2 KOR 6

1 Da yake kuma muna aiki tare da Allah, muna roƙonku kada ku yi na’am da alherin Allah a banza.

2 Domin ya ce,

“Na saurare ka a lokacin samun karɓuwa,

Na kuma taimake ka a ranar ceto.”

Ga shi, yanzu ne lokacin samun karɓuwa! Ga shi kuma, yau ce ranar ceto!

3 Ba ma zamar wa kowa sanadin tuntuɓe, don kada a aibata aikinmu,

4 Amma ta kowace hanya muna bayyana gaskiyarmu, a kan bayin Allah muke, ta matuƙar jurewa, da shan wahala, da ƙuntata, da masifu,

5 da shan dūka, da shan ɗauri, da yawan hargitsi, da yawan fama, da rasa barci, da kuma rasa abinci.

6 Muna kuma bayyana gaskiyarmu ta halin tsarkaka, da sani, da haƙuri, da kirki, da Ruhu Mai Tsarki, da sahihiyar ƙauna,

7 da maganar gaskiya, da kuma ikon Allah. Muna riƙe da makaman adalci dama da hagu.

8 Ana ɗaukaka mu, ana kuma wulakanta mu, ana yabonmu, ana kuma kushenmu. An ɗauke mu kamar mayaudara, mu kuwa masu gaskiya ne.

9 Kamar ma ba a san mu ba, an kuwa san mu sarai, kamar a bakin mutuwa muke, ga shi kuwa, muna a raye, ana ta horonmu, duk da haka ba a kashe mu ba,

10 kamar muna baƙin ciki, kullum kuwa farin ciki muke yi, kamar matalauta muke, duk da haka kuwa muna arzuta mutane da yawa, kamar ba mu da kome, alhali kuwa kome namu ne.

11 Ya ku Korantiyawa, ba mu ɓoye muku kome ba, mun saki zuciya da ku ƙwarai.

12 Ai, ba wata rashin yarda a zuciyarmu, sai dai a taku.

13 Ina roƙonku kamar ‘ya’yana, ku ma ku saki zuciya da mu.

Ku Haikalin Allah Ne

14 Kada ku yi cuɗanya marar dacewa da marasa ba da gaskiya. To, me ya haɗa aikin adalci da na mugunta? Ko kuwa me ya haɗa haske da duhu?

15 Ina kuma jiyayyar Almasihu da iblis? Me kuma ya haɗa mai ba da gaskiya da marar ba da gaskiya?

16 Wace yarjejeniya ce take a tsakanin Haikalin Allah da gumaka? Domin mu haikali ne na Allah Rayayye. Yadda Allah ya ce,

“Zan zauna tare da su, in yi yawo a tsakaninsu,

Zan kuma kasance Allahnsu,

Su kuma su kasance jama’ata.

17 Saboda haka, sai ku fito daga cikinsu,

Ku keɓe, in ji Ubangiji,

Kada ku ko taɓa wani abu marar tsarki,

Ni kuwa in yi na’am da ku,

18 In kasance Uba a gare ku,

Ku kuma ku kasance ‘ya’yana, maza da mata,

In ji Ubangiji Maɗaukaki.”