1 YAH 1

Kalmar Rai

1 Shi da yake tun fil’azal yake nan, wanda muka ji, muka gani da idonmu, muka duba, hannuwanmu kuma suka taɓa, a game da Kalmar Rai,

2 wannan Rai kuwa an bayyana shi, mu kuwa mun gani, muna ba da shaida, muna kuma sanar da ku Rai madawwamin nan wanda tun dā yake tare da Uba, aka kuwa bayyana shi gare mu,

3 to, shi wannan da muka ji, muka kuma gani, shi ne dai muke sanar da ku, domin ku ma ku yi tarayya da mu. Hakika kuwa tarayyar nan tamu da Uba ne, da kuma Ɗansa Yesu Almasihu.

4 Muna kuma rubuto muku wannan ne domin farin cikinmu ya zama cikakke.

Allah Haske Ne

5 Wannan shi ne jawabin da muka ji a gunsa, muke sanar da ku cewa Allah haske ne, ba kuwa duhu gare shi ko kaɗan.

6 In mun ce muna tarayya da shi, alhali kuwa muna zaune a duhu, mun yi ƙarya ke nan, ba ma aikata gaskiya.

7 In kuwa muna zaune a haske, kamar yadda shi yake cikin haske, muna tarayya da juna ke nan, jinin Yesu Ɗansa kuma yana tsarkake mu daga dukkan zunubi.

8 In mun ce ba mu da zunubi, ruɗin kanmu muke yi, gaskiya kuwa ba ta tare da mu.

9 In kuwa muka bayyana zunubanmu, to, shi mai alkawari ne, mai adalci kuma, zai kuwa gafarta mana zunubanmu, ya tsarkake mu daga dukkan rashin adalci.

10 In mun ce ba mu yi zunubi ba, mun ƙaryata shi ke nan. Maganarsa kuma ba ta tare da mu.