2 KOR 5

1 Gama mun sani in an rushe jikinmu na wannan duniya, Allah ya tanadar mana jiki a Sama, wato, wanda shi kansa ya yi, wanda zai dawwama.

2 A jikin nan muna ajiyar zuciya, mun ƙosa mu samu a suturta mu da jiki namu na Sama,

3 gama in aka suturta mu da shi, ba za a same mu tsirara ba.

4 Sa’ad da muke zaune a cikin jikin nan na duniya, nishi muke domin matsuwar da muke sha, ba domin muna so mu rabu da jikinmu na wannan duniya ba ne, amma don so muke yi a suturta mu da na Sama, domin mai rai ya shafe mai mutuwa.

5 Allah kuwa shi ya tanadar mana wannan sākewar, shi da ya ba mu Ruhunsa, domin tabbatar da abin da zai yi a nan gaba.

6 Saboda haka, kullum muke da ƙarfin zuciya, mun kuma sani, muddin muna tare da wannan jiki, a rabe muke da Ubangiji,

7 domin zaman bangaskiya muke yi, ba na ganin ido ba.

8 Hakika muna da ƙarfin zuciya, mun kuma gwammace mu rabu da jikin nan, mu zauna a gun Ubangiji.

9 Saboda haka, ko muna gunsa, ko muna a rabe da shi, burinmu shi ne mu faranta masa zuciya.

10 Don lalle ne a gabatar da mu duka, a gaban kursiyin shari’a na Almasihu, domin kowa yă sami sakamakon abin da ya yi tun yana tare da wannan jiki, ko mai kyau ne, ko kuma marar kyau.

Aikin Sulhuntawa

11 Da yake muna tsoron Ubangiji, shi ya sa muke ƙoƙarin rinjayar mutane. Yadda muke kuwa, ai, sananne ne ga Allah, muna fata ku ma haka abin yake a lamirinku.

12 Har wa yau kuma, ba yabon kanmu muke yi a gare ku ba, sai dai muna ba ku hanyar yin taƙama da mu, don ku sami yadda za ku mai da jawabi ga waɗanda suke fariya da maƙaminsu, ba da halinsu ba.

13 In hankalinmu ya fita, ai, saboda Allah ne, in kuwa a cikin hankalinmu muke, ai, ribarku ce.

14 Ƙaunar Almasihu a gare mu, ita take mallakarmu, saboda haka mun tabbata, da yake wani ya mutu saboda dukan mutane, ashe kuwa, mutuwarsu ce dukansu.

15 Ya kuwa mutu ne saboda dukan mutane, domin waɗanda suke a raye, kada su yi zaman ganin dama a nan gaba, sai dai su yi zaman wannan da ya mutu saboda su, aka kuma tashe shi saboda su.

16 Saboda haka, a nan gaba ba mā ƙara duban kowane mutum bisa ga ɗabi’ar jiki kawai, domin ko da yake mun taɓa duban Almasihu bisa ga ɗabi’ar jiki, yanzu ba ma ƙara dubansa haka.

17 Saboda haka, duk wanda yake na Almasihu sabuwar halitta ne, tsohon al’amari duk ya shuɗe, ga shi, kome ya zama sabo.

18 Duk wannan kuwa yin Allah ne, shi da ya sulhunta mu da kansa ta wurin Almasihu, ya kuma ba mu aikin shelar sulhuntawar,

19 wato, Allah ne, ta wurin Almasihu, yake sulhunta ‘yan adam da shi kansa, ba ya kuwa lasafta laifofinsu a kansu ba, ya kuma danƙa mana maganar nan ta sulhuntawa.

20 Saboda haka, mu jakadu ne na Almasihu, wato, Allah na neman mutane ta wurinmu. Muna roƙonku a madadin Almasihu, ku sulhuntu da Allah.

21 Shi da bai san zunubi ba, Allah ya mai da shi zunubi saboda mu, domin mu mu sami adalcin Allah ta wurinsa.