A.M. 16

Timoti Ya Bi Bulus da Sila

1 Sai kuma Bulus ya zo Darba da Listira. Akwai wani almajiri a Listira, mai suna Timoti, ɗan wata Bayahudiya mai bi, ubansa kuwa Bahelene ne.

2 Shi kuwa ‘yan’uwan da suke Listira da Ikoniya na yabonsa.

3 Sai Bulus ya so Timoti ya rako shi, har ya yi masa kaciya saboda Yahudawan da suke waɗannan wurare, don duk sun san ubansa Bahelene ne.

4 Lokacin da suke tafiya suna bin gari gari, suka riƙa gaya wa jama’a ƙa’idodin da manzanni da dattawan Ikkilisiya suka ƙulla a Urushalima, don su kiyaye su.

5 Ta haka ikilisiyoyi suka ƙarfafa a cikin bangaskiya, a kowace rana suna ƙara yawa.

Wahayin Bulus na Mutumin Makidoniya

6 Sai suka zazzaga ƙasar Firijiya da ta Galatiya, saboda Ruhu Mai Tsarki ya hana su yin Maganar Ubangiji a ƙasar Asiya.

7 Da suka zo kan iyakar ƙasar Misiya, sai suka yi ƙoƙarin zuwa ƙasar Bitiniya, amma Ruhun Yesu bai yardar musu ba.

8 Suka kuwa ratsa ƙasar Misiya, suka gangara zuwa Taruwasa.

9 Wata rana da daddare aka yi wa Bulus wahayi, ya ga wani mutumin ƙasar Makidoniya na tsaye, yana roƙonsa yana cewa, “Ka ƙetaro Makidoniya, ka taimake mu mana.”

10 Da kuwa ya ga wahayin, nan take sai muka nemi tafiya Makidoniya, muka tabbata cewa Allah ne ya kira mu mu yi musu bishara.

Lidiya Ta Ba Da Gaskiya

11 Shi ke nan fa, sai muka tashi a jirgin ruwa daga Taruwasa, muka miƙe sosai har zuwa tsibirin Samutaraki, kashegari kuma sai Niyabolis,

12 daga nan kuma sai Filibi ta ƙasar Makidoniya, wadda take babbar alkarya ce a wannan waje, birnin Romawa ne kuma. A nan birnin muka yi ‘yan kwanaki.

13 Ran Asabar muka fita ƙofar gari, muka je bakin kogi, inda muke tsammani akwai wurin yin addu’a. Nan muka zauna, muka yi wa matan da suka taru magana.

14 Ɗaya daga cikin masu sauraronmu wata mace ce, mai suna Lidiya, mai sayar da jar hajja, mutuniyar Tayatira, mai ibada ce kuma. Ubangiji ya buɗe zuciyarta, har ta mai da hankali ga abin da Bulus ya faɗa.

15 Da aka yi mata baftisma tare da jama’ar gidanta, ta roƙe mu ta ce, “Da yake kun amince ni mai ba da gaskiya ga Ubangiji ce, to, sai ku zo gidana ku sauka.” Sai ta rinjaye mu.

Kulle Manzanni a Kurkukun Filibi

16 Wata rana muna tafiya wurin yin addu’a, sai muka gamu da wata yarinya mai aljani mai duba, tana kuwa samo wa iyayengijinta amfani mai yawa ta wurin dubar.

17 Sai ta riƙa binmu, mu da Bulus, tana ihu tana cewa, “Mutanen nan fa bayin Allah Maɗaukaki ne, suna kuwa sanar da ku hanyar ceto!”

18 Haka ta dinga yi kwana da kwanaki, har Bulus ya ji haushi ƙwarai, ya juya ya ce wa aljanin, “Na umarce ka da sunan Yesu Almasihu, ka rabu da ita.” Nan take kuwa ya rabu da ita.

19 Da iyayengijinta suka ga hanyar samunsu ta toshe, suka danƙe Bulus da Sila, suka ja su har zuwa bakin kasuwa gaban mahukunta.

20 Da suka kai su gaban alƙalai suka ce, “Mutanen nan suna birkita garinmu ƙwarai da gaske, Yahudawa ne kuwa.

21 Suna kuma koyar da al’adun da bai halatta mu karɓa ko mu bi ba, da yake mu Romawa ne.”

22 Sai jama’a suka ɗungumo musu gaba ɗaya, alƙalan kuma suka yi kaca-kaca da tufafinsu, suka tuttuɓe su, suka yi umarni a bulale su da tsumagu.

23 Da aka bulale su da gaske, aka jefa su kurkuku, aka umarci yari ya tsare su da kyau.

24 Shi kuwa da ya karɓi wannan umarni, sai ya jefa su can ciki cikin kurkuku, ya sa su a turu.

25 A wajen tsakar dare Bulus da Sila suna addu’a suna waƙoƙin yabon Allah, ‘yan sarka kuwa suna sauraronsu,

26 farat ɗaya, sai aka yi wata babbar rawar ƙasa, har harsashin ginin kurkuku ya raurawa. Nan da nan ƙofofin suka bubbuɗe, marin kowa kuma ya ɓalle.

27 Da yāri ya farka daga barci ya ga ƙofofin kurkuku a buɗe, ya zaro takobinsa, yana shirin kashe kansa, cewa yake ‘yan sarƙa sun gudu.

28 Amma Bulus ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Kada ka cuci kanka, ai duk muna nan!”

29 Sai yari ya ce a kawo fitilu, ya yi wuf ya ruga ciki, ya fāɗi gaban Bulus da Sila, yana rawar jiki don tsoro.

30 Sa’an nan ya fito da su waje, ya ce, “Ya shugabanni, me zan yi in sami ceto?”

31 Su kuwa suka ce, “Ka gaskata da Ubangiji Yesu, za ka sami ceto, kai da iyalinka.”

32 Sa’an nan suka gaya masa Maganar Ubangiji, shi da iyalinsa duka.

33 Nan take da daddaren nan ya ɗebe su, ya wanke musu raunukansu. Nan da nan kuwa aka yi masa baftisma da dukan iyalinsa.

34 Sa’an nan ya kawo su gidansa, ya kawo musu abinci, ya yi ta farin ciki matuƙa, domin shi da iyalinsa duka sun gaskata da Allah.

35 Amma da gari ya waye, sai alƙalan suka aiko dogarai, suka ce, “Suka ce a saki mutanen nan.”

36 Yari kuwa ya shaida wa Bulus maganar, ya ce, “Alƙalai sun aiko a sake ku, saboda haka yanzu sai ku fito, ku tafi lafiya.”

37 Amma Bulus ya ce musu, “Ai, a fili suka daddoke mu, ba ko bin ba’asi, mu ma da muke Romawa bisa ga ‘yangaranci, suka jefa mu a kurkuku, yanzu kuma sā fitar da mu a ɓoye? Sai dai su zo da kansu su fito da mu.”

38 Sai dogarai suka shaida wa alƙalan wannan magana. Su kuwa da suka ji Bulus da Sila Romawa ne suka tsorata.

39 Sa’an nan suka zo suka tubar musu, bayan kuma sun fito da su, suka roƙe su su bar garin.

40 To, da suka fita daga kurkukun, suka tafi wurin Lidiya. Bayan sun ga ‘yan’uwa, suka kuma ƙarfafa musu zuciya, suka tashi.