KOL 3

1 To, da yake an tashe ku tare da Almasihu, sai ku nemi abubuwan da suke a Sama, inda Almasihu yake, a zaune a dama ga Allah.

2 Ku ƙwallafa ranku a kan abubuwan da suke Sama, ba a kan abubuwan da suke a ƙasa ba.

3 Gama kun mutu, ranku kuwa a ɓoye yake a gun Almasihu cikin Allah.

4 Sa’ad da Almasihu wanda yake shi ne ranmu ya bayyana, sai ku ma ku bayyana tare da shi a cikin ɗaukaka.

Tsohon Rai da Sabon Rai

5 Saboda haka, sai ku kashe zukatanku ga sha’awace-sha’wacen duniya, wato fasikanci, da aikin lalata, da muguwar sha’awa, da mummunan buri, da kuma kwaɗayi, wanda shi ma bautar gumaka ne.

6 Saboda waɗannan abubuwa ne fushin Allah yake sauka a kan kangararru.

7 A dā kuna bin waɗannan sa’ad da suke jiki a gare ku.

8 Amma yanzu sai ku yar da duk waɗannan ma, wato fushi, da hasala, da ƙeta, da yanke, da alfasha.

9 Kada ku yi wa juna ƙarya, da yake kun yar da halinku na dā, da ayyukansa,

10 kun ɗauki sabon halin nan da ake sabuntawa ga sani, bisa ga kamannin Mahaliccinsa.

11 A nan kam, ba hanyar nuna bambanci a tsakanin Ba’al’umme da Bayahude, ko mai kaciya da marar kaciya, ko bare da baubawa, ko ɗa da bawa, sai dai Almasihu shi ne kome, shi kuma yake cikinmu duka.

12 Saboda haka, sai ku ɗauki halin tausayi, da kirki, da tawali’u, da salihanci, da haƙuri, idan ku zaɓaɓɓu ne na Allah, tsarkaka, ƙaunatattu,

13 kuna jure wa juna, in kuma wani yana da ƙara game da wani, sai su yafe wa juna. Kamar yadda Ubangiji ya yafe muku, ku kuma sai ku yafe.

14 Fiye da waɗannan duka, ku ɗau halin ƙauna, wadda dukkan kammala take ƙulluwa a cikinta.

15 Salamar Almasihu kuma tă mallaki zuciyarku, domin lalle ga haka aka kira ku in kuna jiki guda, ku kuma kasance masu gode wa Allah.

16 Maganar Almasihu tă kahu a cikin zuciyarku a yalwace, kuna koya wa juna, kuna yi wa juna gargaɗi da matuƙar hikima ta wurin rairar waƙoƙin Zabura da na yabon Allah, kuna kuma raira waƙa ga Allah, kuna gode masa tun daga zuci.

17 Kome kuke yi, a game da magana ko aikatawa, ku yi duka da sunan Ubangiji Yesu, kuna gode wa Allah Uba ta wurinsa.

Zaman Dacewa na Sabon Rai

18 Ku matan aure, ku bi mazanku yadda ya dace a cikin Ubangiji.

19 Ku maza, ku ƙaunaci matanku, kada kuma ku yi musu kaushin hali.

20 Ku ‘ya’ya, ku yi wa iyayenku biyayya ta kowane hali, domin haka Ubangiji yake so.

21 Ku ubanni, kada ku ƙuntata wa ‘ya’yanku, domin kada su karai.

22 Ku bayi, ku yi biyayya ga waɗanda suke iyayengijinku na duniya ta kowace hanya, ba da aikin ganin ido ba, kamar masu son faranta wa mutane rai, sai dai da zuciya ɗaya, kuna tsoron Ubangiji.

23 Kome za ku yi, ku yi shi da himma kuna bauta wa Ubangiji ne, ba mutum ba,

24 da yake kun sani Ubangiji zai ba ku gādo sakamakonku. Ubangiji Almasihu fa kuke bauta wa!

25 Mai mugun aiki kuwa za a sāka masa da mugun aikin da ya yi, babu kuma tāra.