisuwar nan da hannuna. Ku tuna da ɗaurina. Alheri yă tabbata a gare ku.