A.M. 17

Hargitsi a Tasalonika

1 To, da suka bi ta Amfibolis da Aboloniya, suka isa Tasalonika, inda wata majami’ar Yahudawa tāke.

2 Sai Bulus ya shiga wurinsu kamar yadda ya saba, Asabar uku a jere yana muhawwara da su daga cikin Littattafai,

3 yana yi musu bayani, yana kuma tabbatarwa, cewa lalle ne, Almasihu yă sha wuya, ya kuma tashi daga matattu. Ya kuma ce, “Yesun nan da nake sanar muku, shi ne Almasihu.”

4 Sai waɗansunsu suka amince, suka koma wajen Bulus da Sila, haka kuma babban taron Helenawa masu ibada, da manyan mata ba kaɗan ba.

5 Amma Yahudawa, saboda kishi, suka ɗibi waɗansu ashararai, ‘yan iska, suka tara jama’a suka hargitsa garin kaf, suka fāɗa wa gidan Yason, suna nemansu don su fito da su gaban taron jama’a.

6 Da ba su same su ba, suka jawo Yason da waɗansu ‘yan’uwa, har gaban mahukuntan garin, suna ihu suna cewa, “Mutanen nan masu ta da duniya a tsaye, ga su sun zo nan ma,

7 har ma Yason ya sauke su! Dukansu kuwa suna saɓa dokokin Kaisar, suna cewa wani ne sarki, wai shi Yesu.”

8 Da mutanen gari da mahukunta suka ji wannan, hankalinsu ya tashi.

9 Ba su sake su ba, sai da suka karɓi kuɗin lamuni a hannun Yason da sauransu.

Manzanni a Biriya

10 Nan da nan kuwa da dare ya yi, ‘yan’uwa suka sallami Bulus da Sila su tafi Biriya. Da suka isa can kuma suka shiga majami’ar Yahudawa.

11 To, waɗannan Yahudawa kam, sun fi na Tasalonika dattaku, domin sun karɓi Maganar hannu biyu biyu, suna ta nazarin Littattafai kowace rana, su ga ko abin haka yake.

12 Saboda haka da yawa daga cikinsu suka ba da gaskiya, har da waɗansu Helenawa ba kaɗan ba, mata masu daraja, da kuma maza.

13 Amma da Yahudawan Tasalonika suka ji labari Bulus yana sanar da Maganar Allah a Biriya ma, suka je suka zuga taro masu yawa a can ma, suna ta da hankalinsu.

14 Nan da nan kuwa ‘yan’uwa suka tura Bulus bakin bahar, amma Sila da Timoti suka dakata a nan.

15 Waɗanda suka rako Bulus kuwa, sai da suka kai shi har Atina. Bayan Bulus ya yi musu saƙon umarni zuwa wurin Sila da Timoti, cewa su zo wurinsa da gaggawa, suka tafi.

Bulus a Atina

16 To, sa’ad da Bulus yake dākonsu a Atina, ya ji haushi ƙwarai da ya ga ko’ina gumaka ne a birnin.

17 A kowace rana ya yi ta muhawwara a cikin majami’a da Yahudawa, da waɗansu masu ibada, da kuma waɗanda yake tararwa a bakin kasuwa.

18 Har wa yau kuma waɗansu Abikuriyawa da Sitokiyawa masu ilimi suka ci karo da shi. Waɗansu suka ce, “Me wannan mai surutu yake nufi?” Waɗansu kuwa suka ce “Ga alama, mai yin wa’azin bāƙin alloli ne”– domin kawai yana yin bisharar Yesu, da kuma tashi daga matattu.

19 Sai suka riƙe shi suka kai shi Tudun Arasa, suka ce, “Ko ka faɗa mana wace irin baƙuwar koyarwa ce wannan da kake yi?

20 Domin ka kawo mana abin da yake baƙo a gare mu, muna kuwa so mu san ma’anarsa.”

21 Alhali kuwa duk Atinawa da baƙinsu ba abin da suke yi, sai kashe zarafinsu wajen jin baƙon abu, ko kuma ɗorar da shi.

22 Sai Bulus ya miƙe a tsakiyar Tudun Arasa, ya ce, “Ya ku mutanen Atina, na dai lura, ku masoyan ibada ne ƙwarai, ta kowane fanni.

23 Don sa’ad da nake zagawa, na duba abubuwan da kuke yi wa ibada, har ma na tarar da wani bagadin hadaya da wannan rubutu a sama da shi cewa, ‘Saboda Allahn da ba a sani ba.’ To, shi wanda kuke yi wa sujada ba a tare da kun san shi ba, shi nake sanar muku.

24 Allahn da ya halicci duniya da dukkan abin da yake cikinta, shi da yake Ubangijin sama da ƙasa, ba ya zama a haikalin ginin mutum.

25 Haka kuma ba ya neman wani taimako gun mutum, sai ka ce wani abu yake bukata, tun da yake shi kansa ne yake ba dukkan mutane rai, da numfashi, da dukkan abubuwa.

26 Shi ne kuma ya halicci dukkan al’umma daga tsatso ɗaya, domin su zauna a dukan sararin duniya, ya kuma ƙayyade zamanansu da iyakokin ƙasashensu,

27 wato nufinsa shi ne su neme shi, ko watakila sā laluba su same shi, alhali kuwa ba ya nesa da kowane ɗayanmu.

28 Domin

‘Ta gare shi ne muke rayuwa, muke motsi, muka kuma kasance,’

kamar yadda waɗansu mawaƙanku ma suka ce,

‘Hakika, mu ma zuriya tasa ce.’

29 To, da yake mu zuriyar Allah ne, ai, bai kamata mu tsammaci Allah na kama da wata surar zinariya, ko ta azurfa, ko ta dutse ba, wadda mutum ya ƙago ta dabararsa.

30 Dā kam, Allah ya kawar da kai ga zamanin jahilci, amma yanzu yana umartar dukkan mutane a ko’ina su tuba,

31 tun da yake ya tsai da ranar da zai yi wa duniya shari’a, shari’a adalci, ta wurin mutumin nan da ya sa, wannan kuwa ya tabbatar wa dukan mutane, da ya tashe shi daga matattu.”

32 Da dai suka ji maganar tashin matattu, sai waɗansu suka yi ba’a, amma waɗansu suka ce, “Game da wannan magana kam, mā sāke jin abin da za ka faɗa.”

33 Sai Bulus ya fita daga cikinsu.

34 Amma waɗansu mutane suka koma wajensa suka ba da gaskiya, a cikinsu har da Diyonisiyas, ɗan majalisar Tudun Arasa, da wata mace mai suna Damarisa, da waɗansu dai haka.